Fifa za ta kaɗa kuri'ar bayar da bakuncin kofin duniya na mata 2027

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa za ta kaɗa kuriar zabar wadda za ta bai wa bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata ta 2027.
Masu yin takara kawo yanzu sun hada tsakanin Brazil da hadaka tsakanin Belgium da Netherlands da kuma Jamus.
Dukkan masu takara sun cika dukkan ka'idar da ake bukata, amma Brazil ce kan gaba a hada yawan maki ta fannin filaye da wuraren kwana da sufuri da sauransu.
Idan har Brazil aka bai wa shirya gasar ta 2027, zai zama na farko da za a gudanar da gasar cin kofin duniya ta mata a Kudancin Amurka.
Kasashe 211 da suke mambobin Fifa ne za su kaɗa kuri'ar a taron hukumar na 74 da za a gudanar a Bangkok ranar 17 ga watan Mayu.
Wani bincike da aka gudanar ranar Talata ya nuna cewar Brazil ce kan gaba da 4.5 daga kaso biyar, yayin da Belgium da Netherlands da Jamus keda 3.7.
A makon jiya Amurka da Mexico suka janye daga hadakar neman karbar bakuncin gasar kofin duniya ta mata ta 2027.
Sun sanar da cewar za su mayar da hankali wajen neman shirya wasannin gasar 2031, yayin da Afirka ta Kudu ma ta janye a cikin watan Nuwamba.











