Yaran da ke yin kayan sawa da tarkacen leda da robobin bola a Najeriya

Hoton yarinya sanye da rigar da aka yi da shara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sama da kashi 80 cikin 100 na sharar robobi da ake fitarwa a Najeriya ba a sake sarrafat, a cewar cibiyar kididdiga ta cibiyoyin lafiya.

Yaya kuke yi da jaridunku bayan gama karantawa da kuma ledoji da kwalayen lemo ko kwalabe?

Ga mutane da dama, amsar ita ce suna zubar da su a shara – sai dai hakan ya sha bamban ga wata kungiya a Najeriya da ta rungumi tattara irin wadannan tarkace ko shara suna sarrafa su tare da matasa masu fafutika zuwa abubuwan ado.

Shiri ne na karfafa sarrafa wadannan abubuwa zuwa kayan ƙawa domin tallata ado da kwalliya.

A yanzu, ado da kwalliya kusan su ne suka mamaye kashi 10 cikin 100 na sinadarin kabon (carbon) da ake fitarwa, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar Greenfingers ke jagorantar gangamin tsaftace muhalli a birnin Legas na Najeriya, tun 2012.

Amma a ranar Asabar, sun mayar da hankali wajen shirya taron tallata kayan ƙawa da aka ƙirƙira daga shara a matsayin sabon hanyar ankarar da duniya dabarun rage shara da sake sarrafa su zuwa abubuwan amfani.

Mahalarta taron sun kasance cikin farin ciki da neman karin bayanai kan abubuwan da suka gani, kamar yadda shugaban kungiyar

Asalin hoton, Greenfingers Wildlife Conservation

Bayanan hoto, Mahalarta taron sun kasance cikin farin ciki da neman karin bayani kan abubuwan da suka gani, a cewar shugaban kungiyar

Chinedu Mogbo wanda kuma ya kafa kungiyar ya shaida mana cewa akwai ƙarancin ilimantarwa kan gurbata muhalli da matsalolin sauyin yanayi don haka irin wannan taro da suka yi wa lakabi da “trashion” shi ne hanyar ƙayatarwa da ilimantar da al’umma.

"Muna son matasa su kasance a cikin wannan gangamin na rayuwa a tuddai da kuma ruwa," a cewar Mogbo, wanda ya ƙuduri aniyar shi ma kaso mai girma na sarrafa bola zuwa abubuwan ƙayatarwa na jan hankali.

Greenfingers Wildlife Conservation

Asalin hoton, Greenfingers Wildlife Conservation

Bayanan hoto, Jakar leda da ake amfani da ita wajen siyayya yanzu ta kasance abin da aka sarrafa zuwa tufafin ado da kwalliya.

Sai dai sarrafa bola a Najeriya ba abu ne mai sauki ba: Akwai damuwa daga ɓangaren masu kula da bola ko shara, ana karɓan wannan shara a wuri guda sannan a kai su wani waje na daban – ma'ana ayyukan ba sa tafiya yadda suka dace.

Don haka shirin trashion na nuna hanyoyi mafiya dacewa na gudanar da wannan ayyuka da dabarun sarrafa bola wanda a baya babu masaniya ko kwarewar hakan, a cewarsa.

Chinedu na da yardar cewa "Najeriya ta fi bayar da fifiko a fannin mai, kuma batun dogara da wannan fannin ba mai dorewa ba ne kamar yadda alamomi ke nunawa nan gaba," a cewarsa.

Sharar da aka tattara daga kwatoci da magudanar ruwa da bakin teku da sauran yankunan al'umma – sun samu damar kasancewa tufafin da aka yi bajakolinsu a wannan taro.

Green fingers

Asalin hoton, Green fingers wild life

Bayanan hoto, Greenfingers ta ce Najeriya na rasa damarta a fanin noma da kiwo saboda wasu dalilai.

Kuma hakan na nuna dole a bijiro da wasu dabaru kamar wannan taro mai jan hankali.

"Na yanke shawarar fitowa na yi wannan taro a bana, saboda ina son samar da canji, mun ga sauyin da matsalolin yanayi ke haifarwa, don haka gaskiya ina son kawo sauyi," a cewar Nethaniel Edegwa yar shekara 16.

Greenfingers Wildlife Conservation

Asalin hoton, Greenfingers Wildlife Conservation

Bayanan hoto, Kwalabe da robobi da ledojin shara da kwano na daga cikin abubuwan da aka sarrafa aka tallata a taron ado da kwalliyar.