Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cocin da aka kafa don karɓar 'yan luwaɗi cikin sirri a Kenya
- Marubuci, Esther Ogola
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kenya
Wata coci a Kenya ta shafe shekara 10 da suka wuce tana gudanar da ayyuka a ɓoye. Ba ta bayyana ayyukanta a wanna ƙasar mai cike da addini saboda tana maraba da 'yan luwaɗi masu ibada.
"Lokaci na farko da na shiga cocin sai da na yi kuka," in ji John, wani fasto da yake tare da wata cocin a hirarsa da BBC.
Ya bar cocin da yake ne saboda shugabanninta sun faɗa masa cewa aƙidar jinsinsa zunubi ne da yake buƙatar kar ya yi aure ko jima'i tsawon rayuwarsa.
"Ban taɓa tunanin a rayuwata a matsayina na fasto, zan kasance a wani wuri ba da zan faɗi kalmomi uku da mutane za su ce ba su jituwa da juna; ni baƙar fata ne, ɗan luwaɗi, kuma mai fasto."
Ya ji labarin cocin ne, inda yanzu yake yin wa'azi, a shafukan sada zumunta. Kamar sauran mutanen da muka tattauna da su a cocin, mun ɓoye sunansa don kare rayuwarsa.
Su ma sauran ma'abota cocin na ƙoƙarin kare bayanan da suke bayarwa game da tarukansu - sabbin waɗanda ke son shiga ana bi a hankali wajen tantance su kafin a gayyace su.
Luwaɗi da maɗigo haramun ne ƙarƙashin dokokin Kenya, duk da cewa a wannan shekarar kotun ƙoli ta janye haramcin da aka saka wa ƙungiyoyin 'yan luwaɗi na yin rajista a matsayin waɗanda ba na gwamnati ba.
"Za mu fara. Za mu rufe idanwanmu mu yi addu'a," a cewar Pauline, wata hadimar cocin sanye da baƙar doguwar riga. Sai ɗakin ya yi tsit.
Pauline 'yar luwaɗi ce da ba ta ɓoyewa kuma ta fita daga jinsin mace ko namiji - tana amfani da lamirin suna na "ku" da "su" maimakon "shi" da "ita" - kuma tana cikin waɗanda suka kafa cocin.
Tunanin kaɗaici ne ya fi cika rayuwar Pauline, musamman tun da mahaifinta ya mutu sakamakon cutar HIV lokacin da suke shekara 12.
"Bayan mahaifina ya mutu, mutane suka fara sauya mana fuska. Sun zaci dukkanmu muna da HIV. Ana zuba wa mahaifiyarmu abinci a kwano da kofi daban kuma aka fara hana mu shiga wasu wurare. Coci na cikin wuraren da aka hana mu zuwa saboda mutane na ganin mahaifiyarmu na da cuta," in ji Pauline.
Irin wannan ɗabi'ar ta yaɗu zuwa sauran coci-coci, inda suke nuna damuwa game da rayuwar Pauline - ƙila game da yadda suke yin shigarsu ko kuma yadda suke kasa yin soyayya ko mu'amala da sauran mutane.
Saboda haka sai Pauline da ƙawayenta suka fara haɗuwa a ranakun Lahadi don kallon haɗubobi a dandalin YouTube, da kuma neman sauran 'yan luwaɗi da ke Kenya.
Lokacin ƙyamar 'yan luwaɗi na ƙaruwa a Gabashin Afirka.
Ba su san cewa nan da shekara 10 ɗan zaman da suke yi zai zama dandalin da mutum 200 za su dinga haɗuwa ba.
A wajen Ragina, sai da suka fafata da wani sashe na tsohuwar cocin da take kafin ta bar wurin. Sashen ya ba ta wa'adi bayan an gano cewa tana da budurwa: ko dai ita ko kuma su.
"Na ji kamar an yaudare ni. Ni ce uwar ɗakin wasu daga cikinsu amma yanzu ba zan iya zama da su ba," in ji ta.
Ragina ta zaɓi ta ci gaba da zama da buduwarta. Shekara 10 bayan haka, sai ta ji tana so ta ci gaba da rayuwar coci, kuma yunƙurinta ne ya sa ta haɗu da wannan cocin.
Sai dai lamarin bai kasance mai sauƙi ba ga mambobin cocin, waɗanda suka sha fama da hare-hare - misali, duk lokacin da maƙwabta ko kuma masu ginin da cocin yake suka ji ransu ya ɓaci da kasancewarsu 'yan luwaɗi.
An taɓa rufe ginin nasu duk da cewa sun biya kuɗin haya, aka yi kaca-kaca da ɗakin ibadar tasu, 'yan sanda kuma suka nemi cin hanci don ba su "kariya" ko kuma su kama su.
Sun sauya wuri har sau tara cikin shekara 10, akasari saboda su ci gaba da ɓoye kansu.
Zaman cocin ma mai sauƙi ne, saboda wasu mambobin ba su faɗa wa 'yan uwansu game da aƙidarsu ba, don haka sai sun je sauran coci kafin su haɗu a can daga baya.
"Lokacin da muka fara, kowa yana ɗari-ɗari kuma ya ƙi bayyana wahalhalun da yake ciki," in ji Pauline.
Wannan ne ya sa aka kafa "Chat and Chew", wata majalisa da ke bai wa mambobin damar ba da labaran yadda rayuwa take kasance musu a Kenya.
"Bayan kammala addu'o'i, da yawa sukan nemi su gana da fasto-faston don bayyana damuwarsu kan soyayya, da yadda 'yan uwansu ke ƙyamatarsu, da rashin wurin zama, da sauran ƙalubalen da mutane kan fuskanta saboda kasancewarsu 'yan luwaɗi. Saboda haka muka fara zama a 'Chat and Chew' don ba da labarai, mu rungume juna, mu ƙarfafa wa juna gwiwa."
Yayin da ake ƙara tsanar 'yan luwaɗi a Kenya, Pauline ta ce wasu mambobin sun fara tunanin komawa rayuwar sirri - duk da cewa da yawansu na son cocin ta ci gaba da ayyukanta.
"Lokacin da muka fara, ba mu yi tunanin wurin zai samu muhimanci haka. Amma dai ba za mu taɓa karaya ba, dole mu san yadda za mu ci gaba.
"Ina son wurin nan ya zama buɗaɗɗe ga kowa da kowa kuma mu samo hanyar da za mu dinga girmama juna duk da irin bambancin aƙidarmu da kuma al'adu."