Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kashe fiye da mutum 20 a harbe-harben birnin Lewiston na Amurka
Kafafen yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa an kashe fiye da mutum 20 a wani harbe-harbe a jihar Miane.
Ƴan sanda sun ce wani mutum ɗauke da bindiga ne ya hari wurare daban-daban a birnin Lewiston, inda ya raunata mutane da dama.
An dai buƙaci mazauna yankin su yi zaman su a cikin gida, yayin da aka ƙaddamar da sintiri don neman wanda ya kai harin.
Ƴan sanda sun fitar da wani hoton mutumin da ake zargi ɗauke da wata matsakaiciyar bindiga.
Tuni dai aka gabatar wa shugaba Biden bayanin abin da ya faru.
Kawo yanzu mutane aƙalla 50 ne suka samu rauni, duk da cewa ana cigaba da tattara bayanai.
Cynthia Hunter, wata da ke zaune a kusa da wurin da abin ya faru da bayyana kaɗuwa.
Ta ce "Tun shekarar 2012 nake zaune a nan, bana da wani waje da nake buƙata da ya zarce nan. Na saba ina zuwa nan don hutawa tun ina ƴar shekara 19 kuma abin da ya faru ya matuƙar razana ni.
Bana zaton mun taɓa fuskantar irin wannan matsala a baya, ko ma wani abu mai kama da hakan, akwai wata yarinya da aka harba tare da wasu mutum biyar a can ƙasa. Babu abinda mutum zai iya yi. Ina jin damuwar da mutane ke ciki, wannan ba abu ne mai kyau ba ko kaɗan."
Wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar ta ce hukumomin tsaron tarayya suna taya ƴan sanda wajen zaƙulo mai laifin.
Fadar Whte House ta ce shugaba Biden ya yi magana, ta waya da gwamnan jihar da ma sauran hukumomi.