Arsenal ta tuntuɓi Eze, Manchester United na neman Watkins

Eberechi Eze

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta tattauna da wakilan ɗan wasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Eberechi Eze, mai shekara 27, wanda ke da farashin fam miliyan 67.5. (Guardian)

Ɗan wasan Aston Villa da Ingila Ollie Watkins, mai shekara 29, yana cikin jerin ƴan wasan da Manchester United ke nazari a kai idan ɗan ƙasar Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22, ya bar Old Trafford a bazara. (Athletic)

Bayern Munich ta sanya ɗan wasan gaban Liverpool da Colombia Luis Diaz, mai shekara 28, a jerin sunayen ƴan wasan da ta ke bibiya yayin da ta ke ci gaba da neman ɗan wasan gaba mai kai hari ta gefen hagu. (Sky Germany)

Fulham na shirin fara zawarcin ɗan wasan gaba na Genk da Najeriya Tolu Arokodare, mai shekara 24, wanda Manchester United da AC Milan ke sanya wa ido. (Sun)

Tottenham na son ɗaukar ɗan wasan gaban West Ham Mohammed Kudus, mai shekara 24, kuma ta na da ƙwarin gwiwar cewa za ta iya ƙulla yarjejeniya kan farashin ƙasa da fam miliyan 85. (Telegraph)

West Ham za ta saurari tayin kusan fam miliyan 60 kan Kudus, wanda ke jan hankalin Chelsea da Newcastle da Manchester United. (Guardian)

An bai wa ɗan wasan gaban Brazil Richarlison, mai shekara 28, damar barin Tottenham kuma ana tunanin zai nufi Turkiyya domin komawa Galatasaray. (Sun)

Chelsea na fatan samun kusan fam miliyan 35 idan ta yi nasarar cefanar da ɗan wasan gaban Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 27 a wannan bazarar. (Metro)

Crystal Palace na shirin gabatar da tayin fam miliyan 27 don ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Ingila Hayden Hackney, mai shekara 23, da ɗan wasan baya na Holland Rav van den Berg, mai shekara 20 daga Middlesbrough(Sun).

Manchester United na fafutukar ganin ta sallami Tyrell Malacia, mai shekara 25, bayan PSV Eindhoven ta ƙi amincewa da damar sayen ɗan wasan kan kwantiragin dindindin bayan zaman aro da ya yi a kulob ɗin. (Mirror)

Aston Villa na shirin sallamar matasa ƴan wasa Louie Barry da Kaine Kesler-Hayden, dukkansu masu shekara 22, zuwa ƙungiyoyin Hull da Coventry na gasar Championship. (Athletic)