Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida and Buhari Muhammad Fagge
Kotun Kenya ta dakatar da batun tura dakarun ƙasar Haiti
Asalin hoton, Getty Images
Kotun ƙolin ƙasar Kenya ta bayar da umarnin dakatar da tura ɗaruruwan jami'an 'yan sanda na wani ɗan lokaci a wani mataki na taimakawa ƙasar Haiti wajen magance tashe-tashen hankulan 'yan daba.
Wata jam'iyyar adawa da wasu 'yan ƙasar biyu masu zaman kansu ne suka shigar da buƙatar dakatar da aikin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke marawa baya, waɗanda ke zargin cewa jibge 'yan sandan Kenya a wajen ƙasa ya saɓawa dokar ƙasa.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kimanin 'yan ƙasar Haiti dubu ɗari biyu ne suka rasa matsugunansu sakamakon ƙaruwar tashe-tashen hankula. Umarnin yana aiki har zuwa ranar ashirin da huɗu ga watan Oktoba; (Gwamnati da masu shigar da ƙara za su gabatar da cikakkun hujjojinsu cikin makonni biyu masu zuwa).
Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta tabbatar da yunkurin tattaunawar sulhu
Asalin hoton, EPA
Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta tabbatar da yunkurin shiga tsakanin Hamas da jami'an Isra'ila.
Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters, mai magana da yawun ma'aikatar ya ce ana ci gaba da gudanar da tattaunawar - gami da yiwuwar musayar fursunoni - tun a daren Asabar kuma tana "komai na tafiya yadda ya kamata".
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Majed Al-Ansari ya ce: "Abubuwan da muka sa a gaba su ne kawo ƙarshen zubar da jini da sakin fursunonin da kuma tabbatar da an shawo kan rikicin ba tare da ya shafi sauran yankin ba."
Har yanzu ba a san adadin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza ba, amma ana kyautata zaton cewa Hamas ta kwace mata da kananan yara da tsoffi da kuma sojoji.
Hamas ta ce ba ta da niyyan tattaunawa kan musayar fursunoni a lokacin da ake gwabza fada, a cewar mai magana da yawun ƙungiyar Hossam Badran, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na AFP.
Sahihan bidiyon harin da Hamas ta ƙaddamar kan Isra'ila
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Ƴan Shi'a sun yi tattakin goyon bayan Falasɗinawa a Abuja
Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta bayyana goyon bayanta ga Falasdinawa sakamakon rikicin da ya barke tsakanin su Isra'ila.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tattakin, wanda ya fara da misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin daga Banex Plaza Abuja, ya kare ne a kan titin Ahmadu Bello.
A cikin wata sanarwa da dan kungiyar Sheikh Sidi Munir Sokoto ya fitar, ya ce: “Mun samu kanmu a wata hanyar da ba za mu iya guje wa ba, an daure mu da riga guda daya ta kaddara. Duk abin da ya shafi ɓangare ɗaya kai tsaye, yana shafar kowa da kowa''.
Rikicin da ke da nasaba da hare-haren da aka kai a masallacin al-Aqsa da kuma sansanin 'yan gudun hijira na Gaza a shekarun da suka gabata, ya haifar da asarar rayuka fiye da 1,000 daga bangarorin biyu.
Yanzu muka fara - Netanyahu
Asalin hoton, EPA
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ci gaba da magana kan matakin da ƙasarsa ta dauka bayan hari mafi muni cikin shekaru da kasar ta fuskanta.
Ƙamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito cewa Natanyahu ya shaida wa jami'an kudancin Isra'ila da ke ziyara, cewa "abin da Hamas za ta fuskanta zai kasance mai matukar muni."
Netanyahu ya ci gaba da cewa "wannan somin-taɓi ne kawai...duk muna tare da ku kuma za mu fatattake su da karfin tsiya".
Sama da mutane 700 ne aka kashe a Isra'ila tun bayan da Hamas ta ƙaddamar da kutse cikin Isra'ila a ranar Asabar.
