Gidan yarin Venezuela da ya yi ƙaurin suna wajen azabtar da 'yansiyasa

Asalin hoton, Daniel Arce-Lopez/BBC
- Marubuci, Norberto Paredes
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- Lokacin karatu: Minti 5
"Sun azabtar da ni, amma ba za su iya hana ni magana ba. Muryata kaɗai nake da ita a yanzu."
A haka Juan mai shekara 20 ya fara bayar da labarinsa. Ya yi iƙirarin cewa an azabtar da shi a jiki da kuma ƙwaƙwalarsa a wani gidan yarin Venezuelan bayan zargin sa da hannu a abin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na 28 ga watan Yuli.
Yana ɗaya daga cikin gomman mutanen da aka kama a wurin zanga-zanga kan sakamakon zaɓen da hukumomi suka sanar da Shugaba Nicolás Maduro a matsayin wanda ya lashe shi.
Ba a bayyana bayanan da suka dace game da zaɓen ba, dalilin da ya sa kenan 'yan'adawa da wasu ƙasashen duniya suka ce an yi maguɗi.
Adadin mutanen da aka kama kamar yadda gwamnati ta bayyana sun bai wa mutane mamaki. A farkon watan Agusta, Maduro ya ce tuni aka "'yanta'adda 2,229".
An saki Juan daga gidan yari a tsakiyar watan Nuwamba, 'yan kwanaki bayan Maduro ya nemi shugabannin sashen shari'a su "gyara" duk wani zalinci da aka yi wajen kama mutanen.
BBC ta yi magana da shi ta bidiyo. Saboda tsaron lafiyarsa, ba za mu faɗi wasu labaran ba game da shi, sannan mun sauya sunansa.
Ya nuna wa BBC wasu takardu da hujjoji da suka tabbatar da labarinsa, waɗnda kuma suka yi daidai da sauran labarai da ƙorafin da wasu ƙungiyoyi suka yi.

Asalin hoton, Reuters
Juan mai fafutika ne kuma mai sukar gwamnati. Ya ce sun samu ƙwarin gwiwa kafin fara kaɗa ƙuri'a, inda mutane suka dinga shirin sauya gwamnati.
Amma sanar da nasarar Maduro ya jefa mutane cikin ruɗani da ɓacin rai.
Dubban 'yan Venezuela ne suka fantsama kan tituna domin zanga-zangar adawa da sakamakon.
'Yan'adawa da ƙungiyoyin ƙasashen duniya sun ce an kashe aƙalla mutum 20 a zanga-zangar.
Gwamnatin ƙasar kuma ta zargi 'yan'adawar da haddasa wasu mace-macen.
Foro Penal, wata ƙungiyar adawa da gwamnati a Venezuela, ta ce an tsare mutum 23 kuma daga baya aka neme su aka rasa.
"Babu wanda ya san inda suke a yanzu kuma muna da tabbacin cewa kama su aka yi," a cewar wani lauya a Venezuela Gonzalo Himiob kuma mataimakin shugaban Foro Penal.
Gwamnatin Venezuela ba ta ce komai ba game da rahoton mutanen da suka ɓace.
Juna ya ce yana cikin mutanen da aka kama daga baya.
'Sansanin azabtarwa'

