Yawan sojojin Nijar da aka kashe a harin Tillaberi ya ƙaru zuwa 60

...

Asalin hoton, getty images

Rahotanni sun ce adadin sojojin da suka mutu sanadin harin 'yan ta-da-ƙayar-baya, ranar Litinin 2 ga watan Oktoba a yammacin jihar Tahoua, ya ƙaru zuwa 60.

Akwai adadin wasu sojojin da suka ɓata, waɗanda har yanzu ba a san inda suka shiga ba.

Yana ɗaya daga cikin hare-hare mafi muni da 'yan ta-da-ƙayar-baya suka kai tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi cikin watan Yuli a ƙasar.

Lamarin na zuwa ne yayin da jakadan Rasha a Mali da Nijar ke ziyara a birnin Niamey.

Ma'aikatar tsaron Nijar tun da farko ta ba da sanarwar cewa sojoji 29 ne galibinsu daga runduna ta musamman ne aka kashe, yayin da ƙarin biyu suka jikkata.

Sai dai rahotannin kafofin yada labarai sun ambato majiyoyin fararen hula da na sojoji, na nuna cewa "aƙalla gawa 60 aka binne" a Tillia a kan idon ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Modi.

Ya dai ba da sanarwar cewa maharan sun yi amfani da ababuwan fashewa da motocin ƙunar bakin wake lokacin hare-haren.

A ranar Litinin ne 'yan ta-da-ƙayar-baya masu alaƙa da ƙungiyoyin Alqaeda da IS suka ƙaddamar da mummunan harin.

Bayan aukuwar lamarin ne, shugabannin mulkin soja na Nijar suka ayyana zaman makokin kwana uku a faɗin ƙasar, shi ne makoki na biyu da aka yi a cikin wata biyu.

A watan Agusta, an kashe sojoji aƙalla 17 a yankin Tillaberi yayin wani harin 'yan ta-da-ƙayar-baya. Irin wannan hari a makon jiya ma, ya yi sanadin kashe sojojin Nijar 12.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ƙarƙashin yarjejeniyar tsaro ta baya-bayan nan - mai taken Kawancen Sahel wadda ƙasashen Nijar da Burkina Faso da Mali suka sanya wa hannu, an tura sojojin Burkina, cikin watan jiya zuwa yankin Tillia don horas da dakarun Nijar na musamman a wani bangare na sabon ƙawancen tsaron.

Kungiyoyin 'yan ta-da-ƙayar-baya ga alama sun ƙara yawan hare-haren da suke kai wa lardin Tillaberi bayan shugabannin mulkin soja da suka ƙwaci mulki, sun kori dakarun Majalisar Dinkin Duniya da na Faransa da ke taimaka musu yaki da mayaka masu ikirarin jihadi.

Lamarin na zuwa ne yayin da jakadan Rasha a Mali da Nijar, Igor Gromyko ya gana da Birgediya Janar Abdurahmane Tchiani a birnin Niamey.

Ziyarar jakadan wata alama ce da ke nuna faɗaɗa ƙawancen Rasha a bangaren tsaro da na diflomasiyya a yankin Sahel, yayin da ake ci gaba da matsin lamba ga dakarun Faransa 1,500 su janye daga Nijar.

Nijar na fama da tashe-tashen hankula biyu na 'yan ta-da-kayar-baya da suka hada da wanda ya mamaye sashen kudu maso gabashin ƙasar daga yaƙin da aka dade ana fama da shi a Najeriya mai makwabtaka, da kuma hare-haren masu ikirarin jihadi da ke tsallakawa daga Mali da Burkina Faso.

Aljeriya na yunkurin shiga tsakani

Tashin hankalin na baya-bayan nan ya zo ne a daidai lokacin da masu juyin mulkin Nijar suka nuna cewa suna nazarin tayin da maƙwabciyarsu Aljeriya ta yi na shiga tsakani a tattaunawar miƙa mulki ga farar hula.

Aljeriya, makwabciyar Nijar mai fada-a-ji ta bayyana a ranar Litinin cewa, shugabanni a Yamai sun amince da tayin shiga tsakani a tattaunawar miƙa mulki hannun gwamnatin farar hula.

Sa'o'i kadan bayan haka, ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta nuna cewa akwai hukumomin Nijar da za su binciki tayin shiga tsakani na Aljeriya".

Lokacin miƙa mulki – Shugaban sojojin Nijar, Janar Abdourahmane Tiani, a baya ya ce za su miƙa mulki hannun gwamnatin farar hula a cikin shekara 3

A cikin watan Agusta ne, Aljeriya ta ba da shawarar miƙa mulki hannun farar hula a cikin wata shida karkashin jagorancin wani mutum da dukkan bangarorin siyasar kasar suka amince da shi.

Hukumomin birninAlgiers ba su ambaci takamaiman lokaci ba a cikin sanarwar da suka fitar a ranar Litinin, amma sun ce ministan harkokin wajen kasar Ahmed Attaf zai ziyarci Yamai "cikin dan kankanin lokaci da nufin kaddamar da tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki".

A martanin da suka mayar, shugabannin sojojin Nijar sun ce za a yanke shawarar tsawon lokacin miƙa mulki ne ta hanyar wata majalisa da suka kira dandalin ƴan ƙasar da za ta kunshi kowa da kowa.

Tun bayan juyin mulkin Nijar, hamɓararren Bazoum na tsare a gidansa na shugaban kasa tare da matarsa ​​da dansa. A ranar Litinin, lauyoyinsa sun ce sun shigar da ƙara a kan shugabannin juyin mulkin.

Wannan korafin da kamfanin dillancin labaran AFP ya gani, ya shafi Janar Tiani da “dukkan sauran mutane”, tare da zargin “kai hari da haɗa baki ga hukumomin gwamnati da laifuffukan da ma’aikatan gwamnati suka aikata da kama mutane da tsare su ba gaira ba dalili”.

Lauyoyinsa sun kuma ce suna daukaka kara zuwa ga wasu hukumomi biyu na hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ciki har da kungiyar da ke aiki kan tsare mutane ba bisa ka'ida ba.

Kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka -- a wani kiraye-kirayen da kawayen yammacin Afirka ke marawa baya -- ta yi barazanar yin amfani da karfi soji a matsayin mataki na karshe na maido da hamɓararen shugagan, Bazoum kan ƙaragar mulki, kuma ƙungiyar tana tattaunawa daban-daban da shugabannin Nijar.

Faransa dai na tsare da sojojinta kusan 1,500 a Nijar, tsohuwar kasar da ta yi wa mulkin mallaka a wani bangare na yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel, kuma shugabannin juyin mulkin sun bukaci a samar da “tsarin tattaunawa” don janyewarsu.