'Dole a yi gyara a bangaren shari’a ta Nijeriya '

Masana shari'a a Najeriya sun yi tsokaci ne kan furucin da babban jojin Najeriya mai shari’a Olukayode Ariwoola ya yi inda ya mai da martani ga sukar da wasu `yan Najeriya suka yi dangane da wasu hukunce-hukuncen da kotunan kasar suke yankewa, musamman ma wadanda suka shafi zaben shugaban kasa da na gwamnoni.

Mai shari’a Olukayode Ariwoola ya ce hayaniyar da wasu da ya kira ‘yan tasha ke yi ba za ta sanyaya-gwiwar bangaren shari’a ba

Babban Jojin , ya yi furucin nasa ne a wajen kaddamar da sabuwar shekarar shari`a da nufin jifar tsuntsu biyu da dutse guda, wato ya mai da martani, sannan kuma ya karfafa gwiwar alkalan kasar da kuma bangaren shari`a baki daya, bayan caccaka da sukar da suka sha daga wasu `yan Najeriya.

Wasu ‘yan Nijeriya na zargin cewa wasu alkalan sun nuna son zuciya, tare da zama `yan koren gwamnati a wasu hukunce-hukuncen da suka yanke a kararrakin da suka shafi zaben shugaban kasa, da na gwamnoni da kuma `yan a majalisar dokoki.

Ya bukaci alkalai da su kasance masu himma da kamanta gaskiya a aikinsu na alkalanci, kuma kada su bari son zuciya daga wani bangaren al`umma ya yi tasiri a kan hukunce-hukuncen da suke yankewa, don haka kada su bari wata gada-gada ko hayaniyar `yan tasha ko wani gungun jama`a ta ruda su su koma suna maye gurbin doka da son zuciyar masu hayaniyar.

Sai dai wasu masana shari`a na ganin cewa bai kamata a yi fatali da sukar da wasu ke yi wa bangaren shari`ar ba

Barrister Umar Mainasara Kogo wanda Lauya ne a Abuja, ya shaida wa BBC cewa sukar da ake yi tamkar fitila ce da ke haska hanya:

"Gyra kayanka bai zama sauke mu raba ba, ya kamata ya kalli ta fuskar cewa akwai mutanen da suke ganin nauyin da suke sauke wa bai gamshe su ba. Saboda haka kamata ya yi ya ce za'a duba . Idan wani ya ce rawar da ka ke yi ba dai dai ba toh sai ayi kokari a bincika a gani"in ji shi.

Lauya ya ce sukar da ake yi wa bangaren shari`ar za ta yi wuyar shurewa, kasancewar ba kananan mutane ne kadai ke yin sukar ba, don haka akwai bukatar a kalle ta da idon basira:

"Ai ba wai lauoyoyi kawai ba , akwai alkalai da suka yi suka kan wannan, akwai daya daga cikin manayan alkalan kotun koli wanda ya yi retiya sati biyu ko uku da suka wuce, shi ma ya yi wannan suka"

"Akwai lokacin da su kansu alkalan harda shi babban joji na yanzu suka hada kai suka yi korafi suka kawo kara a kan wancan tsohon alkalin alkalan Najeruya wanda wannan ne ya sa a dole,shi ya zo ya rubuta takardar yin murabus" In ji shi.

A dan haka masanin ya ce ‘dole a yi gyra idan ana son kwaliya ta biya kudin sabulu’

A Najeriya dai bangaren shari`a kan shiga tsaka-mai-wuya tare da fama da irin wannan sukar a duk lokacin da aka shiga kakar shari`o`in zabe, inda ake zargin wasu alkalai da karbar toshiya ko kokarin faranta wa bangaren zartarwa, duk kuwa da cewa suna musantawa.

Kodayake a bangare guda kuma wasu masanan na ganin cewa wasu `yan siyasar su ne matsalar kasar sakamakon zargin da ake mu su na son zuciya wato idan suka kai kara, kotu ta ba su gaskiya a nan kotu tana adalcI amma idan shari`a ba ta yi mu su dadi to alkalai ne matsala.

Ke nan, a wannan lamari kusan kowane gauta já ne sai dai in ba a sa a shi a rana ba.