Asalin hoton, Daniel Arce-Lopez/BBC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Matashin ɗan gwagwarmayar ya ce yana tsaka da harkokinsa lokacin da wasu mutane sanye da riga mai hula suka tsare shi, suka rufe masa fuska tare da zargin sa da zama ɗanta'adda.
"Sun jefa min bam da ake haɗawa da fetur, sannan suka kai ni wani wurin ajiye mutane," a cewarsa.
An tsare shi a wani gidan yari da ke birnin Caracas tsawon makonni, har zuwa lokacin da aka mayar da shi Tocorón, wani ƙasurgumin gidan yari mai nisan kilomita 140 daga Caracas.
"Lokacin da muka isa Tocorón, sun yi mana tsirara, suka dake mu, suka ci mutuncinmu. An hana mu ɗaga kai mu kalli masu gadi, dole ne mu yi ta kallon ƙasa kodayaushe," in ji Juan.
An jefa Juan cikin wani ƙaramin kurkuku mai girman mita uku, inda suka zauna tare da wasu mutum biyar.
Akwai gado shida a gefe guda, akwai wani "tanki mai fanfo da ake amfani da shi a matsayin wurin wanka". Shi ne banɗakin wanka.
"A Tocorón, na ji kamar ina wani sansanin azabtar da mutane ne ba gidan yari ba," a cewar matashin.
"Sun azabtar da mu a jikinmu da ƙwaƙwalwarmu. Ba su bari mu yi barci, kodayaushe sukan zo su nemi mu nuna katinmu da shaida."
Ya ƙara da cewa wajen ƙarfe 6:00 ake kunna ruwan famfo na tsawon minti shida domin su yi wanka.
"Cikin minti shida mutum shida za su yi wanka da ruwa mai sanyin tsiya. Idan kai ne na ƙarshe kuma ba ka yi hanzarin cire kayanka ba, za kashe ruwan a bar ka da kumfa a jiki," kamar yadda ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa sai su koma jiran abinci safe, wanda kan ɗauki lokaci kafin a kawo da kamar ƙarfe 6:00, wani lokacin kuma har 12:00.
Wani lokacin suka samu abincin dare da ƙarfe 9:00 na dare, ko kuma 2:00 na daren wani lokacin.
"Baya ga jiran abinci, babu wani abin da muke yi. Sai dai kawai mu dinga tafiya a cikin ɗakin muna bai wa juna labari. Mukan yi magana kan siyasa amma murya ƙasa-ƙasa, saboda idan masu gadi suka jiyo za su hukunta mu."
'Yawan duka'
Juan ya ce da yawa daga cikin abokan zamansa a gidan yarin sun shiga tsananin damuwa har ma sun koma kamar dabbobi.
"Sukan ba mu ruɓaɓɓen abinci - naman da ake bai wa karnuka ko kaji, ko kuma kifin gwangwani da ya riga ya lalace."
Akan yi wa wasu duka akai-akai, ko kuma a dinga saka su yin tsallen kwaɗo, in ji shi.
Ya ce akan tura waɗanda ake yi wa kallon masu taurin kai zuwa ɗakuna na musamman, ko kuma waɗanda suke magana kan siyasa, ko kuma masu neman su kira 'yan'uwansu ta waya.
Juan ya ce an kai shi ɗaya daga cikin ɗakunan horon a gidan yarin Tocorón, kuma wai sau ɗaya kacal ake ba su abinci cikin kwana biyu.
"Kurkuku ne mai duhu sosai. Na ji yunwa sosai. Abin da ya ƙara min ƙarfin gwiwa kawai shi ne tunanin duk irin zalincin da ke faruwa, da tunanin cewa wata rana zan fito daga ciki," a cewarsa.
Wani ɗakin horon da ya shahara shi ne "Adolfo's bed", in ji Juan, wanda aka raɗa wa sunan mutum na farko da ya mutu a ciki.

Asalin hoton, Daniel Arce-Lopez/BBC
'Na daina jin tsoron gwamnati a yanzu"

Asalin hoton, Getty Images
A cewar Juan, da yawa daga cikin tsararrun na Tocorón na tunani ne kawai game da ranar 10 ga watan Janairu.
Sun yi ta fatan za a sake su a ranar saboda lokacin ne za a miƙa mulki bayan gama zaɓen shugaban ƙasar.
Jagoran 'yan'adawa Edmundo González ya ayyana kan sa a matsayin wanda ya ci zaɓe, kuma ya haƙiƙance cewa zai koma ƙasar daga gudun hijira a Sifaniya domin kama mulki.
Juan ya amince cewa ya ɗan yi da-na-sani saboda har yanzu "akwai ɗaruruwan abokan gwagwarmayarsa" a gidan yari, amma ya ce sun tsara komawa kan tituna don yi wa Edmundo González rakiya ranar 10 ga watan Janairu duk da barazanar da aka yi masa lokacin da aka sake shi.
"Ba na jin tsoro," in ji Juan yana mai cewa ya bar wata wasiƙa "ko da wani abu zai faru da shi".










