Dalilai uku da suka sa ɗaliban Kano suka yi zarra a jarrabawar NECO ta 2025

    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Gwamnati da masana harkokin ilimi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya na ci gaba da murnar nasarar da ta samu bayan ta zarta duka jihohin ƙasar a yawan ɗaliban da suka fi cin jarabawar kammala sakandare ta 2025.

A ranar Laraba ne hukumar National Examinations Council (NECO) ta sanar da sakamakon jarabawar ta kammala sakandare, inda ɗaliban Kano suka fi saura cin darussa aƙalla biyar ciki har da Turanci da Lissafi a 2025.

Tsarin ilimi a Najeriya ya tanadi cewa ba za a bai wa ɗalibi shaidar kammala karatun sakandare ba wato Senior School Certificate Examination (SSCE) sai ya rubuta sannan ya ci Neco ko kuma takwararta ta West Africa Examination Council (Waec).

Gwamnatin Najeriya ce ke shirya Neco, yayin da hukumar ƙasa da ƙasa ke shirya Waec a wasu ƙasashen nahiyar Afirka ta Yamma.

Tuni gwamnatin Kano ta bayyana farin cikinta game da sakamakon, tana mai cewa yunƙurin da ta yi na "gagarumin gyara a fannin ilimi" ne ya jawo nasarar.

Wannan ne karo na farko da Kano ta samu irin wannan nasara a tsawon shekaru da dama duk da irin yawan ɗaliban da take da su da ke rubuta jarabawar duk shekara.

Wasu rahotonni na cewa rabon da ɗaliban Kano su samu irin wannan nasara tun shekara 20.

Ta yaya Kano ta yi zarra?

Da yake bayar da sanarwar a birnin Minna na jihar Neja, shugaban hukumar Neco Farfesa Ibrahim Wushishi ya ce Kano ta zarta saura da ɗalibai 68,159 (kashi 5.02 cikin 100 na jimillar ɗaliban Najeriya) waɗanda suka ci darussa biyar ko fiye, ciki har da Lissafi da Ingilishi.

Jimillar ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarabawar ta a tsakanin watan Yuni zuwa Yulin 2025, inda 818,492 - kashi 60.26 cikin 100 - suka ci darussa biyar haɗi da lissafi da Ingilishi.

A cewar Farfesa Wushishi, jimillar ɗalibai 1,144,496 (kashi 84.26 cikin 100) ne suka ci darussa biyar ko fiye da haka a duka darussa tara da suka rubuta jarabawar a kansu.

Nasarar da Kanon ta samu ta zarta ta jihohi kamar Legas, wadda ke biye mata da ɗalibai 67,007, da kuma Oyo a mataki na uku da ɗalibai 48,742.

Mene ne sirrin samun nasarar?

Masana na alaƙanta wannan nasara da dalilai da dama, ciki har da matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka, domin bunƙasa harkokin ilimi a jihar.

Dalilan sun haɗa da:

Kasafi mai yawa a fannin ilimi

Cikin kasafin kuɗinta na farko a shekarar da ta kama mulki a 2023, gwamnatin jam'iyyar NNPP ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware wa ɓangaren ilimi naira biliyan 95 daga jimillar biliyan 350 - kashi 27.1 cikin 100 na jimillar kasafin.

Bayan haka, a ranar 8 ga watan Yunin 2024 gwamnan ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimin, sannan ya yi iƙirarin cewa gwamnatinsa ta ɗauki ƙarin malamai 5,000 domin inganta sashen.

Bugu da ƙari, gwamnatin ta sake ware wa ɓangaren ilimi kashi 31 cikin 100 (naira biliyan 198) na kasafin kuɗin shekarar 2024.

Kasafin ya zarta kashi 15 zuwa 20 da hukumar kula da ilimi ta Majalisar Ɗinkin Dunya Unesco ta bayar da shawara ga duka gwamnatoci da su dinga ware wa ɓangaren ilimi duk shekara.

Haka nan, kasafin ya zarta adadin da muradin ƙasa kan ilimi da Najeriya ke bi ya tanada na kashi 26 cikin 100 na kasafin kuɗi a matakin gwamnatin tarayya.

Kwamashinan Ilimi na Kano Ali Haruna Makoda ya faɗa wa BBC cewa jajircewar gwamna ce ta jawo baki ɗayan nasarar.

"Duk lokacin da ka samu jajirtaccen mutum dole za a samu nasara," in ji shi.

Sai dai Dr Bilyaminu Bello Inuwa, malami a Tsangyar Ilimi ta Jami'ar Bayero, ya ce ba za a tabbatar da wannan yunƙuri na gwamnati ba tukunna sai nasarorin sun ɗore.

"Za mu tabbatar da wannan nasarar ne idan muka ga ana yin irin wannan murnar a shekaru masu zuwa. Wannan ne zai tabbatar mana cewa kuɗaɗen da gwamnatin ta ce ta zuba sun yi amfani," kamar yadda ya bayyana.

Ayyukan ƙungiyoyin sa'ido

Farfesa Auwalu Halilu shugaban gamayyar kungiyoyi masu bibiya da tabbatar da ci gaban ilimi ne a jihar Kano, kuma ya faɗa wa BBC cewa rawar da ƙungiyoyin sa'ido suka taka ma ta taimaka.

"Da alama idan aka matsa wa gwamnati ta yi abin alkairi ana samun sakamako mai kyau," a cewarsa.

"Lokacin da aka samu faɗuwa mai yawa a jarabawar neman gurbi ta qualifying, mun yi ta rubuce-rubuce kan hakan."

Tallafin karatu

Dakta Bilyaminu ya ce jajircewar da gwamnatin Kano ta nuna wajen bai wa ɗalibai tallafin karatu ya taimaka wajen samun wannan nasara.

"Ɗalibai za su ji ƙwarin gwiwa wajen cin jarabawa saboda tunanin cewa za su samu tallafin ci gaba da karatun gaba da sakandare.

"Yaran da a baya talauci ke sakawa su naɗe hannunsu su koma gefe saboda tunanin ba za su iya ci gaba da karatu ba, wannan zai sa su yi ƙoƙari su ci jarabawar."

Ta yaya za a tabbatar da ɗorewar nasarorin?

Domin ganin nasarorin da aka samu sun ɗore, Dakta Bilyaminu Bello ya bayar da wasu shawarwari kamar haka:

  • Gwamnatin Kano ta ci gaba da ware kaso mai yawa ga fannin ilimi duk shekara
  • A dinga amfani da kuɗaɗen ta hanyar da ta dace, ba wajen gina azuzuwa ba kawai, har da bai wa malamai horo
  • Iyaye da jagororin al'umma su dinga saka ido kan yadda ake gudanar da makarantu
  • Ci gaba da shigar da ƙungiyoyi masu zaman kansu harkokin ilimi domin saka ido
  • Gwamnati ta ci gaba da bai wa ɗalibai tallafi a matakin gaba da sakandare, wanda zai iya saka wa ɗaliban gasa a tsakaninsu wajen neman nasara