An tuhumi mutumin da ake zargi da harbin firaiministan Slovakia da kisan kai

Asalin hoton, Reuters
An tuhumi wani mutum da yunƙurin kisan firaiministan ƙasar Slovakia, Robert Fico bayan ya harbi ɗan siyasar.
Mutumin da ake zargi dai ba a ambaci sunansa ba a hukumance amma rahotanni daga Slovakia sun ambaci cewa yana da shekaru 71 kuma yana zaune a garin Levice.
Rahotanni sun ce mutumin ka iya fuskantar hukuncin ɗaurin rai da rai.
Mista Fico,mai shekaru 59 na cikin wani yanayi amma dai an ce yana murmurewa bayan harbin da aka yi masa wanda mutane da dama suka bayyana da na siyasa.
Ministan cikin gidan ƙasar, Matus Sutaj Estok ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis cewa mutumin da ake zargi da aikata laifin ya yi hakan ne shi kaɗai kuma a baya-bayan nan ya shiga jerin zanga-zangar nuna adawa da gwamnati da aka yi.
Firaiministan Slovakia na samun kulawar likitoci bayan harbin da aka yi masa

Asalin hoton, Getty Images
Firaiministan Slovakia, Robert Fico na murmurewa duk da dai likitoci na cewa yana cikin yanayin mutu kwakwai rai kwakwai bayan an harbe shi ranar Labaraba.
Darekta na asibitin ya ce yanzu haka yana sashen kula da masu matsananciyar jinya bayan kwashe awanni bakwai a wurin tiyata.
Tun da farko dai, mista Fico mai shekara 59 ya yi fama bayan harbin shi da aka yi a harin na garin Handlova. An dai kama mutumin da ake zargi da aikata harbin.
Miriam Lapunikova, darektar asibitin jami'ar F. D. Roosevelt University Hospital da ke Banska Bystrica, inda aka kwantar da mista Fico ta shaida wa manema labarai cewa "yana jin jiki".
A baya dai mataimakin firaiministan, Tomas Taraba ya shaida wa BBC cewa an yi wa mista Fico tiyata ba tare da wata matsala ba kuma "ina da yaƙini zai warke".
Ministan cikin gida, Matus Sutaj Estoka ya bayyana al'amarin da yunƙurin kisa na siyasa.
Mista Fico dai ya kasance mai raba kan al'ummarsa a ƙasar - sannan mutum ne mai cike da taƙaddama a tarayyar Turai bisa kiraye-kirayen da yake yi na kawo ƙarshen tallafa wa Ukraine ta fuskar soji da kuma sanya wa Rasha takunkumai.
To sai dai wannan harin da aka kai masa ya samu suka daga ciki da wajen ƙasar inda aka bayyana harin a matsayin hari kan mulkin dimokradiyya.
Yadda aka harbe Fico a kusa da kusa
Ɗan bindigar da ya harbi mista Fico ya shiga cikin wani ɗan ƙaramin dandazon magoya bayan firaiministan da suka taru a wajen cibiyar raya al'adar da ke garin na Handlova, inda Mista Fico yake yin wani taro.
Harbin ya mamayi masu bai wa mista Fico kariya. Wani bidiyo ya nuna yadda aka ɗauki firaiministan ranga-ranga bayan an harbe shi inda aka sanya shi a cikin mota aka kuma bar wurin.
Ɗan bindigar dai ya harbi firaiministan ne sau biyar a kusa da kusa inda kuma harsasan suka sami mista Fico a ciki da kafaɗa











