Yadda koyarwa ta intanet ke barazana ga aikin malunta

Wata yarinya na ɗaukar darasi ta Intanet a cikin kwamfutar ta a gida a ranar 19 ga watan Mayu, 2020 a Nonthaburi, na ƙasar Thailand.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata yarinya na ɗaukar darasi ta Intanet a lokacin cutar korona

Hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya na nemna a samar da dokoki da zasu hana kwamfutoci maye gurbin malamai a wurin koyarwa

Hukumar ta Unesco, ta kuma ƙara jaddada ƙudirin ta na samar da ilimi ingantacce ga kowa. Hakan na ƙunshe ne cikin rahoto kan lura da al'amuran ilimi a duniya na 2023.

"Wata fasahar na taimakawa a wani ɓangare na koyarwa, sai dai akwai wadda bazata taimaka ba, ba tare da taimakon malamai ba," inji rahoton.

"A fara biyan buƙatun masu koyo, a kuma taimakawa malamai," inji Unesco.

Babban Daraktan hukumar, Audrey Azoulay, ya ce "Mu'amalar intanet ba daidai take da mu'amalar mutane ba.

Matsala ga mazauna karkara

Rahoton na hukumar Unesco ya nuna alfanun da fasahar zamani ta yi wajen hana ilimi ɗurƙushewa a lokacin cutar korona, sai dai ya ce an bar wasu da dama a baya.

Koyarwa ta Intanet a lokacin cutar korona ya gaza samuwa ga rabin biliyoyin ɗalibai da ake da su a duniya, inda hakan ya fi shafar marasa galihu da kuma mazauna karkara.

Har yanzu ba a gano ribar ɗaukar darasi ga yara ta intanet ba. Kaso ɗaya cikin huɗu na makarantun furimare a faɗin duniya basu da wuta, inji rahoton.

"Ilimin sarrafa kwamfuta na amfani ne wajen samun damar yin amfani da duk wata dama ta faɗaɗa ilimi," inji Mano Antoninis, marubucin rahoton

A wata tattaunawa da yayi da BBC, Mr Antoninis ya yarda cewa na'urar zamani kamar wayar hannu na iya samar da hanyar inganta rayuwa ga masu rauni, musamman ƴan gudun hijira.

Sai dai yana ganin hakan a matsayin wani mataki na gaggawa ba wani abu da zai maye gurbin hanyar koyarwa da aka saba da ita ba.

"Kamar misalin gagarumin lamarin hana yara mata ne a Afghanistan zuwa makaranta a ƙasar, sai wasu daga cikin yaran suke ɗaukar darasi ta intanet a ɓoye, duk da kaɗan ne daga cikin su suke da irin wannan damar,"inji shi.

Yara mata a bisa hanyar su ta dawowa daga makaranta a Mazar-i-Sharif a ranar 30 ga watan Octoba, 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yara mata a ƙasar Afghanistan na ɗaukar darasi ta Intanet a ɓoye, sai dai Unesco ta ce hakan mafita ce ta wucin gadi.

Akwai wasu ƙarin ƙalubalen da ke tattare da koyarwa ta intanet.

Mr Anoninis ya ce da yawan manhajar karatu ta intanet bata bin tsarin manhajar karatu ta ƙasa.

"Da yawan manhajar karatu ta intanet anyi ta ne da turanci, saboda haka duk yaran da ke ɗaukar karatu da yaran su , za a barsu a baya,"inji shi.

"Akwai kuma ƙarancin bayanan da za su taimaka wajen sanin manhaja mafi inganci wajen ɗaukar karatu."

Rashin mayar da hankali daga ɗalibai da malamai wajen ƙirƙirar damar tattara bayanai kan alfanun manhajar, na daga cikin abunda ke ƙara janyo koma baya a ɓangaren.

Ƙarancin sa ido

Sauran ɓangaren da ake nuna damuwa akai shine ƙarancin dokoki. Ƙasashe shidda ne kaɗai a duniya ke da dokar kiyaye bayanan mutane.

Unesco ta ce ba wai tana kira ga ƙasashe da su dakatar da karatu ta manhajar Intanet ba , sai dai ba kowane sabon al'amari ne ke zama ci gaba ba.

Wata malama ta rabawa ɗaliban ta biye-rana domin ƙara masu ƙwarin guiwa gaf da zana jarabawar share fagen shiga jami' a, a ranar 1 Yuni, 2023 a Luoyang,na lardin Henan na ƙasar China.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Unesco na nuna mahimmancin malamai da kuma koyarwa a cikin aji.

"Fasahar koyarwa ba lallai tana nufin koyawa ta manhaja ba. Rahohoton ya ƙara bada bayanan hanyoyin da za a iya amfani da fasahar zamani wajen inganta ilimi. Sai dai , yawancin manhaja ba a tsara su domin ɗaukar karatu ba," inji Mr Antoninis.

Ya kuma ƙara da cewa " rahoton baya bada shawara ta kowane ɓangare ga ƙasashe wajen yin watsi da canje-canjen da fasahar zamani ta zo da su ba".

Sai dai ya yi kira ga gwamnatoci da su samar da bayanan gargaɗi.