Da gaske Trump zai kori baƙi miliyan ɗaya daga Amurka?

g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi ta ɗaga kwalaye masu ɗauke da saƙon neman korar baƙi a wuraraen yaƙin neman zaɓen Trump
Lokacin karatu: Minti 5

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya alƙawurta gagarumar korar mutanen da ba su da cikakkun takardun izinin zama a ƙasar.

Yayin da tawagar yaƙin neman zaɓensa ta bayar da amsa kan adadin mutanen da Donald Trump ɗin zai kora, ɗan takarar mataimakinsa, JD Vance ya ambata wani adadi a lokacin wata hira da kafar yaɗa labaran ABC cikin wannan makon.

"Za mu fara da miliyan guda,” in ji. “A wannan ɓangaren ne kuma Kamala Harris ta gaza. Kuma daga nan za mu fara''.

Amma duk da batun korar bakin na cikin ƙudurorin Donald Trump, har ma ta kai ga ana ɗaga kwalayen da ke ɗauke da saƙonnin ''A kori baƙi masu yawa yanzu'', Masana na cewa akwai matsaloli na shari'a da sauran fannoni dangane da korar baƙi masu yawa.

Waɗanne ƙalubalen shari'ar zai fuskanta?

Alƙaluman baya-baya nan daga sashen tsaron cikin gida da binciken cibiyar Pew sun nuna cewa akwai kusan baki miliyan 11 da ba su da cikakkun takardun izini da ke zaune a Amurka, kuma bincike ya nuna cewa adadin kusn bai sauya sosai ba tun 2005.

Da yawa daga cikinsu sun jima suna zaune a ƙasar, kusan kashi hudu cikin biyar na adadin na zaune a ƙasar fiye da shekara 10.

'Yan cianin da ke zaune a ƙasar, ba bisa ƙa'ida ba na da 'yancin ba su matakan da dace don fitar da su daga ƙasar, ciki har da hukuncin kotu kafin fitar da su daga ƙasar.

Matsalar rage baki a ƙasar zai iya haifar da ƙaruwar shari'o'in fitar da baƙi a kotunan 'yancirani a ƙasar, waɗanda dama cike suke da shari'o'in baki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kathleen Bush-Joseph, mai sharhi kan tsare-tsaren baƙin haure, a jami'ar Washington, ta ce za a yi haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da jami'an shige-da fice na yankunan a wani ɓangare na korar baƙin.

"Gwamnati za ta zaƙulo baƙin hauren a gidajen yari bayan jami'an shige da fice sun gurfanar da su a a kotu an kuma yanke musu hukuncin tsarwa, maimakon gamnati da kanta ta shige farautarsu''.

Alal misali, Ms Bush-Joseph ta yi nuni da sanarwar da aka yi a farkon watan Agusta daga ofisoshin ofisoshin ƙananan hukumomin Broward na Florida da Palm Beach, inda suka ce ba za su tura wakilai don taimaka wa duk wani shirin korar jama'a ba.

"Akwai wasu da yawa da ba za su ba da hadin kai ba da shirin Trump na korar baƙi daga ƙasar," in ji ta. "Hakan ya kara wa shirin wahala."

Duk wani shirin korar baƙi na iya fuskantar ɗimbin ƙalubalen shari'a daga ɓangaren shari'a da masu fafatiar kare haƙƙin bil'adama.

Duk da haka kuma , hukuncin Kotun Koli na 2022, na nufin cewa kotuna ba za su iya ba da umarni kan manufofin tilasta korar baƙi ba.

..

Asalin hoton, Getty Images

Ko hakan zai yiwu a kan ka'ida?

Idan gwamnatin Amurka ta sami damar ci gaba da korar jama'a, hukumomi zasu fuskansu ƙalubale da dama.

A lokacin gwamnatin Biden, yunkurin korar ya mayar da hankali ne kan baƙin hauren da aka tsare kwanan nan a kan iyaka. Amma baƙin haure da aka kora daga yankunan da basa kusa da yakokin Amurka suna da yawa kuma da dama daga cikinsu masu laifi ne da suke barazana ga tsaron ƙasar.

An dakatar da samamen da ake kaiwa a wuraren aiki lokacin mulkin Trump a shekara ta 2021.

