CAF ta fara bincike kan rikita-rikatar Super Eagles da Libya

A

Asalin hoton, CAF

Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika CAF ta sanar da cewa ta samu bayanai kan abin da yake faruwa tsakanin hukumomin kwallon kafa na Najeria da Libya a wasan neman gurbin shiga gasar kofin ƙasashen nahiyar ta 2025.

CAF ta ce ta tuntuɓi hukumomin kwallon kafar ƙasashen Najeriya da na Libya domin jin abin da yake faruwa game da yadda tawagar Super Eagles ta maƙale a filin jirgin sama da ke Libya awanni masu yawa, bayan nan aka ce su sauka.

A yanzu dai Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika ta gabatar da wannan matsala ga kwamitin ladabtarwarta domin bincike tare da ɗaukar mataki kan wanda ya karya dokar hukumar.

Ƴanwasan Super Eagles

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, NFF ta ce 'yan wasan Najeriya sun shafe kusan awa 15 a filin jirgi suna jira

Tawagar Super Eagles ta kama hanyar komawa Najeriya

Tawagar Super Eagles ta 'yanwasan Najeriya ta kama hanyar komawa gida bayan shafe kusan awa 15 a filin jirgin sama na ƙasar.

Shugabar hukumar 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da hakan a shafinta na X bayan ɗanjarida Adepoju Tobi Samuel ya ce suna shirin shiga jirgin komawa.

Hakan na nufin Najeriya ba za ta buga wasan neman shiga gasar Kofin Afirka ba da aka tsara a gobe Talata da Libya, bayan tashi wasan farko Nigeria 1-0 Libya a makon da ya gabata.

Tawagar ta Super Eagles ta yi zargin da gangan hukumomin Libya suka sauya filin jirgin da ya kamata su sauka, yayin da ita ma hukumar ƙwallon Libya ke cewa sun fuskanci irin wannan matsalar lokacin da suka je Najeriya.

Yanzu kallo ya koma kan hukumar ƙwallon Afirka Caf domin ganin hukuncin da za ta ɗauka game da lamarin.

Ba za mu buga wasa da Libya ba - Super Eagles

William Troost-Ekong

Asalin hoton, William Troost-Ekong/X

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya - Super Eagles, William Troost-Ekong ya ce shi da ƴanwasan ƙasar sun yanke shawarar cewa ba za su buga wasa da Libya ba a wasan neman shiga gasar cin kofin Afirka ta 2025.

Troost-Ekong ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa game da halin da suka tsinci kansu bayan isar su Libya domin buga wasa a ranar Talata.

Ƴanwasa da jami'an tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta Super Eagles sun tsinci kansu cikin wani yanayi bayan da suka shafe kusan awa 15 a filin jirgin sama na Abraq da ke Libya.

A yammacin ranar Lahadi ne, tawagar Super Eagles ta isa Libya domin buga zagaye na biyu na wasan neman shiga gasar kofin ƙasashen Afirka ta 2025 da za a yi a Morocco.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumomin Libya suka tilasta jirgin Super Eagles sauka a filin jirgin sama na Abraq, maimakon filin jirgin saman Benghazi da tun asali aka tsara ƴanwasan za su sauka, kamar yadda hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta bayyana.

Najeriya da Libya za su ɓarje gumi ne a zagaye na biyu na wasan a ranar Talata.

A wasan farko da aka buga a Najeriya, Super Eagles ɗin ce ta doke Libya da ci ɗaya da nema.

Hotuna da bidiyo da NFF ta fitar a shafukan sada zumunta sun nuna yadda yanwasan na Super Eagles suke zaune dirshan a filin jirgin saman, inda suke ta hira bayan shafe fiye da sa'o'i 12 cikin jirgi daga Najeriya zuwa Libya.

Hukumomi sun ce bayan nan, ƴanwasan kuma za su sake saɓar titi inda za su yi tafiyar awa uku a mota daga Abraq zuwa Benghazi wurin da za su taka leda.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya ma ta yi ƙorafi kan yadda hukumomin Najeriya suka ajiye su tsawon sa'o'i lokacin da jirginsu ya sauka a ƙasar a wasan farko da suka je yi.

Wani abu da ke ci gaba da ɗaure wa mutane kai a shafukan sada zumunta shi ne ko abin da ya faru ramuwar gayya ce da hukumomin Libya suka ɗauka kan abin da suka ce ya faru da su a Najeriya.

Kyaftin ɗin na Eagles ya ce akwai buƙatar hukumar ƙwallon kafa ta Afirka CAF ta yi duba kan yanayin da suke ciki da kuma abin da ke faruwa da su a Libya.

A cewarsa "ba za mu yarda mu je ko ina ta titi ba, ko da kuwa da tsaro, babu mu da tabbacin tsaro. Idan muka amince da haka, kuna iya tunanin yanayin da masaukinmu ko abincin da za su ba mu zai kasance."

William Troost-Ekong

Asalin hoton, William Troost-Ekong/X

William Troost-Ekong

Asalin hoton, William Troost-Ekong/X

Mu ma Najeriya ta yi mana haka - LFF

..

Asalin hoton, LFF

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya (LFF) ta ce ba da gangan aka bar tawagar Super Eagles ta Najeriya yashe a filin jirgi ba, duk da cewa su ma an yi musu hakan a Najeriyar.

“Mun damu matuƙa kan abin da ya faru da tawagar ƙwallon ƙafan Najeriya, gabanin wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Afirka," in ji sanarwar da ta wallafa a shafinta na X.

"Dduk da dai mun yi nadamar abin da ya faru, muna kuma jan hankali cewa irin wannan matsala tana iya faruwa bisa kuskure a kowanne lokaci, ko dai saboda ƴan gyare-yare a filin jirgi ko saboda binciken jami'an tsaro ko kuma wasu ƙalubale na daban daga jiragen saman ƙasa da ƙasa.

''Muna matuƙar mutunta Najeriya, kuma muna bayar da tabbacin cewa ba da gangan aka samu wannan matsala ta karkatar da jirgin tawagar Super Eagles ba.

"Mu ma mun fuskanci irin wannan matsala lokacin da muka je Najeriya a makon da ya gabata, amma ba mu zargi hukumomi da aikata hakan da gangan ba."

Bayan wasan farko da Najeriya ta doke Libya 1-0 a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a ranar Juma'a, an tsara buga wasa na biyu a birnin Benghazi na Libya ranar Talata.