Golan PSG Donnarumma zai yi jinyar raunin da ya ji

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron ragar Paris St-Germain, Gianluigi Donnarumma ya ji mummunan rauni a fuskarsa abin da ya kai ga an cire shi daga wasan da suka yi nasara 4-2 kan Monaco a Lig 1.
Dan wasan bayan Monaco Wilfried Singo ya taka fuskar golan na Italiya kuma sai an yi masa dinki 10 a ƙalla domin rufe ciwo.
Matvey Safonov ne ya maye gurbinsa a minti na 22 da fara wasa lokacin da ake 0-0. Ba dai a yi wa Singo ko wanne irin hukunci ba, duk da cewa ya ji masa rauni ko da yake ya yi ba da niyya ba ne.
Kocin ƙungiyar Luis Enrique ya ce: "Hukuncin alƙalin wasan? Ba zan ce komai a kai ba, Ban ga matakin da ya ɗauka ba, amma ganin lamari irin wannan abu ne mai wuya ko da yaushe.
"Dan wasan bai je da nufin cutar da golanba. Akwai wuya alƙalancin irin wannan wasan, amma ba ina magana ba ne kan aikin lafari ba."
A wata sanarwa da suka fitar bayan wasan, PSG ta ce za a yi wa golan gwaji a asibiti a ranar Alhamis kuma dole "ya huta na wani lokaci".
Osmane Dembele ne ya ci kwallo biyu a wasan bayan da Derire Doue ya ci kwallo sannan Ramos ma ya ci, yanzu PSG na sama teburi da maki 10 tazara.







