Daga wannan World Cup din zan yi murabus a Argentina

Lionel Messi ya ce daga kofin duniyar da za a yi a Qatar a watan Nuwamba, zai yi murabus daga bugawa Argentina wasa.

Dan shekara 35 din da yake taka leda a Paris St-Germain ya buga wa Argentina kofin duniya hudu, ya ci ya ci kwallo shida ya kuma taimaka an ci biyar a wasa 19.

A 2014, ya kai kasarsa matakin karshe na gasar, sannan a 2021 ya taimaka wa kasar ta lashe Copa America, kuma World Cup ne kawai ya zamarwa dan wasan koma baya.

"Babu shakka wannan ne kafin duniya na karshe da zan buga," in ji Lionel.

Da yake zantawa da ESPN Messi ya kara da cewa: "ina kirga saura kwanaki nawa a fara World Cup.

Akwai kaguwa da kuma fargaba a lokaci guda. Ina son ya zama yanzu, abin da zai faru da kuma wanda kan je ya dawo.

A 2005 ne messi ya fara bugawa kasarsa wasa, kuma ya buga wasa 164 ya zuwa yanzu ya ci kwallo 90.

Argentina da ke matsayi na hudu na kasashen duniya da Fifa ta fitar, za ta kara da Saudiyya da Mexico da Poland a rukunin C wanda za a fara a ranar 20 ga watan Nuwamba.

"A World Cup komai zai iya faruwa. Duka wasannin na da zafi. Wanda aka fi mayar da hankali a kansa zai iya samun nasara," a cewar Messi.

"Ba ni da tabbas ko mu ne wadanda aka fi mayar da hanakali a kai, amma ko da yaushe Argentina na sawun gaba saboda tarihi.

"Yanzu abinma ya zarce haka saboda lokacin da muke ci. Kuma watakila akwai kasashen da suka sha gabanmu a wannan gasar."