'Mu muka karɓo yaranmu daga hannun masu garkuwa da mutane, ba ƴansanda ba'

Ba sabon labari ba ne cewa an saki ƴanmatan nan biyar waɗanda masu garkuwa da mutane suka sace a Abuja.

Masu garkuwa da mutane sun sace ƴanmatan guda shida da mahaifinsu ne a gidansu da ke Abuja.

Daga baya suka saki mahaifin yaran mai suna Mansour Al-Kadriyah tare da umartarsa da ya je ya nemi naira miliyan 60 kafin a saki yaran.

Sai dai bayan mako ɗaya, mahaifin yaran bai samu damar biyan kuɗin ba, inda masu garkuwan suka kashe ɗaya daga cikin yaransa mai suna Nabeeha, wadda ba ta daɗe da kammala karatun jami'a ba, sun yi hakan ne a matsayin gargaɗi ga iyayen domin su gaggauta nemo kuɗin fansa.

Haka nan ma a wannan lokacin sun ƙara yawan kuɗin fansar da suke nema.

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka fara bayar da gudummawar kuɗi ga iyalan domin a ceto ƴanmatan.

An saki ƴan matan ne bayan shafe kwana 19 a hannun masu garkuwa da mutane.

Ta yaya aka saki ƴan matan?

A ranar Talata da dare, mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya reshen birnin tarayya, Abuja, Josephine Adeh, ta sanar da cewa jami'an ƴan sanda sun kuɓutar da ƴanmatan.

Wata sanarwa da Adeh ta fitar, ta ce ƴansanda tare da haɗin gwiwar jami’an sojin Najeriya ne suka samu nasarar ceto yaran.

Sai dai, lokacin da BBC ta tuntuɓi iyalan Al-Kadriyah don jin yadda aka saki ƴanmatan, abun da suka faɗa ya saɓa da na ƴansanda da kuma sojoji.

Kawun yaran, Sheriff Al-Kadriyah, wanda malami ne a sashen addini da tarihi na Jami'ar Jihar Kwara, ya bayyana cewa su suka kuɓutar da yaransu.

Sheriff ya ce sun biya kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutanen kafin a saki ƴanmatan.

Ya ce bayan biyan kuɗin da kwanaki huɗu ne masu garkuwar suka kira su da su zo su karɓi yaran a jihar Neja.

"Ƴan uwa ne a cikin iyalai suka haɗu domin biyan kuɗin fansar da kuma fitar da iyalin cikin wahalar da suka shiga."

"Ba zan iya faɗan nawa muka biya masu garkuwa da mutanen ba domin sakin ƴanmatan saboda dalilai na tsaro, amma sun karɓi maƙudan kudaɗe a hannunmu."

Ya ce da gaske ne sojoji sun raka waɗanda suka kai kuɗin domin kare su.

"Ba gaskiya ba ne cewa ƴansanda ne suka ceto ƴanmatan ba, mun biya kuɗin fansa kafin sakin su.

"Masu garkuwa da mutanen sun kira mu a ranar da suka yi niyyar sakin ƴanmatan, sannan suka ba mu adireshin wajen da za mu haɗu.

"Sojoji sun bi bayan waɗanda suka je karɓar yaran domin ba su kulawa, babu wani jami'in ɗansanda da ya bi mu.

"Ba wai mun ce ƴansanda ba su yi aiki ba, sai dai dangane da sakin ƴanmatan, ƴansanda ba su kuɓutar da su ba, biyan kuɗi muka yi."

Sheriff Al-Kadriyah ya gode wa dukkan waɗanda suka taimaka musu da tallafin kuɗi domin sakin ƴaransu, inda ya ce kuɗin ya taimaka musu sosai wajen ceto yaran nasu.

Ina ƴanmatan suke yanzu?

Ya ƙara da cewa bayan shafe kwanaki 19 a hannun masu garkuwa da mutane, akwai buƙatar duba lafiyar yaran.

Ya ce ƴanmatan suna asibiti a yanzu inda ake ci gaba da kula da su.

Ya kuma ce mahaifin yaran shi ma yana asibiti, inda yake samun kulawa saboda masu garkuwa da mutanen sun jikkata shi kafin su sake shi ya je ya nemi kuɗi.

"Sun lakaɗa wa mahaifin yaran duka saboda sun faɗa masa cewa ya je ya kawo kuɗi lokacin da yake hannunsu, sai dai ya gaya musu cewa ba shi da kuɗi."

"Wannan ne ya sa suka lakaɗa masa mugun duka, don haka yana buƙatar kulawa ta lafiya kuma yana karɓar magani da murmurewa."

"Masu garkuwan sun kashe mutum huɗu ranar da suka kashe Nabeeha."

Sheriff Al-Kadriyah ya kuma bayyana cewa a ranar da masu garkuwa da mutanen suka miƙa gawar Nabeeha, akwai wasu gawawwaki uku na mutanen da aka kashe.

Don haka ya buƙaci gwamnati da ta shawo kan matsalar tsaro, domin ganin an kawo ƙarshen ayyukan masu garkuwa da mutane a kowace rana a Najeriya.