Aƙalla mutane 560 ne aka kashe a Gaza bayan da Isra’ila ta ƙaddamar da nata hare-haren a matsayin ramuwar gayya kan farmakin da mayakan Hamas suka kai.
Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza
Falasdinawa sun yi jana'izar mamatan Gaza
Ana kuma gudanar da jana'iza a fadin Zirin Gaza.
Dangi sun taru don jana'izar wasu 'yan gida daya da suka rasu a hare-haren Isra'ila na baya-bayan nan.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Masu makoki sun dauko gawar wani bafalasdine a kan titin Rafa da ke kudancin Gaza.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Dangi sun taru don jana'izar iyalin Shamalkh
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Mata na duban gawawwakin da aka rufe da likkafani
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Mata masu makoki suna bai wa juna baki da tausar zukatan juna
'Yan Isra'ila sun binne sojan da aka kashe a hare-hare
Isra'ila na jana'izar waɗanda suka mutu, bayan hare-haren da aka kai a baya-bayan nan.
Wata jana'iza da ake gani a nan, sojoji sun sauke akwatin gawar wani takwaransu sojan Isra'ila a kibbutz na Kfar Menahem, da ke kudancin Isra'ila.
Yuval Ben Yaakov ya mutu ne, yayin fafatawa da mayakan Hamas a kan iyaka da Zirin Gaza.
Ana iya ganin waɗanda suka halarci jana'izar suna rufe fuskokinsu lokacin da suke nuna takaici.
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Har yanzu akwai gawawwakin mayaƙan Hamas yashe a Isra'ila
Har yanzu gawawwakin mayakan Hamas na kwance a cikin ɓaraguzai, yayin da kuma tuni aka kwashe ƴan Isra'ila da aka kashe domin tantancewa da kuma binne su.
Wani direban Isra’ila ya tsaya inda ya dauki dutse don jifan wata gawar mayakin Hamas, lamarin da ya haifar da fushi a bangarorin biyu na kan iyaka.
Yayin da dakarun Isra'ila da ke da wadatattun kayan aiki ke ƙoƙarin kawar da sauran mayaƙan da ke da alhakin kai harin, Hamas na ci gaba da harba makaman roka, ba dare ba rana.
Na'urorin tsaron saman Isra'ila da ake kire 'Iron Dome' na aiki tukuru,amma duk da haka sun gaza tare dukkan rokokin da aka harbo daga Gaza.
Shirye-shiryen da Isra'ila ke yi na nuna cewa watakila suna shirin kai wani gagarumin farmakin soji a Gaza, inda tankokin yaki da sojoji da motoci masu sulke suka taru a kusa da kan iyaka.
Gaza 'nan gaba kaɗan za ta kasance babu man fetur, magunguna da abinci'
Bayanan bidiyo, Zagaye cikin mota a titunan Gaza da hare-haren Isra'ila suka fadawa
Zirin Gaza na daf da faɗawa cikin wata sabuwar matsalar ayyukan jin ƙan ɗan'adam idan aka hana kayan buƙatun rayuwa shiga yanki, a cewar hukumomi, yayin da Isra'ila ta mayar da martani ga hare-haren ƙungiyar Hamas.
Mazauna Zirin Gaza sun ce ba a shigar da kayan agaji ba tun ranar Asabar, kuma a ranar Litinin Isra'ila ta ayyana "datse komai gaba ɗaya" a yankin - inda ta ce za a yanke hasken lantarki da shigar da abinci da man fetur da kuma ruwan sha.
Gaza, yanki ne da mutane kimanin miliyan 2.3 ke rayuwa, kuma kashi 80 cikin 100 na mutanen sun dogara ne a kan kayan agaji.
Mutane sama da 500 ne suka mutu a can, yayin hare-haren ramuwar gayya na Isra'ila.
Isra'ila ce ke iko da sararin samaniyar Gaza da gaɓar ruwanta, kuma tana iyakance mutane da kayayyakin da za su iya tsallakawa cikin yankin..
Masar ita ma, tana matukar taƙaita mene ne da kuma wane ne zai tsallaka cikin Gaza, ta hanyar kan iyakarta da yankin.
