Icardi zai yi jinyar watanni tara ko sama

Lokacin karatu: Minti 1

Dan wasan gaban Galatasaray Mauro Icardi zai yi jinya har zuwa ƙarshen wannan kakar saboda karayar da ya samu a ƙafarsa a wasan da suka fafata da Tottenham a gasar Europa.

Dan wasan Argentinan an yi ta duba shi kusan mintina biyar gabanin a fitar da shi daga filin a wasan da suka yi nasara kan Tottenham da ci 3-2.

Icardi mai shekara 31 ya faɗi ƙasa ne lokacin da yake ƙoƙarin tare kwallon da golan Tottenham Fraser Forster ya buga.

Kungiyar ta Turkiyya ta ce tsohon ɗan wasan PSG za a fara yi masa ƙaramin aikin farfaɗowa daga raunin gabanin a yi masa babban aikin da zai yi jinya.

Tsawon lokacin da ake ɗauka a jinyar karayar yagewar nama tsakanin 'yan kwallo yana farawa ne daga wata shida zuwa tara.

Icardi ya koma Turkiyya ne a 2022 a matsayin aro na kaka guda daga PSG, daga baya kuma ya koma ƙungiyar a matsayin cikakken ɗan wasanta.

Ya ce kwallo 61 cikin wasa 86 da ya bugawa ƙungiyar ta Istanbul.