Gargaɗin DSS ga NLC da fatalin cire tallafin lantarki

Wannan maƙale ce da ke duba kan muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata

A cikin makon da ya gabata ne hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi kira ga ƙungiyar ƙwadago ta NLC da ta janye ƙudurinta na shirya zanga-zangar gama gari domin samun zaman lafiya a Najeriya.

NLC ta tsara shiga yajin aikin ranar 27 da 28 ga watan Fabarairu a wasu yankunan ƙasar domin nuna rashin jin daɗinta ga halin matsin rayuwa da ƴan Najeriya ke fuskanta da wasu matsaloli.

Wannan ya zo ne yayin da kwamishinan ƴan sanda a Abuja, CP Ben Igweh cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar, ya ce rundunarsa ba ta da masaniya kan zanga-zangar da ake shirin yi a Abuja.

Majalisar dattawa ta yi watsi da cire tallafin lantarki

A cikin makon da muke bankwana da shi ɗin ne kuma majalisar dattawan Najeriya ta yi fatali da shirin gwamnatin ƙasar na janye tallafin da take bayarwa a harkokin wutar lantarki, wanda hakan ke nufin kuɗin da ake biya na wutar zai ƙaru.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne a zamanta na ranar Laraba.

A tattaunawarsa da BBC Sanata Ali Ndume ya ce babu yadda za a yi a ƙara kuɗin wuta ba tare da sahalewar majalisa ba.

"Wutar da ba ma a samunta ta yaya za a ƙara kuɗinta, a haka ma ni inajin ana karɓar kuɗaɗen da suka wuce iyaka daga hannun alumma'', in ji dan majalisar datawan daga jihar Borno.

Zazzabin Lassa ya bulla a asibitin sojoji na Kaduna

A makon da ya gabatan ne kuma aka samu ɓullar cutar zazzaɓin lassa a asibitin sojoji na na '44 Nigerian Army Reference Hospital'.

Tuni dai gwamnan jihar Uba Sani ya bayar da umarni ga ma'aikatar lafiyar jihar ta gudanar da bincike domin gano musabbin ɓullar cutar.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar, Muhammad Lawal Shehu, ya fitar ya ce gwamnatin jihar ta samu labarin bullar cutar zazzabin Lassa a asibitin sojojin.

Cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutum hudu a cikin harabar asibitin, yayin da aka samu mutum uku da ke nuna alamun kamuwa da cutar.

Tuni dai jami'an lafiyar jihar da hadin gwiwar hukumomin asibitin suka dauki matakai domin dakile bazuwar cutar.

Gwamnatin Legas ta ɓullo da matakan sassauta ƙuncin rayuwa

Haka kuma a tsakiyar makon da ya gabatan ne gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana wasu jerin matakai da gwamnatinsa za ta ɗauka don sassauta wa al’ummar jihar halin matsin rayuwa da ake fuskanta a faɗin ƙasar.

Matsin rayuwar da al’ummar Najeriya ke ciki dai ya janyo zanga-zanga a wasu jihohin ƙasar, ciki har da Kano da Oyo da kuma Osun.

Ana ɗora alhakin tsadar rayuwar da mutane ke fuskanta ne a kan matakan da gwamnatin tarayyar ƙasar ta ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta tantance farashin dala.

Lamarin ya haifar da tashin gwauron-zabi na farashin kayan abinci da na masarufi da kuma rashin albarkar kuɗin da ke hannun al’umma.

Jerin matakan sassauta matsin rayuwar da gwamnan ya ɗauka sun haɗa da rage ranakun aiki ga ma'aikata, da ciyar da mutum 1,000 kyauta a kowace rana

Sojojin Najeriya sun gargaɗi masu kiran a yi juyin mulki

Haka kuma a makon da ya gabatan ne babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gargaɗi masu kiraye-kirayen juyin mulki sakamakon matsin rayuwa.

Janar Musa ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin da yake ganawa da ƴan jarida a birnin Fatakwal na jihar Ribas, bayan ƙaddamar da ayyukan wasu gine-gine.

Babban hafsan sojin ya buƙaci masu furta irin waɗannan kalamai da su daina.

An dai gudanar da jerin zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa a jihohin Kano da Oyo da Ogun a ƙasar ta Najeriya, yayin da mutane ke ci gaba da kokawa kan tsadar kayan masarufi.

Kotu ta tura Murja Kunya asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa

Haka kuma a makon da ya gabatan ne wata kotu da ke zaman ta a birnin Kano ta bayar da umarnin tura ƴar tiktok Murja Ibrahim Kunya zuwa asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta.

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Babajibo Ibrahim ne ya tabbatar wa BBC hakan bayan zaman kotun da aka yi ranar Talata.

A hirar sa da BBC, Babajibo ya ce "yanayin da take ciki da kamanninta da kuma maganganun da take faɗa sun nuna cewa ba ta cikin hali na cikakken hankali."

Ya ƙara da cewa "wannan ne dalilin da ya sa alƙalin ya buƙaci a tura wadda ake zargin zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa har zuwa ranar 20 ga watan biyar, 2024."