Najeriya ta ɗauki fansa a kan Uganda ta kuma kai zagayen gaba a Afcon

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Najeriya ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka da ake yi a Morocco, bayan doke Uganda 3-1 ranar Talata.
Wannan shi ne karon farko da Super Eagles ta lashe dukkan wasa uku a cikin rukuni tun bayan 2021.
Sun kuma fuskanci juna a karo na biyu kenan a Afcon a wasa uku-uku a rukuni na uku da suka kara Complex Sportif de Fes.
Wasa tilo da suka fuskanci juna a Afcon shi ne a zagayen daf da karshe a 1978, inda Uganda ta yi nasarar cin Najeriya 2-1
A karawar da suka yi a 1978 a daf da karshe, Uganda ta fara cin ƙwallo ta hannun Abdulla Nasur a minti na 11 daga baya Najeriya ta farke ta hannun Martins Eyo a zagaye na biyu.
Sai dai daf a tashi ne Phillip Omondi ya ci wa Uganda na uku da ya kaita zagayen gaba.
An sabunta wannan gurbin bayan tashi daga karawar da Najeriya ta ci Uganda 3-1 ranar Talata a Afcon a Morocco.
Jimilla sun kara sau tara tsakaninsu a dukkan fafatawa. Uganda ta yi nasara huɗu, Najeriya ta ci wasa uku da canjaras biyu
Haka kuma an haɗa rukuni tare da Uganda da Najeriya a wasan neman shiga gasar cin kofin Afirka na 1994 da kuma na 2008.
A wasa huɗu da za su kara kenan gida da waje Najeriya ta yi nasara biyu, Uganda ta ci ɗaya da canjaras ɗaya - Kuma Super Eagles ce kan kai bante zuwa gasar.
Wasan baya-bayan nan da suka haɗu shi ne na sada zumunta ranar 20 ga watan Nuwamba da aka tashi canjaras a Asaba a jihar Delta a Najeriya.
Kawo yanzu a wasa uku ba a doke Uganda ba a karawa da Najeriya, wadda ta yi nasara biyu da canjaras ɗaya.
Wasan karshe da Super Eagles ta ci Uganda a Afcon a wasan neman shiga gasar 2008 ta ci 1-0 ranar 24 ga watan Maris 2007 a filin MKO Abiola a Abeokuta, inda Nwankwo Kanu ne ya zura ƙwallon a raga a minti na 73.
Nasarorin da Uganda ke yi a Afcon

Asalin hoton, Getty Images
- Ta fara da rashin nasara a hannun Tunisia, sannan ta raba maki da Tanzania.
- Kenan ta buga wasa biyar a Afcon ba tare da nasara ba, aka dke ta uku da canjaras biyu.
- Wasan bayan nan da ta ci a Afcon shi ne nasara 2-0 a hannun Jamhuriyar Congo a 2019.
- Ana zura mata ƙwallo a raga a wasa biyar baya a Afcon, karawar da ƙwallo bai shiga ragarta ba tun wasan farko a cikin rukuni a 2019.
- Tarihin da take take da shi a wasa na biyu a cikin rukuni a Afcon shi ne ta yi fafatawa shida da nasara ɗaya da canjaras ɗaya aka doke ta huɗu daga cikinsu.
- Rabon da ta yi nasara a wasan karshe a cikin rukuni tun bayan da ta ci Morocco 3-0 a 1978.
- An kuma doke ta wasa na uku a karawar cikin rukuni a 1968 da 1974 da 1976 da kuma 2019.
- Wasan da ba a doke ta ba a wasan karshe a cikin rukuni shi ne a 2017 da ta yi 1-1 da Mali.
- Ta sha kashi a wasan karshe a cikin rukuni a 2019 da Masar ta doke ta 2-0.
- Idan har Uganda ba ta doke Najeriya ba, za ta yi ban kwana da gasar Afcon karo na shida ba tare da cin wasa ba da ya haɗa a gasar 1968 da 1974 da 1976 da kuma 2017.
- Idan kuma har ta kai zagaye na biyu zai zama karo na uku kenan bayan 1978 da kuma 2019.
- Dukkan ƙwallo biyu da Uganda ta ci daga ƴan wasan da suka shiga canji ne da ya haɗa da wadda Denis Omedi ya zura wa Tunisia da ta Uche Ikpeazu da ya ci Tanzania.
- Denis Omedi yana da hannu a ƙwallo biyun da Uganda ta ci, wanda ya zura ɗaya a ragar Tunisia, shi ne ya bayar da wadda aka ci Tanzania.
- Omedi ya shiga wasa biyu a canjin ƴan wasa yana da hannu a ƙwallo biyun da Uganda ta zura a raga.
- Allan Okello ya nemi ragar Tanzani sau biyar, shi ne kan gaba a wannan ƙwazon a wasa ɗaya a Afcon a kasarsa.
- Uganda ta kai hari shida zuwa ragar Tanzania da cin ɗaya daga ciki.
- An zura ƙwallo huɗu a ragar Uganda daga hari bakwai da aka kai mata a Afcon a Morocco.
Ƙwazon da Super Eagles ke yi a Afcon

