Yara biyu sun rasu a rigima tsakanin masu kallon ƙwallon ƙafa da ƴansanda a Chile

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ƙananan yara guda biyu sun rasu bayan rigima ta ɓarke tsakanin masu kallon ƙwallon ƙafa da ƴansanda a ƙasar Chille.
An samu hargitsin ne kafin fara wasa tsakanin ƙungiyar Colo Colo da ke Chille da takwararta Fortaleza ta Brazil a gasar cin kofin Copa Libertadores.
An samu matsala ne lokacin da ƴansanda suka hana masu kallon kallon ƙwallo kusan guda 100 shiga filin wasan.
"Bayanan da muka tattara shi ne wata katanga ce ta faɗo kan yaran nan guda biyu, amma muna cigaba da bincike ko motar ƴansanda ce ta kashe su," in ji mai bincike Francisco Morales.
Kafofin watsa labaran ƙasar sun ruwaito cewa yaran da suka rasu akwai mai shekara 13 da 18.
Shugaban ƴansanda Alex Bahamondes ya ce an kama ɗansanda guda ɗaya bisa zarginsa da laifi, kuma yana tsare, "ana cigaba da ɗaukar bayanansa game da lamarin."
An fara wasan bayan turmutsutsun, amma daga bisani aka dakatar.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta kudancin Amurka Conmebol ta ce tana, "tana alhinin mutuwar yaran guda biyu a kusa da filin wasan."











