Ko tsagaita wuta na iya kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas?

Asalin hoton, Getty Images
Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan wata 15 ana gwabza yaƙi a Gaza.
Hakan na zuwa ne ƴan kwanaki gabanin rantsar da Donald Trump a karo na biyu a matsayin shugaban Amurka a ranar 20 ga watan Janairu.
Ana fatan wannan tsagaita wuta - wadda ta wucin-gadi ce - za ta rikiɗe zuwa zaman lafiya na dindindin.
Amma kamar yadda aka gani a sauran rikice-rikice, wannan zai buƙaci a gudanar da gagarumin aikin diflomasiyya.
Me ake nufi da tsagaita wuta?
A cewar Majalisar Dinkin Duniya babu wata fassarar da kowa ya amince da ita ta kalmar ''tsagaita wuta'', duk da cewa kalmar ta samo asali ne daga umarnin soji na ''tsayar da wuta'', wanda shi ne akasin umarnin ''bude wuta''.
Ma'anarta na iya nufin duk abin da ɓangarorin da ke rikicin suka amince ta zama a yayin da suke tattaunawar sulhu.
Amma, Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai bambanci tsakanin ''tsagaita wuta'' da kuma ''dakatar da ƙiyayya''.
Ta ce ''dakatar da ƙiyayya'' wata yarjejeniya ce ta fatar baki da ke nufin a dakatar da faɗa ko adawa tsakanin ɓangarorin biyu.
''Tsagaita wuta'' kuma na kasancewa yarjejeniya ce da ta ke a rubuce, kuma wadda ke ɗauke da sharuɗɗa da suka haɗa da:
- Dalilin tsagaita wutar
- Matakan siyasa da za su biyo bayan hakan
- Lokacin da za ta fara aiki
- Faɗin yankin da za ta shafa
Za kuma ta iya ƙunsar bayanai kan irin ayyukan sojin da za a iya gudanarwa da waɗanda aka haramta da kuma yadda za a sanya ido kan tabbatar da an kiyaye sharuɗɗan yarjejeniyar.

Asalin hoton, Getty Images
Misali, yaƙin basasa a da ta ɓarke a Liberia ya zo ƙarshe a shekarar 1993 lokacin da gwamnatin riƙon ƙwarya ta haɗin kan ƙasa ta ƙulla yarjejeniya da Jam'iyyar National Patriotic Front of Liberia da United Liberation Movement of Laberia for Democracy.
Bangarorin biyu sun amince da dakatar da shigo da makamai da alburusai, an kuma dakatar da kai hare-hare kan wuraren soji, an kuma hana tayar da zaune tsaye, an kuma haramta amfani da nakiyoyi da sauran abubuwa masu fashewa.
Shin tsagaita wuta matakin wucin gadi ne ko kuma na dindindin?
Yana iya zama duka biyun, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
Wani lokaci, ɓangarorin biyu da ke rikici da juna na iya amincewa da tsagaita wuta na wucin gadi, ko kuma a matsayin matakin farko na sulhu.
Wannan na iya zama don rage tashin hankali ko kuma sawwaƙe matsalolin jin-ƙai.
Lokacin da Isra'ila da Hamas suka amince da tsagaita wuta na wucin gadi, wanda ya gudana tsakanin ranar 24 ga Nuwamba zuwa 30 ga Nuwamba, 2023, Hamas ta saki mutane 105 da ta yi garkuw da su domin karɓo wasu fursunoninsu guda 240.
Hakanan za'a iya amincewa da tsagaita wuta a matsayin matakin farko domin samar da ingantaccen yanayi da zai taimaka wurin tattauna hanyoyin da za a iya bi domin cimma yarjejeniyar tsagaiata wuta ta dindindin.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin watan Yunin 2000, Habasha da Eritria sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya don kwantar da tarzoma ta yadda za a iya gudanar da tattaunawar tsagaita wuta. An sanya hannu kan wannan yarjejeniya ce a watan Disamba, a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar Algiers da ta kawo ƙarshen yaƙinsu.
Duka da haka, ana iya ci gaba da yaƙi bayan an ƙulla yarjeniyoyin tsagaita wuta na wucin gadi masu rauni.
Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta shiga tsakani atattaunawar tsagaita wuta don ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin basasa a Labanon a shekarun 1978 da 1981 da kuma 1982. Sai dai faɗa ya ɓarke bayan kowace yarjejeniya kuma yakin da aka fara a shekarar 1975, bai ƙare ba sai a shekarar 1990.
A wasu lokuta, ɗaya ko duka ɓangarorin biyu da ke rikici na iya neman yin amfani da tsagaita wuta na wucin gadi don ƙarfafa matsayinsu a ƙasa.
Tabbataciyar tsagaita wuta (ko ta dindindin) yawanci tana zuwa ne bayan an yi nasarar tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarorin biyu da ke yaƙi da juna.
Yawanci ta kan shafi kwance damara ko wargaza rundunonin dakarun da ke ƙasa, amma tsare-tsaren tsaro na iya ci gaba da kasancewa har tsawon shekaru masu yawa bayan cimma yarjejeniyar.

Asalin hoton, Getty Images
Misali Yarjejeniya 'good Friday' da aka yi a yankin Ireland ta Arewa ta ƙushi sharaɗin cewa ƙungiyar IRA da sauran ƙungiyoyi da su amince da matkin jingine makamansu.
Yarjejeniyar ta kuma ƙunshi sharuɗɗan da ke da niyyar bunƙasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da suka haɗa da buɗe iyakokin Ireland ta Arewa da Jumhurriyar Ireland domin gudanar da hada-hadar kasuwanci.
Waɗanne irin nau'ukan taƙaitattun tsagaita wuta ake da su?

Asalin hoton, Getty Images
Isra'ila da Hamas sun kira tsagaita wuta na wucin gadi da aka yi a watan Nuwamba 2023 a matsayin "dakatar da buɗe wuta na jin-kai".
A wasu lokuta ana amfani da dakatar da buɗe wuta na jin-ƙai don rage zafin faɗan ko kuma a rage matsalolin jin-kai.
Misali gwamnatin Sudan ta amince da tsagaita wuta da ƙungiyoyin ƴan ta'adda guda biyu, wato Sudan Liberation Movement da Justice and Equality Movement, waɗanda suka dakatar da faɗan da ake yi a Darfur na tsawon kwanaki 45 domin bai wa hukumomi damar kai kayan agaji ga al'ummar yankin.
A shekara ta 2004, bayan da bala'in tsunami ya afkawa ƙasar Indonsia, gwamnatin ƙasar Indonesiya da kuma ƴan ƙungiyar 'Free Aceh Movement' sun sanar da tsagaita wuta domin a kai agaji a yankunan da suke gwabza faɗa.
Haka kuma ana iya samun yarjejeniyoyin dakatar da fada a wani yanki, wanda ake kira tsagaita wuta a yanki.
A cikin 2018, Majalisar Dinkin Duniya ta ƙulla yarjejeniya tsakanin gwamnatin Yemen da ƴan ƙungiyar Houthi domin dakatar da faɗa a kusa da tashar jiragen ruwa ta Hodeida na Bahar Maliya don kare al'ummar yankin.











