Kawuna sun rabu kan korar da sojojin Nijar ke wa ƙasashen duniya

r

Asalin hoton, AFP

Masu sharhi kan lamuran siyasa a Yammacin Afrika na nuna fargaba kan yadda alaƙa tsakanin Nijar da manyan ƙasashen duniya ke ƙara taɓarɓarewa.

Wannan na zuwa ne lokacin da hukumomin ƙasar suka umurci jakadiyar Majalisar Ɗinkin Duniya, Louise Aubin ta fice daga kasar cikin sa'o'i 72.

Wannan mataki da ke ɗauke cikin wata takarda da hukumomin suka aike wa Sakataen Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, wadda a ciki suka ce "shi ne tare da hadin bakin kasar Faransa suka koro tawagar ministan harkokin wajen Nijar" daga taron majalisar karo na 78 da ya gudana a Satumba.

Haka kuma sun ce Nijar ta ƙara "fuskantar irin wannan ƙasƙanci a wasu tarukan duniya da suka gudana da Nijar ta so halarta".

Wannan ya matuƙar girgiza mutane da dama a ciki da wajen ƙasar, ganin cewa MDD a mafi yawan lokaci takan tsaya ga maslahar ƙasashe ba tare da ta sanya siyasa a ciki ba.

Ana kallon wannan matakin zai mayar da hannun agogo baya a ayyukan da ƙasashen duniya ke yi a Nijar, da kuma ayyukan agaji da MDD take gudarwa na jin ƙai.

Aubin wadda 'yar Canada ce an naɗa ta a matsayin wakiliyar MDD a Nijar a watan Janairun 2021.

A watan Disamban bara, Burkina Faso da ke makwabtaka da Nijar ta kori nata wakilin MDD a ƙasar, bayan da shugabannin sojoji suka sallami waɗanda aikinsu bai zama dole ba a Ouagadougou, babban birnin ƙasar.

r

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kai ya rabu yayin da wasu ke nuna goyon baya ga matakin shugabannin sojin suka ɗauka na raba gari da manyan ƙasashen duniya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan ne mataki na baya-bayan nan da Sojojin juyin mulkin Nijar suke fuskanta, bayan hukuncin da suka fuskanta daga Amurka, wadda ta bayyana cewa ta gamsu a yanzu an yi juyin mulki a Nijar.

Amurka ta sanar da dakatar da mafi yawan tallafin da take bai wa Nijar bayan ta ayyana mamayar da sojoji suka yi a ƙasar a matsayin juyin mulki, tare da takaita ikonta na ba da agaji ga ƙasar da ke yammacin Afirka.

Cikin wata sanarwa da hukumomin Amurka suka fitar a ranar Talata, sun ce za su ci gaba da bayar da wasu kayan agaji ga ƙasar.

Tun daga 2012, Amurka ta kashe aƙalla dala miliyan 500 a Nijar, wajen taimaka mata a yaƙin da take yi da masu iƙirarin jihadi a ɓangaren Sahel, inda aka tabbatar ƙungiyoyin da ke kai hare-hare a yankin suna da alaƙa da al-Qaeda da kuma IS.

Nijar ita ce ƙasar da ta fi samun taimakon sojin Amurka a Yammacin Afrika, kuma ita ce ƙasa ta biyu mafi girma a yankin Sahel.

Akwai sansanin sojin Amurka na sojin sama da ake kira Air Base 201 a Nijar da ke Agadez da ke arewacin ƙasar, sai kuma na Air Base 101 da ke Yamai babban birnin ƙasar.

Wannan ya sa sojojinta suka kai 1,100 a ƙasar.

Za ta dakatar da duk wani taimakon da ba na jin ƙai ba, ciki har da horar da sojojin Nijar.

Amma za ta ci gaba da amfani da jiragen sa ido kan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi domin tabbatar da tsaron sojojin Amurka.

Akwai kusan dakarun Amurka 1,000 a Nijar wadanda za su cigaba da zama a ƙasar.

Gabanin wannan mataki sai da ta fara ɓaɓewa da uwar gijiyarta Faransa.

..

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jirgin Faransa ƙirar A400M ne ya yi aikin jigilar sojojin Faransa da ke Yamai daga filin jirgin Diori Hamani zuwa na N'Djamena babban birnin Chadi.

Ta kori wakilin Faransa, Sylvain Itte tare da neman sojojin Faransan su fice daga ƙasar baki ɗaya.

Irin wannan taɓarɓarewar dangantakar ta fara ne da ƙungiyar Raya Tattalin ƙasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, wadda a baya ta ayyana cewa za ta iya ɗaukar matakin soji kan Nijar.

Yan Nijar da dama a yanzu haka na bayyana mabanbantan ra'ayoyinsu kan wannan taɓarɓarewar alaƙa tsakanin ƙasarsu da ke ƙarƙashin juyin mulkin soji da kuma manyan ƙasashen duniya da suka dogara da taimakonsu.

"A yau tafiyar da ake ciki talaka shi ke wahala, kuma yau duk wanda ya san Nijar, ya san tana cikin wahala.

A yau idan Nijar ta ce ba ta da ruwa da CEDEAO ba ruwanta da Najeriya, ba ruwanta da Tarayyar Turai da Amurka da kuma Faransa.

A ɗauka Faransa ba ta mana komai, tun lokacin da CEDEAO ta sa mana takunkumi kowa na ji a jikin shi.

Ka ga shinkafar nan da kake saya jaka goma yau jaka sha ake sayanta." in ji wani Dan Nijar.

Wani da yake da ra'ayin korar waɗannan ƙasashe ya ce: "Ni abin bai ba ni mamaki ba, saboda Faransa ta fito ta ce ba ta yarda da wannan juyin mulki ba, kuma abin da ya biyo baya kun gan shi, dama mutanen Nijar ba su son Faransan suna ta kiraye-kirayen su fice daga ƙasar.

"Yanzu ga Amurka ta fito ta yi makamanciyar wannan magana, ta ce ba za ta bayar da tallafi ba, ba za ta bayar da horon soji ba, ke nan ita ma sojojin nata cewa za a yi su tattara su yi tafiyarsu.

"Ka ga akwai Italiya, su ma duk suna nan, dukkansu wanga mataki da Amurka ta ɗauka shi ne nasu. Alamu na nuna tafiya za su yi, ina amfaninsu, yadda Faransa ba ta da amfanin komai haka nan sauran ƙasashen ba sa amfani komai," in ji wani mai goyon bayan korar ƙasashen.

Shi kuma wani mai sassaucin ra'ayi cewa ya yi,: "Sauran ƙasashe su tausaya mana, su san cewa ƙasarmu ta Nijar tana amfani da su kamar yadda suke amfani da ita.

"Ke nan lokacin hulɗa ne, mu ba ma jayayya da kowa, abu ne Allah ya kawo shi. Kamata ya yi su zo su kama mana, muma mu kama in ya so a fita cikin wannan matsala.

"Su ba sa son juyin mulki, mun amince, mu ma ba mu son juyin mulki. Su zo su kama mana a koma kan tafarkin dimokuradiyya. Domin in ba a zauna ba a iya a ciwo kan matsalolin da muke fuskanta a yau."