Arsenal ta yi wa Saliba tayin sabon kwantiragi, Juventus na sa ido kan Lookman

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta yi wa dan wasan bayanta William Saliba tayin sabon kwantaragi, Benfica na son dan wasan Manchester City Bernardo Silva, yayin da Besiktas ke daf da kammala siyan Jota Silva daga Nottingham Forest.
Arsenal ta yi wa dan wasan bayanta William Saliba dan Faransa tayin sabon kwantaragi na tsawon shekaru biyar yayin da ake ci gaba da tattaunawa da dan wasan mai shekaru 24, wanda kwantiraginsa zai kare a shekara ta 2027. Real Madrid na sa ido kan halin da dan wasan ke ciki. (FootMercato)
Liverpool na da kwarin gwiwar cewa za su jagoranci fafatukar sayen dan wasan baya na Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, a bazara mai zuwa lokacin da kwantiraginsa da Crystal Palace zai kare, kuma suna neman fam miliyan 87 don sayen dan wasan Bayern Munich da Faransa Michael Olise, mai shekara 23. (Caught Offside)
Dan takarar shugabancin Benfica Joao Noronha Lopes na son siyan dan wasan gaban Manchester City Bernardo Silva a watan Janairu idan aka zabe shi kuma tuni ya tattauna da dan wasan Portugal mai shekaru 31, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa. (Record Portuguese)
Besiktas na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan gaban Portugal Jota Silva, mai shekara 26, daga Nottingham Forest. (Fabrizio Romano)
AEK Athens na son dauko dan wasan Faransa Anthony Martial, mai shekara 29, kuma ta yi tayin tsohon dan wasan na Manchester United ga kungiyoyin Mexico da dama. (FootMercato)
Martial zai tafi Monterrey domin a duba lafiyarsa bayan da AEK Athens ta ba shi izinin yin hakan. (Fabrizio Romano)
Juventus na sa ido kan dan wasan gaban Atalanta Ademola Lookman mai shekaru 27 a matsayin wanda zai maye gurbin Dusan Vlahovic dan kasar Serbia mai shekaru 25, wanda ake sa ran zai bar kungiyar ta Seria. Dan wasan Manchester United da Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24 ma na iya zaba zabin kungiyar. (Tuttosport)
Inter Milan ta ci gaba da neman dan wasan tsakiya na Faransa Manu Kone kuma burinsu na sayen dan wasan mai shekaru 24 zai iya taimaka wa Roma wajen samun kudin da za su yi amfani da su wajen cika ka'idar hada hadar a kasuwar musayan yan wasa. (Gazzetta dello Sport)
An yi wa dan wasan Chelsea dan kasar Portugal Dario Essugo, mai shekara 20 tiyata a cinyarsa kuma zai yi jinyar akalla makonni 12. (Telegraph)










