Ana ci gaba da kai hari wasu yankunan Zamfara duk da sulhu da 'yanbindiga

Asalin hoton, OTHERS
Rahotanni na nuna cewa 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare suna kashe mutane da kuma sace dabbobi da sauran dukiya a wasu sassa na yankin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, a Najeriya.
A lamari na bayan-bayan nan sai da 'yan bindigan suka kashe mutum biyar, suka raunata wasu hudu a garin Galadi.
Hare-haren dai na aukuwa ne duk da yunkurin yin sulhu da al'ummomin wasu garuruwa na Shinkafin ke yi da 'yan bindigan, da kuma matakan tsaro da ake dauka.
Matsalar hare-haren 'yan bindiga, wadda ta zame wa yankin arewa maso yammacin Najeriya wani karfen-kafa, na ci gaba da addabar garin Galadi da sauran kauyuka da dama da ke makwabtaka da shi a yankin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Kamar dai yadda wani mutumin yankin ya shaida wa BBC:
''Ko a ranar Litinin da ta gabata an kawo hari a wani gari da yake kusa da mu na Bargaja, da rana tsaka inda suka dauki mutane a yayin da suke cikin aiki a gonakinsu
''kamar yadda Laraba ma da ta gabata da karfe 10:15 na dare sun kara kawo hari a nan Galadi, inda suka kewaye gaba daya Galadin in banda bangare guda shi ma saboda gulbi ya tare a wannan gefen inda suka bude wa Galadi wuta gaba daya ta kowane gefe,'' in ji shi.
Ya kara da cewa : ''Hakan ya sa ka yi asarar rayukan mutane biyar kuma hudu suna kwance a asibiti. A wannan lokacin ba su tafi da kowa ba saboda saboda dauki da aka samu daga wasu jami'an tsaro da suka zo daga Shinkafi.
Ya yi bayani da cewa : ''Don a nan muna da jami'an tsaro amma ko da suka zo kawo wannan harin sun mamaye sansanin da jami'an tsaron suke.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Haka kuka mutumin na yankin na Galadi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce wadannan hare-hare na ci gaba da aukuwa ne, duk kuwa da shirin da al'ummomin yankin ke yi da na gwamnatin tarayya, don tattaunawar sulhu da 'yan bindigan.
Yayin da BBC ta tuntubi babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Zamfara kan kafafen yada labarai, Mustafa Jafaru Kaura, ya ce har yanzu matsayin gwamnatin jihar bai sauya ba, game da nisantar tattaunawa ko sulhuntawa da 'yan bindiga:
''Don haka idan har wani abu ya faru a wannan gari na Galadi to gwamnatin jihar Zamfara na bakin cikin faruwar wannan al'amari kuma tana yin dukkanin mai yuwuwa domin ganin an ci gaba da wannan fada da kuma fatattakar barayin nandomin ganin Allah ya kawo mana saukin wannan matsala.''
Masana harkar tsaro dai na ci gaba da yin tsokaci, cewa kokarin magance matsalar ta tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya , abu ne da ke bukatar matakai irin na bai daya.
Kuma wadanda za a dauka lokaci daya, idan dai ana so a ga karshen wannan matsala da ta ki ci ta ki cinyewa.










