Wane ɗan wasa ne ya fi yin fice a shekarar 2025?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
An shiga sabuwar shekarar 2026 inda aka yi bankwana da 2025 shekarar da ta kasance ɗaya daga waɗanda wasu ƴan wasan tamaula suka taka rawar gani da ta kai sun yi fice a duniya.
Tun daga matasan da suka haskaka da waɗanda suka daɗe da gogewa a fannin taka leda da rawar da suka taka a shekarar da aka yi ban kwana da ita suna da yawa makil.
BBC ta yi duba na tsanaki an kuma zakulo wasu ƴan ƙwallon da suka yi fice a wata 12 da ya gabata.
Harry Kane (Bayern Munich)

Asalin hoton, Getty Images
Ƙyaftin ɗin tawagar Ingila yana kan ganiya, wanda ke haskawa a Jamus a kaka ta biyu da yake murza leda a Bayern Munich.
Tsohon ɗan wasan Tottenham, mai shekara 32 ya sharara ƙwallo 60 a shekarar 2025 a tawagarsa ta Ingila da kuma Bayern Munich.
Hakan ya sa ya shiga sawun gaba cikin ƴan wasan da suka ci ƙwallaye da yawa a shekara, koda yake ƙyaftin ɗin tawagar Argentina, Lionel Messi ne kan gaba mai 91 a raga a 2012 a tarihi.
Lamine Yamal (Barcelona)

Asalin hoton, Getty Images
Lamine Yamal shekararsa 18, wanda kullum ake maganarsa a kafafen yaɗa labarai da magoya baya da ƴan kallo da kuma masu zuwa da tsaki ƙwan ƙwazon da yake yi a wasanninsa.
Ya haskaka a tawagar Sifaniya a gasar cin kofin nahiyar Turai Euro 2024, wanda ya kara nuna gogewa da basirar taka leda a shekarar 2025 da muka yi ban kwana da ita.
Matashin ya ci ƙwallo bakwai ya bayar da takwas aka zura a raga a wasa 14 a La Liga a Barcelona a kakar nan.
Tun daga tsakiyar shekarar 2025 ya ci ƙwallo 11 ya bayar da 10 aka zura a raga a tawagar Sifaniya da kuma Barcelona.
Ousmane Dembele (Paris St-Germain)

Asalin hoton, Getty Images
Ousmane Dembele ya fara shekarar 2025 da sa ƙwazo kuma yana ganiya da ta kai ya ci ƙwallo 15 a wasa takwas da fara wasannin cikin shekarar, wanda ya ci 35 a karawa 53 a 2024/25 kakar da ya kafa tarihin cin ƙwallaye a sana'arsa ta taka leda.
Mai shekara 28, wanda ya nuna gogewarsa a filin tamaula ya sa ya lashe ƙyautar Ballon d'Or, musamman saboda ƙwallayen da ya zazzaga a raga a 2025.
Shekarar ta zama abin alfahari da ɗan wasan wanda ya lashe Champions League da manyan kofi uku a babbar gasar tamaula ta Faransa da zuwa wasan karshe a Fifa Club World Cup da lashe Uefa Super Cup.
Erling Haaland (Man City)

Asalin hoton, Getty Images
Erling Haaland na kan ganiya a kakar tamaula a bana a Manchester City da kuma tawagarsa ta Norway.
Mai shekara 25, ya zura ƙwallo 25 a raga a wasa 24 da fara kakar nan, sannan yana kan gaba da ya sa Norway ta samu gurbin shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da kuma Mexico - wanda ya ci ƙwalo 16 a wasa takwas a neman gurbin zuwa gasar kofin duniyar.
Wannan shi ne karon farko da Norwat za ta fafata a gasar kofin duniya tun 1998.
Cole Palmer (Chelsea)

