Trump ya tura dakaru domin murƙushe tarzomar kama baƙin haure a Los Angeles

Asalin hoton, OTHERS
Shugaban Amurka Donald Trump ya tura jami'an rundunar taro ta tarraya 2000 domin murkushe tarzomar da ta biyo bayan, kamen bakin haure a wata gunduma da yawanci mazaunanta 'yan asalin Latin Amurka ne a birnin Los Angeles.
Matakin ya biyo bayan zanga-zangar da aka shiga kwana na biyu ana yi tsakanin mazauna yankin da kuma jami'an shige da fice da na kwastan da ke kama bakin haure don fitar da su daga kasar.
Umarnin da Shugaba Trump ya bayar na tura jami'an rundunar tsaron ta tarayya domin tabbatar da tsaro da kuma aiwatar da shirin nasa na zakulowa da kame bakin haure a gundumar ya gamu da suka daga gwamnan jihar ta California Gavin Newsom.
Gwamnan ya ce abu ne na tsabar rashin Imani, da zai kara dagula halin da aka shiga na tarzoma a kwana na biyu.
Shi kuwa shugaban hukumar kula da iyakokin kasar Tom Horman, ya ce sun yi hakan ne domin kare birnin na Los Angeles.
A ranar Asabar gwamnan ya kira Trump ta waya inda suka tattauna kusan tsawon minti 40, kamar yadda kakakin gwamnan ya sheda wa kafar yada labarai ta CBS, - mai mu'amulla da BBC a Amurka.
Kakakin bai bayar da wani karin bayani a kann tattaunawar da mutanen biyu suka yi ba.
Jami'an na amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma kulki domin tarwatsa masu tarzomar da ke arangama da jami'an a wannan gunduma da galibi mazaunanta Hispaniyawa ne wato – 'yan asalin Latin Amurka.
A wannan makon an kama akalla mutum 118 a birnin na Los Angeles, karkashin shirin na fitar da bakin haure daga Amurkar.
Rahotanni na cewa kusan al'amura sun kwanta a yankin da ake tarzomar amma kuma ana ci gaba da dauki-ba-dadi tsakanin masu tarzomar da jami'an da ke kamen bakin hauren.
Har yanzu yankin da aka fara zanga-zangar na murtuke da hayaki mai sa hawaye – in da jami'an kamen ke kokarin kawar da masu tarzomar.
Makwabta da masu zanga-zangar sun ce akwai baki da aka rufe a shaguna da sauran kantina na hada-hadar kasuwanci , da ke tsoron idan suka fito za a kama su.
Sama da kashi 80 cikin dari na mazauan wannan gunduma Hisfaniyawa ne.
Wata sanarwar manema labarai da fadar gwamnatin Amurka ta fitar a kwanan nan ta nuna cewa, jami'na da ke kamen bakin hauren na gamuwa da mummunan hari daga gungun masu adawa da shirin a birnin Los Angeles na jihar ta California.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sanarwar ta ce, ana kamen ne domin dakatarwa da kuma mayar da al'amura yadda suke ainahi a da, na hana kutsen bakin haure a Amurka, kamar yadda wannan sanarwa ta ce.
Sanarwar ta kara da cewa kasancewar hukumomin jihar ta California, 'yan Democrat sun ki sauke nauyin da ya rataya a wuyansu nak are 'yan kasa, hakan ya sa Shugaba Trump ya bayar da umarnin tura jami'an tsaro 2000 na rundunar tarayya, don maganin tarzomar da aka bari tana ta ruruwa.
Shugaban hukumar kula da iyakokin kasar ta Amurka wanda ya je birnin shi da kansa ya lashi takobinaiwatar da Shirin na kame da korar bakin hauren – ko ana ha maza ha mata a cewarsa.
Tun da farko shugabar birnin na Los Angeles Karen Ruth Bass ta zargi jami'an da ke kamen bakin hauren da abin da ta kira dasa ta'addanci a birni na biyu mafi girma a Amurka.
Shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta tarayya FBI da takawaransa na hukumar tsaron cikin kasar sun sun ce kalaman shugabar birnin na jefa rayuwar jami'an tsaron tarayya cikin hadari.