Tun bayan hare-haren safiyar Asabar, Isra'ila ta dakatar da duk kayan masarufin da ke shiga Zirin Gaza, ciki har da abinci da magunguna. Mutane da dama a yanzu ba su da lantarki da intanet, kuma nan gaba kaɗan ba za su iya samun muhimman kayan buƙatun rayuwa, kamar abinci da ruwan sha ba.
Hukumomi sun yi gargaɗin cewa man fetur ɗin da ake da shi a Zirin Gaza, zai iya ƙarewa a cikin sa'a 24 zuwa 72.
Hukumar ayyukan jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargaɗin cewa man fetur ɗin da ake da shi ba zai wuce kwanaki ƙalilan ba.
Ko kafin taƙaita al'amura a baya-bayan nan, mazaunan Gaza tuni suke fama da tsananin ƙarancin abinci da taƙaita zirga-zirga da kuma ƙarancin ruwan sha.
Rikicin Gaza: 'Ban taba zaton zan rayu ba'
A ranar Litinin, ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce za su ƙaƙaba wani matakin "datse komai gaba ɗaya" a yankin.
"Ba lantarki, babu ruwan sha, babu iskar gas - duka za a datse SU," in ji shi, ya ƙara da cewa "muna faɗa da dabbobi ne kuma za mu ɗauki mataki gwargwado."
Ministan samar da ababen more rayuwa na Isra'ila daga bisani ya ba da umarnin katse ruwan sha zuwa Gaza nan take, yana cewa: "Abin da aka saba yi a baya, ba za a yi shi ba a nan gaba."
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar lafiya ta al'ummar Falasɗinawa ta ce asibitoci na fuskantar ƙarancin magunguna da kayan amfanin asibiti da man fetur saboda matakan Isra'ila.
Ta yi kira ga ƙasashen duniya su buƙaci Isra'ila ta "dawo da hasken lantarki", kuma ta samar da muhimman buƙatun rayuwa kamar magunguna da man fetur da jannaretocin lantarki.
Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta ƙaddamar da gagaruman hare-haren ramuwar gayya ta sama a Gaza tun ranar Asabar, inda ta kashe aƙalla mutum 511, tare da jikkata ƙarin 2,750, a cewar ma'aikatar lafiyar Falasɗin.
Daren Lahadi musamman ya ga manyan hare-hare, da yiwuwar su ne mafi girma da Gaza ta yi fama da su a cikin shekaru - gaba ɗaya tsawon daren, an yi ta jin tashe-tashen bam masu ƙarar gaske bi-da-bi a faɗin Zirin.
Yayin da hare-haren suka ci gaba da gudana bayan alfijir, baƙin hayaƙi ya mamaye sararin samaniya, kuma ana iya jin ɗanɗanon ƙurar gine-ginen da suka ruguje a cikin iska.
Wasu daga cikin hare-haren, an kai su ne a yankin kan iyaka da ke gabashin Gaza, daga inda mayaƙan Hamas suka ƙaddamar da hare-harensu da safiyar Asabar.
Ga alama Isra'ila tana kai farmaki kan waɗannan yankuna ne, daidai lokacin da take ƙoƙarin haɓaka matakan tsaro a can.
Akwai kuma rahotanni daga shaidu da ke cewa Isra'ila na amfani da makaman atilare a yankin kan iyaka.
Isra'ila ta ce tana kai hare-hare ne kan tungogin Hamas ne a Gaza, sai dai akwai rahotannin da ke cewa ana far wa fararen hula.
Ma'aikatar harkokin wajen Falasɗin ta ce hare-haren Isra'ila sun auka wa sansanonin 'yan gudun hijira guda biyu a Gaza - Al-Shati (wanda ake kira sansanin bakin teku) da kuma sansanin Jabalia - inda rahotanni suka ce, an jikkata mutane da dama, wasu kuma sun rasu.
Wani bidiyo da aka yaɗa a intanet daga Jabalia, ya nuna hargitsewar al'amura sosai, ciki har da wata gawar mutum da ake ƙoƙarin ɗaukewa da kuma wani mutum wanda ƙura da jini suka lullube jikinsa.