Korar mutanen da aka kama a cikin Amurka saɓanin waɗanda ke kan iyaka ya yi ƙasa da 100,000 tsawon shekaru goma, bayan da ya kai sama da 230,000 a farkon shekarun gwamnatin Obama.

Masana na shakkar ko jami'ai 20,000 na Ice tare da ma'aikatan sa kai zasu iya iya samo alƙaluman da aka bayyana a lokacin yaƙin neman zaɓen Trump.

Mista Reichlin Melnick ya ƙara da cewa aikin korar yana ɗaukar lokaci mai tsawo kuma ana farawa ne da kamo baƙin haure da ba su da takardun shaida.

Daga nan sai a ajiye wadanda aka kama a wani matsuguni kafin gabatar da su gaban Alkalin ƴan gudun hijira ƙarkashin wani tsari da aka jima ana amfani da shi.

A nan ne kawai za a iya fidda waɗanda aka kama ɗin daga Amurka, tsari ne da ya ke buƙatar diflomasiyya daga ƙasar da zata karɓe su

"A kowane ɗayan waɗannan wuraren, Ice ba ta zata aiki kan miliyoyin mutanen ba, "in ji Mista Reichlin-Melnick.

Trump ya ce zai yi sanya Dakarun National Guard ko sojojin Amurka don su taimaka a kari baƙi.

A tarihi rawar da sojojin Amurka ke takawa a al'amuran shige da fice ta taƙaitu ga ayyukan taimako a kan iyakar Amurka da Mexico.

Bayan amfani da sojoji da jami'an tsaron yanki. Trump ya ba da cikakkun bayanai kan yadda za a iya aiwatar da irin aiki na korar jama'a.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Aikin fidda baƙin hauren zai buƙaci ƙarin kuɗaɗe.

Tasirin hakan a siyasa da tattalin arziƙi

Masana sun yi ƙiyasin cewa jimillar kuɗin fitar da mutane miliyan ɗaya ko fiye zai kai dubu ko ma ɗaruruwan biliyoyin daloli.

Kasafin kudin hukumar Ice na sufuri da kora a shekara ta 2023 ya kai daka miliyan ɗari huɗu da asirin $420m daidai da fan miliyan ɗari uku da asirin da bakwai (£327m). A bara hukumar ta kori mutane fiye da 140,000.

Za a tsare dubban baƙin haure ya yinda suke jiran zaman kotu ko fidda su daga ƙasar, kodayake Trump ya yi hasashen gina babban sansani don tsugunar da su baki daya.

Adam Isacson, wani masani kan ƙaura da iyakoki daga Washington ya ce "Hotun korar jama'a masu tayar da hankali na iya haifar da matsala a siyasar Trump ɓangaren hulɗa da jama'a..

"Kowacce unguwa a Amurka zata ga yadda za a sanya mutanen da ta ke so da ƙauna cikin motoci don fidda su daga Amurka," cewar Mista Isacson.

Ko an taɓa aikin korar baƙin haure da dama a baya?

A ƙasa da shekaru hudu na gwamnatin Trump da ta gabata, an kori mutane kusan miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar daga kan iyaka da cikin Amurka.

Gwamnatin Biden wadda ta kori kusan mutane miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya zuwa watan Fabrairu wannan shekara ta 2024 tana da alamun nasara a aikin kamar yadda ƙididdiga ta nuna.

A cikin wa'adi biyu na gwamnatin Obama lokacin Mista Biden na mataimakin shugaban kasa an kori fiye da mutane miliyan uku, lamarin da ya sa wasu masu fafutukar kawo sauyi kan shige-da-fice suka kira Barack Obama a matsayin "shugaban masu korar baƙi''.

Kwatancen tarihi daya tilo da shirin korar jama'a ya faru a shekara ta 1954, lokacin da aka kori mutane kusan miliyan ɗaya da dubu dari uku wani aiki mai taken Operation Wetback, a baya ana amfani da wannan suna don ɓatanci ga mutanen Mexico.

Kodayake an samu bambancin adadin tsakanin masana tarihi.

Shirin, karkashin Shugaba Dwight Eisenhower ya fuskanci mummunar suka daga jama'a saboda an kori wasu ƴan asalin ƙasar ta Amurka sannan kuma an fuskanci ƙarancin kuɗaɗe a shekara ta 1955.