Muhimman abubuwa 10 da suka faru a zagayen rukuni na Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da aka kammala wasannin zagayen rukuni a gasar Euro 2024 jiya Laraba, tawagogi 24 sun buga wasa 72 a tsakaninsu.
Daga cikinsu 16 sun yi nasarar kaiwa zagaye na biyu kuma na sili ɗaya ƙwala.
Ga wasu daga cikin alƙaluma na abubuwan da suka faru a zagayen:
- An buga wasa 72
- An ci ƙwallo 81
- Sifaniya ce kaɗai ta ci wasanninta uku
- Sifaniya ce kaɗai ba a zira wa ƙwallo a raga ba
- Jamus ta fi kowace tawaga cin ƙwallaye (8)
- Jamus da Portugal ne suka fi kowace tawaga yawan riƙe ƙwallo a wasa, inda suka riƙe jimillar kashi 64.3 na ƙwallon
- Georges Mikautadze na Georgia ne kan gaba a cin ƙwallaye (3)
- Cristiano Ronaldo ne ya fi kowa yawan yunƙurin cin ƙwallo (12)
- Romelu Lukaku na Belgium ne ya fi kowane ɗan wasa ɓarar da babbar dama (6)
- Giorgi Mamardashvili na Georgia ne ya fi kowane gola hana ƙwallo shiga raga bayan ya kare 20