Asalin hoton, Getty Images
- Ta lashe wasa biyu a jere a cikin rukuni da doke Tanzania da Tunisia.
- Tuni ta kai zagayen ƴan 16 a gasar cin kofin Afirka da ake yi a Morocco.
- Wannan shi ne karo na 16 a jere da Najeriya ta kai zagaye na biyu a Afcon.
- Rabon da ta kasa kaiwa zagaye na biyu a Afcon tun 1982.
- Wannan shi ne karo na 19 da Najeriya take haura zagaye na biyu daga karawar rukuni a Afcon
- Babu kasar da ta kai Super Eagles yawan kaiwa zagaye na biyu a Afcon fiye da Najeriya.
- Wasan da ta ci Tunisia shi ne nasara ta 35 da Najeriya ta yi a cikin rukuni a Afcon daga karawa 59 da rashin nasara 10 daga ciki, Masar ce kan gaba da yawan nasara a karawar rukuni mai 41.
- Kan yi nasara a karawar cikin rukuni a wasa huɗu baya har da cin wasa biyu a 2023 da doke Ivory Coast 1-0 da kuma Guinea Bissau da kuma nasara biyu a gasar da ake yi a Morocco.
- Dukkan wasannin tana yin nasara ne da rarar ƙwallo ɗaya tsakani.
- Karawar cikin rukuni da ta yi nasarar cin ƙwallo fiye da ɗaya ita ce a kan Guinea-Bissau da ta ci 2-0 a 2019.
- Idan har Najeriya ta yi nasara a kan Uganda, zai zama ta lashe dukkan karawa uku a cikin rukuni a karon farko tun bayan 2021.
- Super Eagles ta zura ƙwallo a raga a wasa tara baya a Afcon - wasan da ba ta ci ƙwallo ba shi ne a zagayen ƴan 16 da Tunisia ta doke ta a 2021.
- Haka kuma ta kan zura ƙwallo a raga a wasa takwas baya a karawar cikin rukuni a Afcon, rabon da ta kasa cin ƙwallo a wasan karshe a cikin rukuni tun 2019 da ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Madagascar.
- Tun daga 2010 Najeriya ta ci ƙwallo takwas da ka a Afcon, Kamaru ce kan gaba a wannan bajintar mai 11 da kuma Ivory Coast mai 10.
- Victor Osimhen ya ci ƙwallo na biyu a Afcon a wasan Tunisia - ta farko da Equatorial Guine a 2023 da suka tashi wasa 1-1 a karawar farko a cikin rukuni.
- Dukkan ƙwallayen da Osimhen ya ci Ademola Lookman ne ke bashi su da yake ci da kai.
- Osimhen ya ci ƙwallo shida a wasa biyar baya a dukkan karawa a Najeriya.
- Ƙwallon da Ademola Lookman ya ci da bayar da biyu aka zura a raga a karawa da Tunisia ya zama na biyu da yake da hannun a cin ƙwalo uku a wasa ɗaya tun bayan ƙwazon Odion Ighalo a wasa da Kamaru a 2019 (ya zura biyu a raga ya kuma bayar da ɗaya aka ci).
- Kenan Lookman ya zura ƙwallo biyar a raga a AFCON.
- A wasa tara da Lookman ya yi, yana da hannu a cin ƙwallo takwas, wanda ya zura biyar a raga ya bayar da uku aka ci.
- An ci Najeriya ƙwallo a kowanne wasa huɗu baya a Afcon - wasan karshe da ta yi ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba tun 1-0 da ta doke Angola a kwata fainals a 2023.