Ma'aikatar harkokin wajen ta kuma ce hare-haren ta sama sun samu wata makaranta ta Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, wadda ke tsugunnar da ɗaruruwan fararen hula ciki har da ƙananan yara da tsofaffi.
An yi ganawar tarihi tsakanin Isra'ila da Falasdinu
Yadda zaman fargaba ke karuwa a Yammacin Kogin Jordan
Da gaske an saki Sunday Igboho mai rajin kare ƙabilar Yarbawa?
'Mun kashe wasu mayaƙa da suka nemi shigowa Isra'ila daga iyakar Lebanon'
Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Isra'ila sun sanar da kashe wasu mayaka da suke yunƙurin tsallaka iyakar Isra'ila daga Lebanon.
Sojojin sun ce suna samun taimakon jirge masu saukar ungulu ne daga rundunarsu.
Sanarwar da sojojin suka fitar ba ta fayyace ko da suwa mayaƙan ke da ƙawance ba.
Kakakin Hezbollah ya ce dakarun Lebanon ba su da hannu cikin harin Isra'ila
Ana yi wa Shahrukh Khan bazaranar kisa
Asalin hoton, Bollywood
Rundunar 'yan sandan Maharashtra ta ƙara yawan jami'an tsaron da za su riƙa bai wa fitaccen tauraron nan na Bollywood Shahrukh Khan kulawa saboda barazanar da ake masa da rayuwarsa.
Akwai jami'an tsaro na kwamfanin Y Plus 11 da suke tare da shi, ciki har da kwamdoji 11 da motar 'yan sanda da ke rakiya guda daya.
Kamfanin dillancin labarai na PTI ya ambato wani jami'in 'yan sanda na cewa Shahrukh Khan na fuskantar barazana game da rayuwarsa tun bayan sakin fim ɗinsa na 'Jawaan".
Amma kuma Shahrukh Khan ne zai riƙa biyan kuɗin jami'an da za su riƙa gadinsa.
A cewar rahotannin Shahrukh Khan ya higar da ƙara a hukumance ga Gwamnatin Maharashtra cewa ana yi masa barazanar kisa.
'Yan sanda sun ce nan da awa 24 za a kai wasu jami'ai hudu gidan Shahrukh Khan daga Mumbai.
Abin da ya sa tauraruwar Sharuhkhan ke ci gaba da haskawa duk da sauyin zamani
An aike sakon barazanar kisa ga Potter da iyalansa
Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
Kotu ta yanke wa dan sanda hukuncin kisa kan laifin kashe lauya a Lagos
Asalin hoton, Getty Images
Babbar kotun jihar Lagos ta samu wani mataimakin sufirtandan da aka dakatar daga aiki - da laifi inda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda hallaka wata lauya mazauniyar birnin Lagos.
Mai shari'a Ibironke Harrison ta cimma matsayin cewa masu shigar da kara wato gwamnatin jihar Lagos sun tabbatar da hujja ta yankan shakku a kan mutumin da ta samu da laifi, wato ASP Vandi.
"Kotu ta samu wanda aka yi kara da laifi a kan tuhuma daya ta aikata kisa. Kuma za a rataye ka ta wuya har sai ka mutu." alkaliyar ta ce.
A ranar 16 ga watan Janairu ne gwamnatin jihar Lagos ta gurfanar da Vandi a gaban kotu saboda harbin lauya mai juna biyu 'yar shekara 41, Barista Omobolanle Raheem a shingen bincike na Ajah ranar 25 ga watan Disamban 2022.
'Da kuɗin tallar lemu na tura ƴata makaranta har ta zama lauya'
Me ya kawo fargabar rashin tsaro a Lagos?
Saka ba zai buga wa Ingila wasa da Austalia da Italiya ba
Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce mutum 511 sun mutu a hare-haren Isra'ila
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce an kashe mutum 511 kuma an jikkata 2,750 bayan hare-haren roka da Isra'ila take kai wa Zirin Gaza tun daga safiyar Asabar.
