Trump ya yi barazanar ƙaƙaba wa Rasha takunkumi kan yaƙin Ukraine

Mark Rutte da Trump ranar Lahadi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Donald Trump ya ce Amurka za ta aikewa Ukraine da manyan makamai na biliyoyin dala, tare da barazanar ƙaƙabawa Rasha da abokan kasuwancin ta ƙarin haraji, idan har Moscow ba ta amince da tsagaita wuta nan ba da jimawa ba.

Yayin wani taro da sakatare janar na ƙungiyar tarayyar Turai, Mark Rutte, Mr Trump ya bai wa Rasha wa'adin kwana 50 ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Ukraine.

Wannan mataki gagarumin sauyi ne daga yadda aka saba ganin Donald Trump na amfani da salon diflomasiyya wajen neman kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine.

Kafin yanzu dai tallafin makaman da Ukraine ta samu daga Amurka duk sun fito ne daga gwamnatin Biden, amma a yanzu Trump na nuna alamar sake tallafawa Kyiv da manyan makaman kai hare-hare, ba iya na bayar da kariya ba, ciki harda waɗanda za su iya kaiwa can cikin Rasha idan aka harba su.

Sai dai ya gindaya sharadin cewa tarayyar Tura ice za ta biya dukkan kuɗin makaman da Amurka za ta bai wa Ukraine.

Shugaba Trump ya kuma aike da wani saƙo na ba-zata ga ƙasashen tarayyar Turai masu yin hannun riga da tsare-tsarensa.

Haka nan kuma kalaman shugaba Trump game da takwaransa na Rasha a ƴan kwanakin nan sun fara ɗaukar zafi, musamman bayan mummunan harin da Rasha ta kai Ukraine jim kaɗan bayan tataunawarsa da Putin ta waya.

A yanzu dai, Mr Trump ya ce yana cikin fushi da shugaban Rasha kuma ya bai wa Mr Putin wa'adin kwana 50 ya ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta, ko kuma ya ƙaƙaba manyan takunkumi a kan Moscow da ƙawayen ta, irin su China da India.

Shi ma Mr Rutte ya bayar da tabbacin cewa Amurka za ta bai wa Ukraine kayan yaƙin da ta ke buƙata kuma ƙungiyar tarayyar Turai ce za ta biya kuɗin makaman da kuma shigewa gaba wajen miƙa su ga Ukraine.

Trump ya ce su ma ƙasashen tarayyar Turai za su bai wa Ukraine tallafin kayan yaƙi, musamman na kare sararin samaniya, domin hana Rasha kai mata munanan hare-hare.

Daga Rutte har Trump babu wanda ya bayyana irin makaman da za a bai wa Kyiv, amma Mr Rutte ya ce za a haɗa da makami mai linzami.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a wani saƙo na shafinsa na X ya ce sun tattauna da shugaba Trump, inda ya yi masa godiya a kan tallafinsa ga Ukraine domin ta kare kanta.