Argentina za ta buga wasan ƙarshe da Colombia

h

Jefferson Lerma ya ci wa Colombia kwallo daya mai ban haushi a wasan kusa da ƙarshe da suka doke Urugay da mutum 10 kacal a gasar Copa America.

A yayin wasan an samu hargitsi tsakanin wasu 'yan wasa da magoya baya kafin a tashi.

Dan wasan Liverpool Darwin Nunez wanda ya shiga damuwa, ya zubar da damarmaki da yawa a wasan, kafin daga baya dan wasan Crystal Palace Lerma ya ci kwallo daya da kai.

Dan wasan tsakiyar ƙungiyar James Rodriguez ne ya kawo masa kwallo a minti na 39 da fara wasan, ta kwanar da suka samu.

A

Asalin hoton, Getty Images

A ƙarshen mintina 45 da fara wasan ne dan wasan Colombia Daniel Munoz ya samu katin gargaɗi na biyu bayan duka Manuel Ugarte da ya yi da hannunsa.

Urugay sun yi ƙoƙarin farke kwallon da aka ci su, ko da yake Luis Suarez ya farke kwallon ama ba a ansa ba.

Mateus Uribe ya zubar wa da Colombia wasu damarmaki guda biyu a ƙarshen lokaci amma duk da haka sai da suka yi nasara.

Yanzu Colombia za ta fafata da Argentina a wasan ƙarshe na Copa America a ranar Litinin 15 ga wasan Yuli da misalin ƙarfe daya na dare.

Ita kuma Urugay za ta ɓarje gumi ne a matakin neman na uku da Canada a ranar Lahadi 14 ga watan.