Lukashenko: Ba wanda zai yi wa Rasha bore ya yi nasara

Alexander Lukashenko ne ya ƙulla yarjejeniyar kawo ƙarshen tawayen da mayaƙan Wagner suka yi.
Don haka idan akwai wanda zai iya ƙarin haske kan wannan lamarin, tabbas shi ne, shugaban na Belarus. Haka dai muke sa rai.
BBC na cikin rukunin 'yan jarida da aka gayyata zuwa Fadar Independence da ke birnin Minsk don "tattaunawa" da Mista Lukashenko.
Makonni kaɗan da suka gabata ne aka yi ta ce-ce-ku-ce game da lafiyarsa. Amma shugaban Belarus ya nuna a zahiri cewa yana da ƙarfinsa. "Tattaunawar" ta ɗauki kusan sa'o'i huɗu.
Maimakon ya ƙara mana haske, sai ya ƙara dagula labarin tawayen da aka yi a Rasha na baya-bayan nan.
Bisa yarjejeniyar da aka yi tsakanin kungiyar Wagner da Kremlin, shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin ya kamata ya koma Belarus, tare da wasu mayaƙansa.
Hakan bai faru ba. Har ya zuwa yanzu dai.
"Ya zuwa safiyar yau," in ji Mista Lukashenko, "mayaƙan Wagner, suna cikin sansanonin da suka koma bayan Bakhmut.
"Kan batun Yevgeny Prigozhin, har yanzu yana St Petersburg, sai dai in da safiyar yau ne ya tashi zuwa Moscow. Ko kuma wataƙila yana wani wuri daban, amma dai ba ya Belarus.''
Na tambayi Alexander Lukashenko ko hakan yana nufin yarjejeniyar ta wargaje ke nan.
Ya musanta hakan. Amma muna gani kamar ana tattaunawa a bayan fage da ba za a gaya mana ba.

Asalin hoton, BELARUS PRESIDENTIAL POOL
Babu jituwa tsakanin Moscow da Minsk kan batun tawayen.
A karshen makon da ya gabata gidan talabijin na ƙasar Rasha ya bayyana cewa Shugaba Vladimir Putin ya fito daga cikin abubuwan da suka faru a matsayin jarumi.
"Ina tsammanin babu wanda ya fito daga cikin wannan yanayin a matsayin jarumi," in ji Mista Lukashenko.
"Ba Prigozhin ba, ba Putin ba, ba Lukashenko ba. Babu jarumai. Kuma darussan da ke cikin wannan? Idan muka ƙirƙiri ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai irin wannan, muna buƙatar sa ido a kansu tare da kula da su sosai."
"Tattaunawar" ta ci gaba kan batun makaman nukiliya. Musamman ma, makaman nukiliyar da Rasha ta girke a Belarus.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Allah Ya kiyaye ranar da zai kai in yanke shawarar yin amfani da su," in ji Mista Lukashenko kwanan nan, ya kara da cewa, "amma ba zan yi shakkar amfani da su ba."
Na tunatar da shi waɗannan maganganun.
"Joe Biden na iya faɗar magana irin wannan, ko Firaminista Sunak," in ji Mista Lukashenko. "Da kuma abokina Xi Jinping da kuma babban yayana Shugaba Putin."
"Amma waɗannan ba makamanku ba ne muke magana akai," na nuna masa. "Makaman Rasha ne, hakkin yanke shawara a kansu ba naku ba ne."
Shugaban Belarus ya mayar da martani ya ce "A Ukraine gaba daya sojoji suna faɗa da makaman ƙasashen waje ne, ko ba haka ba." "Makaman Nato. Domin sun ƙarar da nasu. To me ya sa ba zan iya faɗa da makaman wasu ba?"
Amma muna magana ne game da makaman nukiliya, ba bindiga ba, na amsa masa.
"Nukiliya, ƙwarai. Su ma makamai ne. Ƙananan makaman nukiliya."
Daga maganganunsa na nukiliya za ku iya tabbatar da cewa Alexander Lukashenko mutum ne mai jayayya.
Amurka, da EU da Birtaniya ba su amince da shi a matsayin halastaccen shugaban ƙasar Belarus ba.
A shekarar 2020 'yan kasar Belarus sun fantsama kan tituna suna zarginsa da murɗe zaben shugaban ƙasar.
Da ƙarfin tsiya aka murƙushe zanga-zangar.
Na ambaci shari'ar 'yar gwagwarmayar adawa Maria Kolesnikova da aka ɗaure.
"Tsawon watanni an hana 'yan uwanta da lauyoyinta shiga gidan yari, me ya sa?" Na yi masa tambaya.
"Ban san komai game da wannan ba," in ji shi.
Na tunatar da Mista Lukashenko cewa, "Lokacin da na yi hira da kai a kakar shekarar 2021, akwai fursunonin siyasa 873 a Belarus," . "Yanzu akwai 1,500."
"Babu wani shafi a cikin kundin dokokinmu da ya shafi laifukan siyasa," in ji shi.
Rashin wani shafi kan laifukan siyasa ba yana nufin babu fursunonin siyasa ba ne, na nuna masa.
" Fursunonin ba za su iya zama fursunonin siyasa ba, idan babu shafi," in ji shi. "Yaya za su kasance hakan?"











