Ko Ganduje da Barau sun raba gari ne?

Lokacin karatu: Minti 3

Alamu na nuna cewa an samu rabuwar kai tsakanin ƴan jam'iyyar APC a jihar Kano, inda ƴaƴan jam'iyyar suka karkasa mubaya'arsu ga jagororin jam'iyyar guda biyu, waɗanda ake hasashen kamar sun raba gari da juna a yanzu haka.

Yanzu haka dai wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa wasu na mubaya'a ga ɓangaren tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, inda wasu kuma suke nuna goyon bayansu ga ɓangaren mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da ma sauran magoya bayansa.

Alamun ɓarakar ya ƙara fitowa fili ne lokacin da aka yi wani taro a Kano, inda ba a ga Sanata Barau Jibrin da ƙaramin ministan gidaje ba.

Rahotanni na cewa saboda saɓani da rarrabuwar kai a jam'iyyar APC a jihar Kano, ta kafa wasu kwamitoci uku, waɗanda suke ci gaba da aikin tuntuɓar ƴaƴan jam'iyyar musamman waɗanda suke ji an ɓata musu a jam'iyyance, don ganin an rarrashe su an tafi tare.

Me ya hana Barau halartar taron?

BBC ta tutunɓi ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Yusuf Abdullahi Ata dangane da dalilin da ya hana su halartar taron na APC, sai ya ce.

"Ba wani rabe-rabe a APC a Kano domin shi wancan taro da ba a ga fuskata ba kuma ba a ga fuskar mai girma DSP ba, ai ba wani abu ba ne tunda za ka ga shi ma mai girma Abdullahi Ganduje da Murtala Garo duk ba su je ba, saboda ba sa Najeriya. Ni ma kuma na san ba zan iya samun taron ba saboda ayyuka na na ofis a can a Abuja.

Shi ya sa ma tun kwana ko biyar da muka yi wani taro da shi mai girma Abdullahi Abbas na ce masa ba zan samu damar zuwa ba, amma kuma duk abin da aka yi a wurin muna tare da shi. Haƙiƙa wasu na da bambancin ra'ayi amma kuma lokaci ne kawai zai nuna haka."

Ba mu da matsala - Abdullahi Abbas

Shugaban jam'iyyar APC, na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya ce babu wata ɓaraka a tsakaninsu inda ya ce wani uziri ne babba ya hana su zuwa taron.

"Ka san ita siyasa ai ba wani abu ba ne illa ka taka ni ka shure ni. Mutane ne masu tunani da buƙata daban-daban kuma duk wanda bai samu ba sai abin ya zama ka yi masa laifi.

''Idan ba ka yi sa'a ba ma shi kansa wanda ya samu sai ya ce ba haka yake so ba kuma an yi masa laifi'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa ''duk irin wannan ɓaraka muke neman mu ɗinɗinke domin uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya yadda za mu tunkari zaɓe''.

'Siyasa kasuwar buƙata'

To sai dai duk da hujjojin da ɓangarorin suka bayar na cewa babu wata matsala, masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin ko ba-ɗaɗe ko ba jima, sai an ji su a rana kasancewar dukkan alamomin tabbatuwar hakan sun bayyana.

Yusuf Musa malami ne a tsangayar kimiyyar siyasa a Jami'ar Baba-Ahmad, da ke Kano kuma masanin kimiyyar siyasa ya kuma ce buƙata ce za ta iya zama mafarin rabasu.

"Wato duk inda buƙata ta yi karo tsakanin ɗan siyasa da wani to yawanci an raba gari kenan'', in ji shi.

''Ita kuma buƙata a siyasance kala biyu ce, ko dai ta zamo ta mutum ɗaya da yake son ya cimma wannan buƙatar, ko kuma mutane da yawa kuma kowa a cikinsu na da tasa buƙatar amma kowa ba zai iya cimma ta shi kaɗai ba''.

Masanin siyasar ya ce to sai su haɗu domin cimma wannan buƙatar tasu ta gaba ɗaya.

Ya ƙara da cewa irin wannan buƙatar ce ke neman dara jam'iyyar gida biyu.

''Akwai ɓangaren Barau Jibrin kuma suna da buƙatunsu, idan ka duba muradan Barau Jibrin ba su wuce na neman takarar gwamnan Kano ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Malam Yusuf Musa ya kuma ce buƙatar sai ta yi karo da irin wannan buƙatar ta wasu da su ma burinsu na gwamnan ne.

''Saboda haka dole ne a samu saɓani da rabuwar kai a jam'iyyar. Idan dai har ba a iya zama an daidaita ba domin ganin kowa ya samu abin da yake so, idan kuma ba haka to lallai saɓani dole ne." In ji Malam Yusuf Musa.