'Ayyukan Isra'ila ka iya jefa Gabas ta Tsakiya cikin haɗari'

Mutum na biyu mai ƙarfin faɗa a ji a Hezboullah - wata rundunar sojojin sakai mafi ƙarfi a Lebanon da Iran ke marawa baya - ya ce kisan da Isra'ila ke yi wa fararen hula a Gaza ka iya jefa Gabas ta Tsakiya cikin haɗari.
Sheikh Naim Qassem ya shaida wa BBC cewa "za a iya fuskantar wani yanayi maras kyau a yankin, kuma babu wanda ya isa ya dakatar da faruwar hakan".
Mataimakin shugaban Hezboullah ya bayyana haka ne yayin tattaunawar da ya yi a Beirute, yayin da ma'aikatar lafiyar da Hamas ke tafiyarwa a Gaza ta ce an kashe sama da mutum dubu goma a yankin.
Kashe-kashen Isra'ilan ya biyo bayan harin da Hamas ta kai mata ne a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 1,400 - kuma 1,000 daga cikinsu fararen hula ne.
"Haɗarin da ake fuskanta na gaske ne, saboda Isra'ila na ƙara sauke fushinta kan fararen hula tana kashe mata da yara ƙanana. Ana tsammanin a ci gaba da irin waɗannan hare-hare kuma a zauna lafiya a wannan yankin? ba na tsammanin hakan mai yiwuwa ne."
Ya daga kan cewa ƙaruwar hakan zai zama yana da alaƙa da matakan Isra'ila. "Duk wani mataki na da sakamako," in ji shi.
Hezboullah, "ƙungiyar Allah ce," tana da hanyoyi daban-daban masu yawan gaske.
Ƙuniyar 'yan Shi'an da Amurka da Birtaniya da ƙungiyar ƙasahsen larabawa ke mata ƙallon ƙungiyar "yan ta'adda" - ita ce babbar jam'iyyar siyasa da kuma ta dakarun soji mafi girma a Lebanon.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya zuwa yanzu matakin da take ɗauka game da rikicin gaza ya hada da jankunne mai ƙarfi, amma tana bi a hankali wajen rawar da take taka wa.
Yayin da wani hari Isra'ila ta sama ya kashe wata mata da yara uku a kudancin Lebanon ranar Lahadi, ita ma Hzboullah ta yi amfani da wani makamin roka a rikicin ta kashe wani Baisra'ile guda.
Shugaban Hezboullah Hassan Nasrallah ya yi gargaɗin cewa duk farar hular da aka kashe a Lebanon za a girbi irinsa a tsallake iyaka. Sai dai bai gargaɗi Isra'ila a kan shiga yaƙi ba.
"Yayin da ya jaddada cewa "an gabatar da duk wani zaɓi da ya kamata" ƙungiyar mayaƙan sakan ta tabbatar da cewa ita ce ta kai harin kan iyakar da kanta, anda ya nufi sojoji kai tsaye.
An lashe mayaƙanta sama da 60 amma tana da mayaƙan da a shirye suke su maye gurbinsu.
Wani mayaƙi da aka binne a Lebanon a wannan makon shi ne na biyar a gidansu da suka mutu wajen yi wa Hezboullah yaƙi.
Tun daga farkon tattaunawar har ƙarshe mataimakin shugaban Hezboullah na son nuna cewa ƙungiyar ta kare kai ce - duk da cewa a 2006 ta yi wa Isra'ila rushe-rushe kuma ta sace mata wasu sojinta biyu a wani harin kan iyaka da ta kai.
Sheikh Qassem ya yi iƙirarin Isra'ila ce " ta takali rikicin Gaza a boye".
Lokacin da BBC ta ce a bayyane yake Hamas takai hari a ranar 7 ga watan Oktoba, sai ya bayyana harin a matsayin na ramuwa kan mamayar da Isra'ila take yi wa ƙasar Falasdinawa.
Ya kuma maimaita wani iƙirarinsa da babu hujja cewa dakarun Isra'ila ne suka kashe fararen hularsu ba Hamas ba. Amma ina kyamarar jikin hulunan kwanasu da suka nuna yadda suka kai harin?
Sai ya mayar da amsar tambayar da cewa " Me yasa ba kwa ganin abin da Isra'ila ke yi a Gaza,". "Suna kashe fararen hula suna rushe gidaje."
Ya kira harin da Hamas ta kai a matsayin "gagarumin sakamako ga turjiyar Falasdinawa" ya musanta suna jin jiki kan hakan. Ina batun mutum 10,000 da aka kashe a Gaza tun bayan harin?" kisan ƙare dangin da Isra'ila ke yi shi yake ƙara wa Falasdinawa ƙaimi su kare ƙasarsu.
Ya yarda cewa Iran na "taimakawa har ta hanyar kuɗi" ga Hezboullah ama ya ce ba Iran ba ce ke faɗin yadda kungiyar za ta yi ba. Sai dai masana na cewa Tehran ke yanke hukuncin shiga yaki ko kuma akasin hakan.
Idan har dakarun Isra'ila suka faɗa yaƙi da Hezboullah to za su fafata da maƙiyan da ke da makaman da ko wasu ƙasashen ba su da su. Ana hasashen Hamas na da makaman roka da masu linzami da suka kai 150,000.
Tana da mayaƙa kimanin dubu 60, ciki har da dakaru na musamman, da mayakanta na ko da yaushe da kuma na ko-ta-kwana a cewar Nicholas Blandford, wani mai sharhi kan harkokin tsaro da ke zaune a Beirut, wanda ya karanci Hezboullah na gwamman shekaru.
A 2006 vƙungiyar ta fafata da Isra'ila amma Lebanon aka fi yi wa barna. An kashe mata sama da mutane 1,000, kuma mafi yawansu fararen hula ne, kuma duka ƙasashen da ke makwabtaka Hezboullah na da ƙarfi a cikinsu. Ita kuma Isra'ila an kashe mata sojoji 121 da fararen hula 44.
Akwai abubuwa da dama da za su iya ƙara ta'azzara wannan shikici - ya haifar da yaƙi tsakanin Hezboullah da Isra'ila. Kuma idan hakan ya tabbata zai haifar da ɓarna mai yawa a yankin, in ji Blandford.
"Zai mayar da abin da ke faruwa a Gaza kamar wasan yara." ya shaida wa BBC.
"Za a rufe Isra'ila baki ɗaya na lokacin rikicin. Kuma mafi yawan al'umarta za su koma fakewa a tantuna," in ji shi.
"Babu wani batun hukumar jiragen sama ko ta ruwa. Makamin mai linzamin Hezboullah zai kai ga sansanin sojin kasar da ke tsallaken iyaka."
A yanzu dai daga Hezboullah har Isra'ila da Iran suna kaffa-kaffa, wasu tsoffin magaunta da suka sake tsintar kansu a wata duniyar adawa.











