An tanadi hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk mutumin da ya ce mai neman jinsi ne a Uganda

Asalin hoton, AFP
Mutanen da ke bayyana kansu a matsayin masu neman jinsi ɗaya na cikin haɗarin fuskantar hukuncin ɗaurin rai da rai bayan da majalisar dokokin ƙasar ta amince da wani sabon ƙudiri na murƙushe ayyukan masu wannan halayya.
Ƙudirin ya ƙunshi hukuncin kisa ga waɗanda suka ci zarafin yara da kuma mutane masu rauni.
Wani mai fafutukar kare hakkin jama'a ya fada wa BBC cewa muhawarar da aka tafka kan kudirin ta haifar da fargabar kai karin hare-hare kan masu neman jinsi.
"Akwai barazana da yawa. Ana ta kiran mutane a yi musu barazana da cewa cewa ''idan ba ka ba ni kudi ba, zan bayar da rahoton cewa kai mai neman jinsi ne," in ji su.
An dai haramta ayyukan masu neman jinsi a Uganda amma wannan kudirin ya bijiro da wasu sabbin laifuka.
Fitowa ka bayyana kanka a matsayin mai neman jinsi ya zama laifi a karon farko.
Abokanai da yan uwa da al'ummar gari suna da damar kai karar duk mutumin da aka samu yana aikata wannan halayya ga hukumomi.
An amince da kudirin da ya samu goyon bayan yan majalisar dokokin Uganda.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Wannan dokar za ta haifar da kyama da tsangwama da wariya ga masu neman jinsi - har da wadanda ake zargin suna neman jinsi - sannan za ta haifar da cikas ga ayyukan kungiyoyin farar hula da ma'aikatan lafiya da shugabannin al'umma," in ji Tigere Chagutah, Daraktan Amnesty International na Gabashi da Kudancin Afirka.
Makwanni kafin muhawarar, nuna kyama ga masu wannan halayya ta fito fili a kafafen yada labarai, kamar yadda wani mai fafutuka da aka sakaya sunansa ya fada wa BBC.
"A wasu yankunan, jami'an tsaro na amfani da wannan dama ta tatsar kudi daga hannun mutanen da suke zargi da neman jinsi. Wasu iyalan ma suna kai rahoton ƴaƴansu ga ƴan sanda."
A yanzu ƙudirin zai je gaban Shugaba Yoweri Museveni wanda zai iya amfani da ƙarfin ikonsa - ko dai ya ƙi amince da ƙudurin ya zama doka wanda hakan zai kyautata alaƙarsa da ƙasashen yamma ko kuma ya amince da ƙudurin ya zama doka, abin da zai ɓata wa yamma.
Shugaban ya yi furuci da dama na nuna kyama ga masu neman jinsi a makwannin baya-bayan nan.
Ya kuma soki kasashen yamma saboda matsa lamba kan Uganda game da batun.
Wata mai rajin kare masu neman jinsi ta zargi gwamnati da amfani da kudirin wajen karkatar da hankalin jama'a daga gazawarta wajen magance damuwarsu kan matsin tattalin arziki.
"Suna ƙoƙarin rura wutar batun masu neman jinsi domin kawar da hankalin mutane daga abin da ya fi muhimmancin ga yan Uganda baki ɗaya.
Babu wani dalili da zai sa a samu wani kudiri da ya tanadi laifi kan masu neman jinsi," in ji Clare Byarugaba ta kungiyar Chapter Four Uganda.
Masu goyon bayan kudirin sun ce suna kokarin kare ƴaƴansu amma Ms Byarugba ta ce "Ko mutum ya kasance mai neman jinsi ko ba ya wannan halayya, ya kamata gwamnati da majalisar dokoki su samar da dokoki ko ma su aiwatar da dokokin da ake da su na kare dukkan yara - maza da mata daga cin zarafi ta lalata."
Me ƙudirin ya ce?
Ba a kai ga wallafa dokar ba a hukumance amma wasu bangarorin dokar da aka tattauna a kansu a majalisar sun hada da:
- Mutumin da aka samu da laifin safarar yara domin sanya su a dabi'ar neman jinsi zai fuskanci daurin rai da rai.
- Mutane ko cibiyoyi da ke goyon baya ko ma daukar nauyin ayyukan masu neman jinsi ko wallafawa, watsawa ko rarraba takardun ayyukansu suma za su fuskanci tuhuma ko hukuncin dauri.
- Kungiyoyin kafafen yada labarai da yan jarida da mawallafa za su fuskanci tuhuma ko dauri kan wallafa rahoto ko yada ayyukan da ke tallata su"
- Hukuncin kisa kan mai neman jinsin da ya yi lalata da yaro ko wani mai naƙasa ko masu rauni ko a yanayin da wanda mai neman jinsi ya yi lalata da shi ya gamu da cuta.
- Masu bayar da hayar gida suma za su iya fuskantar hukuncin dauri idan aka yi amfani da gidajensu wajen yin lalata da masu neman jinsi ko yara kanana.
Wata kwarya-kwaryar kungiyar yan majalisar dokokin Uganda a kwamitin da ke nazari kan kudirin sun bayyana sabanin ra'ayi kan kudirin.
Sun ce laifukan da kudirin ke neman a hukunta na kunshe a kundin shari'a na laifuka na kasar.
A 2014, kotun kundin tsarin mulkin Uganda ta soke wata dokar da ta tsaurara dokoki kan masu neman jinsi.
Dokar ta hada da haramta tallatawa ko daukar nauyin kungiyoyin masu neman jinsi da ayyukansu da kuma nanata cewa ya kamata a hukunta ayyukan masu wannan dabi'a da daurin rai da rai inda kuma kasashen yamma suka yi tur da lamarin.
Kotun ta zartar da hukuncin soke kudirin saboda majalisa ta amince da shi ne ba tare da cimma adadin yawan yan majalisar da ya kamata su yi zama ba.
Kasashen Afirka 30 ne suka haramta ayyukan masu neman jinsi inda mutane da dama ke mutunta dokokin addini da al'adu.










