Bakin haure: Donald Trump na kara fuskantar matsala

Asalin hoton, Getty Images
Dubban mutane ne ake sa ran za su fita kan tituna a Amurka domin shiga zanga-zangar nuna adawa da manufofin bakin-haure na gwamnatin Shugaba Donald Trump - ciki har da batun nan na raba iyaye da 'ya'yansu.
An shirya tarurruka sama da 750 a duka fadin kasar, wadanda ake yi wa taken "iyalai a dunkule su ke a ko'ina".
An shirya wannan macin ne tun kafin Shugaba Trump ya soke shirinsa na raba iyaye da kananan 'ya'yansu a kan iyakar Amurka da Mexico.
Sai dai wadanda suka shirya zanga-zangar sun ce ta dace a yi ta a kowanne lokaci idan dai har manufar nan da ake kira Zero Tolerance a Turance - wato nuna rashin sani ko sabo kan bakin haure tana nan a tsarin kasar.
Batun wasu yara kimanin 2,000 da har yanzu ba a kai ga mayar da su hannun iyayensu ba - duk da umarnin da shugaban kasar da kuma wani alkali suka bayar - shi ne ke kara rura wutar lamarin.
Wadanda suka shirya macin na kira da a kawo karshen tsare 'yan ci-rani, ko da kuwa a lokutan da aka raba iyalai.
Suna da kuma da aniyar nuna adawarsu da dokar hana mutane shiga kasar daga wasu kasashen Musulmi biyar, wadda kotun kolin kasar ta tabbatar a makon nan.
Wannan ka iya zamowa zanga-zanga mafi girma da aka taba yi kan batun bakin haure ko 'yan ci-rani, lamarin da ke kara fito da rabuwar kawuna a kasar a karkashin gwamnatin Mr Trump.











