Muna sane da ƙalubalen da ake fuskanta a wasu yankuna - INEC

Shugaban hukumar zaɓen Najeriya (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumar na lura tare da sanya ido game da yadda zaɓe ke gudana a faɗin ƙasar.

Ya ce hukumar ta samu rahotonnin wasu 'yan matsaloli nan da can, to sai dai hukumar a shirye take wajen magance matsalolin.

A yau ne dai hukumar ke gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya.

Farfesa Mahmud ya ƙara da cewa burin hukumar shi ne tabbatar da samun sahihi da ingantaccen zaben a ƙasar.

Farfesa Yakubu ya ce wannan shi ne karo na farko da hukumar ke gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara ba tare da ɗage zaɓen ba.

Ya ce ana ci gaba da zaɓe a faɗin ƙasar, kuma na'urar BVAS da ake amfani da ita tana aiki yadda ya kamata a wurare da dama a faɗin kasar.

Ya ce rahotonnin da hukumar ke samu daga ofisoshin hukumar na jihohi da birnin tarayya na nuna cewa ƙorafe-ƙorafen da jama'a ke yi game da aikin na'urar BVAS na ci gaba da raguwa.

"Haka kuma mun gano wasu matsaloli, ɗaya daga cikin matsalolin da muka fuskanta ita ce ta rashin samun damar buɗe rumfunan zaɓe a kan lokacin da aka tsara za a buɗe su da misalin ƙarfe 8:30 na safe."

Farfesa Yakubu ya ce an buɗe wasu rumfunan zaɓen a ƙurarren lokaci, ya kuma alƙawurta cewa duk mutumin da yake kan layi kafin ƙarfe 2:30 na rana to za a bar shi ya kaɗa ƙuri’arsa komai daɗewa.

Shugaban INEC ɗin ya ce wasu dalilan da suka sanya ba a buɗe rumfunan zaɓen a kan lokaci ba, an same su ne sakamakon matsalolin da aka samu wajen rarraba kayan aikin zaɓen duk kuwa da irin shirin da hukumarsa ta yi wajen ganin aikin ya tafi ba tare da wata matsala ba.

Ya ce hukumar ta samu nasarar kai kayan aikin zaɓe wurare da dama a kan lokaci kamar yadda aka tsara.

Ya kara da cewa wata matsalar da aka fuskanta ita ce Matsalar tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.

Ya ce ‘’alal misali ba mu samu nasarar kai kayan aikin zaɓe a mazaɓar Alawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja ba, saboda ‘yan fashi sun kai hari yankin’’, don haka ne ma jami’an tsaro suka ba mu shawarar jinkirta zuwa wajen na ɗan wani lokaci.

‘’Kuma ina farin sanar da ku cewa a halin yanzu an kai jami’an zaɓe kuma aikin zaɓen na tafiya kamar yadda ya kamata a halin yanzu," in ji shi.

Haka kuma a yankin ƙaramar hukumar Oshimili ta jihar Delta wasu ‘yan daba sun kai hari wata rumfar zaɓe tare da sace na’u’rorin BVAS guda biyu.

Amma a ƙoƙarinmu na tabbatar da an gudanar da zaɓen, mun sake aikawa da wasu na’urorin BVAS ɗin bayan da jami’an tsaro suka daidaita al’amura, domin tabbatar da ci gaba da zaɓen kamar yadda aka tsara.

Haka kuma a ƙaramar hukumar Safana ta jiha Katsina, nan ma shugaban INEC ɗin ya ce ‘yan daba sun kai wa wata rumfar zaɓen hari tare da ƙwace na’urorin BVAS guda shida, inda nan ma ya ce hukumar ta sake aika wasu na’urorin domin tabbatar da ci gaban aikin zaɓen bayan da jami’an tsaro suka magance matsalar.

Shugaban INEC ɗin ya ce jami’an taro sun samu nasarar ƙwato na’urorin BVAS ɗin uku, inda har yanzu uku ke hannun waanda suka kai harin.

Ya ƙara da cewa an ƙaddamar da harin ne kan na’urorin na BVAS kawai, ba takardun kaɗa ƙuri’a ko akwatunan zaɓe ba.

Ya ƙara da cewa hukumar zaɓen ta samu wasu ƙorafe-ƙorafe daga jam’iyyu kan ƙarancin katin shaidar wakilan jam’iyyu a wasu rumfunan zaɓen.