Faransa ta haramta wa ɗalibai mata sanya abaya a makarantun gwamnati

Abaya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An shafe watanni ana tafka muhawara kan sanya abaya a makarantun Faransa

Ma'aikatar ilimi a Faransa ta bullo da tsarin haramta wa dalibai mata musulumi sanya rigunan abaya a makarantun gwamnati.

Matakin zai soma aiki da zaran an soma sabon zangon karantu a ranar 4 ga watan Satumba.

Faransa na da mataikai masu tsauri na haramci kan duk wata alama da ke nuna addini a makarantun gwamnati da gine-ginen gwamnati, tana mai cewa ya take dokokin fifita wani addini.

Tun a shekara ta 2004 aka haramta sanya hijabi ko ɗankwali a makarantun gwamnati da ke faɗin kasar.

''Bai kamata da zaran ka shiga aji, ka iya tantace addini mutum ba kawai daga kallonsu, a cewar Ministan Ilimi, Gabriel Attal a lokacin tattaunawa da tashar Faransa ta TFI, yana mai jadadda cewa: ''Na yanke hukunci daga yanzu cewa babu batun sanya hijabi a makarantu.''

Matakin na zuwa ne baya an shafe watanni ana tafka muhawara kan sanya abaya a makarantun gwamnatin Faransa.

Rigar abaya ta kasance suturar da ake samun karuwar amfani da ita a makarantu, abin da ya rinka haddasa rabuwar kawuna a siyasanse, inda jam'iyyu masu tsatsauran ra'ayi ke tursasa batun haramci kan rigar, yayin da masu sassaucin ra'ayi ke nuna matukar damuwarsu kan 'yanci mata manya da kanana Musulmi.

''Rashin fifita addini wani tsari ne da ke bai wa mutum 'yanci ba tare da takura ba a makarantu,''kamar yada Mista Attal ya shaidawa TFI, yana mai shaida cewa abaya ''sutura ce da ke nuna addini'', wanda haka na iya zama kamar gwaji ko wani abin tunziri tsakanin daliban makaratu.''

Ya ce zai ba da umarni kai-tsaye a wata sanarwa kafin a buɗe makarantu idan an kammala hutun zagon karshe.

Abaya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dalibai Musulmi na nuna rashin jindadinsu da matakin hannasu sanya abaya

A 2010, Faransa ta haramta sanya hijabi ga kowa a faɗin kasar abin da ya tunzura mutane a ƙasar da ke da yawan al'ummar Musulmi miliyan biyar.

Faransa ta haramta duk wata alama da ke nuna addini a makaratu tun karni na 19, ciki harda alama ko tambarin Yesu da Kiristoci ke amfani da shi, a kokarin daƙile tasirin cocin katolika a faninin ilimin ƙasar.

An rinka yi wa dokar garambawul da kara wasu dokokin a tsawon shekaru domin shigar da kowanne ɓangare na al'umma, ciki harda Musulmi masu amfani da hijabi da Yahudawa masu sanya hula a tsakiyar kai, amma dai ba a haramta abaya ba, sai a wannan lokaci.

Hijabi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ida dokar ta soma aiki mata dalibai za su daina sa hijabi da abaya a makarantu

Muhawara ko ce-ce-ku-ce kan alamar Musulunci ta ta'azzara tun lokacin da wani ɗan gudun hijirar Chechen ya fille kan wani malami Samuel Paty, bayan ya nunawa dalibai hoton barkwancin Annabi Muhammad, a kusa da makarantarsu a wani yanki da ke Paris a 2020.

Sanarwar ta kasance matakin farko na sabbin dokokin da Mista Attal ya bullo da su, bayan Shugaba Emmanuel Macron ya naɗa shi ministan ilimi a watannin da suka wuce yana da shekaru 34.

Kungiyar CFCM, da ke wakiltar Musulmai a fadin Faransa, ta ce sutura ba ita kadai ba ce abin da ke nuna alamar addini.