Rashford zai koma buga wasannin aro a Aston Villa

Marcus Rashford

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Aston Villa ta kusan ƙulla yarjejeniayar ɗaukar ɗan wasan Manchester United, Marcus Rashford, kafin a rufe kasuwar cinikayyar ƴar ƙwallo ranar Litinin.

Wata majiya ta sanar da BBC cewar ana tattaunawa kan cinikin ɗan wasan, amma da aiki nan gaba kafin a kammala komai.

Rabonda Rashford ya buga wa United tamaula tun karawa da Viktoria Plzen a Europa League da ta ci 2-1 ranar 12 ga watan Disamba.

A makon da ya wuce Ruben Amorim ya ce ba zai yi amfani da Rashford ba koda zaman benci ne, gwara ya sa mai shekara 63, mai horar da masu tsare raga.

Rashford ya fara wasa a United tun yana da shekara bakwai, ya yi mata karawa sama da 400 da lashe Europa League da FA Cup biyu da kuma EFL Cup biyu.

Ya ci wa United ƙwallo 138 har da 30 da ya zura a raga a kakar 2022-23.

Ya ci ƙwallo a wasan farko da Amorim ya tashi 1-1 a gidan Ipswich ranar 24 ga watan Nuwamba, sannan ya ci Everton biyu a karawar da United ta yi nasara 4-0.

United ba ta yi amfani da Rashford ba a fafatawar hamayya da ta doke Manchester City 2-1 ranar 15 ga watan Disamba,

A cikin watan Janairu, Villa ta ɗauki ɗan wasan Sifaniya, Andres Garcia daga Levante da na Netherlands, Donyell Malen daga Borussia Dortmund.

Ranar Juma'a Aston Villa ta sayar da ɗan wasan Colombia, Jhon Duran ga Al-Nassr mai buga gasar Saudi Arabia kan £71m.

Villa ta ƙi sallama tayin da Arsenal ta yi wa Ollie Watkins.

Aston Villa tana ta takwas a teburin Premier League, sannan tana cikin ƴan takwas ɗin farko da suka kai zagayen gaba kai tsaye a Champions League a bana.