Asalin hoton, Getty Images
Wannan kakar ta zowa da Cole Palmer da kalubalen jinya, amma tun kan nan ta taka rawar gani a Fifa Club World Cup da Chelsea a Amurka a watan Yuni, kuma shi ne fitatcen ɗan ƙwallon gasar.
Ya sa ƙwazon da ta kai Chelsea ta samu komawa buga Champions League da bayar da ƙwallo biyun da aka ci Real Betis da ta kai ƙungiyar da ke buga Premier League ta lashe Conference League.
Palmer, mai shekara 23 ya ci ƙwallo uku ya bayar da biyu aka ci a raga, kuma babu wanda ya kai shi wannan kokarin.
Nuno Mendes (Paris St-Germain)

Asalin hoton, Getty Images
Bayan da Paris St Germain ta lashe Champions League da kofi uku a babbar gasar tamaula ta Faransa a 2025, ƴan wasanta ne ke gaba-gaba a yawan ƙwazo da nuna bajinta.
Ɗan wasa Nuno Mendes, mai shekara 23 ya nuna kansa a matakin ɗaya daga fitattu a gurbin masu tsare baya daga gefen hagu a duniya, saboda rawar da yake takawa a PSG.
Gianluigi Donnarumma (Paris St-Germain/Man City)

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron raga, Gianluigi Donnarumma, wanda ya koma Manchester City daga Paris St Germain kan fara kakar nan, shi ne ya lashe ƙyautar mai tsaron raga na Fifa da aka bayyana a farkon watan Disamba a 2025.
Ɗan wasan tawagar Italiya ba zai mance da ƙwazon da ya yi ba a shekarar 2025, wanda PSG ta lashe Champions League a karon farko a tarihi da kuma ɗaukar manyan kofi uku a gasar tamaula ta Faransa da kaiwa zagayen karshe a Fifa Club World Cup da Chelsea ta yi nasarar ɗauka a Amurka.
Mai shekara 26 na yin bajinta a Manchester City a bana, inda ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama take ta biyu a teburin Premier League, sannan ta huɗu a teburin gasar zakarun Turai ta Champions League.
Pedri (Barcelona)

Asalin hoton, Getty Images
Pedri, mai shekara 23, wannan ce kaka mafi ƙyau a tarihin sana'arsa ta taka leda a kakar 2024/25, wanda ya bayar da gudunmuwar da Barcelona ta lashe kofi uku a babbar gasar cikin gida ta Sifaniya, wanda ake kwatantan shi da ɗaya daga cikin fitattun ƴan ƙwallo a duniya.
Ya ƙwace ƙwallo sau 254 shi ne kan gaba a wannan bajintar tsakanin ƴan wasa da ke buga manyan gasar Turai biyar, hak kuma shi ne kan gaba a samar da damarmaki, wanda ya yi haka sau 70 a Barcelona.
Duk da cewar yawan jin raunin na kawo masa cikas, amma duk da haka yana da mahimmaci a wasannin Barcelona a kakar nan, ya kuma taka rawar gani a ƙungiyar da take matakin farko a bana da mai rike da kofin Real Madrid ta biyu.
Kylian Mbappe (Real Madrid)

Asalin hoton, Getty Images
Kylian Mbappe ya zazzaga ƙwallaye da yawa a 2025, wanda ya ci 59 a Real Madrid a dukkan wasannin da ya yi mata a shekarar nan.
Hakan na nufin cewar mai shekara 27 ya yi kan-kan-kan da yawan ƙwallayen da Cristiano Ronaldo ya ci a cikin shekarar 2013.
Vitinha (Paris St-Germain)

Asalin hoton, Getty Images
Saboda da rawar da yake takawa, ɗan wasan ƙwararre ne matuƙa, duk da cewar sai an yi nazarai na musammam kafin ka sa ƙwallo cikin fitattu na duniya, amma dai mai shekara 25 yana da matukar ƙyau a fannin taka leda a 2025
Idan aka kwatanta shi da fitaccen ɗan wasa Andres Iniesta, Vitinha mai buga gurbi iri ɗaya da na tsohon ɗan ƙwallon Barcelona yana da ƙwarewa da gogewar da take taimaka masa ya mamaye wasanni daga tsakiyar fili ga Paris St-Germain.











