Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu garkuwan da suka kashe Nabeeha sun sako ƴan'uwanta
'Yan bindiga sun sako 'yan matan nan biyar daga cikin shida da suka sace a yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Hakan ya biyo bayan kashe daya daga cikin ‘yan matan mai suna Nabeeha kimanin mako biyu da suka gabata.
Kisan Nabeeha abu ne da ya tayar da hankalin al’ummar Najeriya, musamman tun bayan da matsalar garkuwa da mutane ta fara tsananta a yankin Abuja.
'Yan uwan Nabeeha da BBC ta tuntuba sun tabbatar da komawar 'yan matan biyar gida a cikin daren jiya Asabar.
Haka zalika hotunan bidiyon komawar 'yan uwan Nabeeha na ta yawo a shafukan sada zumunta, inda 'yan kasar ke ta san barka da farin cikin sakin matan.
Mu ne muka ceto ƴanmatan da aka sace - ‘Yansanda
A wata sanarwa da rundunar 'yansandan Najeriya ta fitar, ta ce jami’anta ne suka kubutar da 'yan matan a wani samame da suka kai a kusa da dajin kajuru da ke Kaduna da misalin karfe 11:30 na daren Asabar, 20 ga watan Janairu.
Sanarwa da jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yansanda, reshen birnin tarayya, Abuja, Josephine Adeh ta fitar na cewa: “Bayan matsa kaimi na sashen yaki da satar mutane na rundunar ‘yansanda tare da hadin gwiwa da jami’an sojin Najeriya game da harin da masu garkuwa da mutane suka kai kan unguwar Zuma 1 na yankin Bwari a ranar 2 ga watan Janairun 2024, ‘yansandan yankin Birnin Tarayya sun samu nasarar ceto wadanda abin ya rutsa da su.”
Sanarwar ta kara da cewa “tuni aka hada su da ‘yan’uwansu.”
Sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani kan ko an yi artabu tsakanin jami’anta da masu garkuwa da mutanen ba ko kuma a’a.
A ranar Talata 2 ga watan Janairu, 2024 ne ƴan fashin daji suka auka gidan su Nabeeha suka sace ta tare da mahaifinta da ƴan 'uwanta mata biyar.
Daga bisani suka saki mahaifinta domin ya kawo kudin Fansa, lamarin ya kuma kai ga kashe Nabeeha saboda gaza cika wa'adin biyan kudin fansa.
Lamarin da ya jima yana ci wa al'umomi da dama musamman a arewacin ƙasar tuwo a ƙwarya, duk da yunƙurin da hukumomi suka ce suna yi na magance shi.
Su wane ne ƴanmatan da aka sako?
Najeebah wadda ta karanci safiyo, wato 'Quantity Surveying' a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Akwai kuma Nadheerah wadda ita kuma take a shekara ta uku a sashen nazarin ajiye namun daji a jami'ar ta Ahmadu Bello.
Sauran ƴan'uwan nasu su ne Adeebah da Aneesah da kuma Mardiyyah.
Nabeeha, wadda ita ce ta rasa ranta a hannun masu garkuwa da mutane ita ce ƴa ta biyu a cikin ƴaƴan mahaifinta wadda ake sa ran za a yi bikin yayenta a makarantar ranar 27 ga watan Janairu.