Isra'ila ta ce tana kai hare-haren bam ɗin ne kan wuraren Hamas bayan wani hari da Isra'ila ba ta yi tsammani ba a safiyar Asabar da Falasɗinawa suka kai, suka riƙa harbi kan me uwa da wabi.
Rikicin Isra'ila da Falasdinu: Rayuwa a Zirin Gaza
Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
Nijar ta rage kasafin kudinta da kashi 40 cikin 100 saboda takunkumi
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Nijar ta sanar da rage kashe kudaden da take shirin kashewa a shekarar 2023, inda ta rage kasafin kudinta da kashi 40 cikin dari.
Wannan shawarar ta zo ne bayan takunkumin da kasashen duniya suka kakaba wa kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.
Gwamnatin mulkin sojan ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka watsa ta gidan talbijin a ranar Asabar din da ta gabata.
Sojojin sun sanar da rage kasafin kudin daga dala biliyan 5.3 (£4.3bn) zuwa dala biliyan 3.2, duk da cewa ba a samu cikakkun bayanai na rage kuɗaɗen ba.
Akalla kashi 40 cikin 100 na tallafin kasafin kudin kasar Afirka ta Yamma ana sa ran zai fito ne daga abokan huldar waje.
Juyin mulkin da ya hamɓarar da shugaba Mohamed Bazoum ya janyo hukumomi kamar kungiyar ECOWAS da Tarayyar Turai da Amurka sun sanya takunkumi da datse kadarori, da rufe kan iyakokin ƙasar da kuma dakatar da kayan agaji.
Wadannan matakan sun haifar da tashin gwauron zabin abinci da karancin kayan masarufi, da suka hada da magungunan ceton rai.
Gwamnatocin sojoji da ke makwabtaka da Mali da Burkina Faso dai sun goyi bayan juyin mulkin Nijar.
Takunkumin da Ecowas ta saka wa Nijar ya fara haifar da tsadar rayuwa
China ta ƙaƙaba wa jami'an Amurka takunkumi
An kashe Amurkawa tara a harin da aka kai Isra'ila
Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Amurka ta tabbatar da mutuwar 'yan ƙasarta tara a Isra'ila.
Cikin wata sanarwa Fadar White House ta ce " muna miƙa ta'aziyyarmu ga waɗanda abin ya rutsa da su da muka iyalansu, kuma muna fatan waɗanda suka jikkata za su warke da wuri."
"Kuma za mu ci gaba da bibiyar wannan lamari kuma mu ci gaba da tattaunawa da abokanmu na Isra'ila, musamman hukumominsu."
Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
Isra’ila ta umarci Falasɗinawa su fice daga gidajensu
'Fargaba da rusa gidaje sun raba mutum 123,000 da muhallansu'
Asalin hoton, Reuters
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 123,538 ne aka raba da gidajensu a Gaza, akasari "saboda fargaba da damuwa a kan tsaron rayuwa da ruguza musu gidaje".
Ofishin Babban jami'in Ayyukan jin kai ya kara da cewa mutum 73,000 ne suka je makarantu don samun mafaka.
Adnan Abu Hasna - mai magana da yawun hukumar kula da Falasdinawa 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai tsammanin adadin zai karu.
"Akwai wutar lantarki a waɗannan makarantu, mun samar musu da abinci da ruwan sha mai kyau, da magunguna domin su samu nutsuwa," in ji shi.
Akwai mutum miliyan biyu da rabi da ke rayuwa a Gaza. Gabanin gabatar da hare-harenta na ramuwa a ranar Asabar, kuma Isra'ila ta yi gargaɗin cewa mutane su bar yankunan da dama.
"Ina kira ga mutanen gaza da su fice daga yankin yanzu, domin muna dab da fara kai hare-hare ko ina a kowanne lokaci da duka ƙarfinmu," in ji Firaiminista Benjamin Netanyahu.
Wace ce Hamas, mene ne ke faruwa a Isra'ila, da sauran tambayoyi
Mulkin mallakan da ya hargitsa rayuwa a Gabas ta Tsakiya