Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kotun ƙolin Amurka ta amince da haramta amfani da TikTok
- Marubuci, Tom Gerken & Liv McMahon
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Technology reporters
- Lokacin karatu: Minti 3
Kotun ƙoli ta Amurka ta tabbatar da dokar haramta amfani da manhajar TikTok a ƙasar, sai dai idan kamfanin da ya mallaki manhajar, wato ByteDance, ya amince ya sayar da manhajar kafin 19 ga watan Janairu.
Kamfanin ByteDance, na China, ya ƙalubalanci dokar kuma ya musanta cewa yana saɓa dokar kare ƴancin tofa albarkacin baki kan masu amfani da manhajar su fiye da miliyan 170 a Amurka.
Sai dai Kotun ƙolin ya yi watsi da ƙalubalantar hukuncin da kamfanin ya yi, wanda hakan ke nufin wajibi ne manhajar TikTok ɗin ta samu mai sayenta da aka amince da shi domin samar da manhajar samfurin Amurka ko kuma ta fuskanci dakatarwa.
Hukumomi a Amurka da ƴan majalisu sun zargi kamfanin ByteDance da alaƙa da gwamnatin China kuma sun bayyana manhajar a matsayin barazana ga tsaron ƙasar.
Ko Shugaban ƙasa mai jiran gado Donald Trump zai iya samun hanyar da zai bi domin dakatar da dokar da ya ce yana adawa da ita?
Shugaban manhajar ta TikTok Shou Zi Chew zai yi fatan hakan- kafar yaɗa labarai ta CBS abokiyar hulɗar BBC a Amurka na ruwaito cewa zai halarci rantsar da Trump tare da tsofaffin shugabannin ƙasa da ƴan uwa a ranar 20 ga watan Janairu.
Kuma duk abin da ya faru da shafin sada zumuntan, wa zai amfana da rashin tabbas din da ya mamaye makomarsa?
Ko mutane za su iya amfani da TikTok bayan haramta shi?
Hanyar da ake ganin Amurka za ta haramta TikTok ita ce ta hanyar umurtar rumbun manhajoji, kamar 'Google play store' da 'Apple store' su cire manhajar a Amurka, ta yadda babu wanda zai iya sauke ta a wayarsa.
Hakan na nufin mutane ba za su iya bin hanyoyin da aka amince da su wajen shiga manhajar ba - duk da dai hakan kuma na nufin mutanen da suka riga suka sauke manhajar, za ta ci gaba da kasancewa a kan wayoyinsu.
Sai dai kuma waɗanda ke da manhajar a wayoyinsu kafin haramta ta ba za su iya sabunta ta ba, wanda hakan za zai sa manhajar ta lalace ta yadda ba za a iya amfani da ita ba.
Hakazalika, sabunta manhaja na taimakawa wajen toshe matsalar masu yin kutse a manhaja, a dalilin haka idan mutane ba za su iya sabunta ta ba, zai bai wa masu kutse damar kutsawa cikin wayoyin miliyoyin mutanen da ke amfani da manhajar.
Tabbas akwai hanyoyi da dama da masu amfani da manhajar za su bi domin tsallake shingen haramcin.
Tuni aka fara wallafa hoton bidiyo, wanda ya karaɗe shafin na TikTok da ke ilmantar da masu amfani da shi yadda za su yi amfani da VPN( virtual private network) - wata hanya da za ta bai wa mutum damar nuna kamar yana wani yankin ne na daban.
Haka nan kuma wayoyi da dama na bayar da damar sauya yankin da mutum yake a rumbun sauke manhajoji, wanda hakan ke nufin za ka iya ganin manhajojin da halas ne amfani da su a wasu ƙasashen - duk da cewa hakan na iya haifar da wasu matsalolin.
Haka nan kuma mutum zai iya ɗabbaƙa manhajoji da ya sauke kai-tsaye daga intanet - sai dai wannan zai iya kai wa ga karya yarjejeniyar haƙƙin mallaka - kuma hakan na da nasa haɗurran.
Sai dai kasancewar gwamnati na da masaniya kan hakan, ta buƙaci a haramta bin irin wannan tsarin, wanda hakan zai sanya mutane ba za su samu sauke manhajojin ba.
Saboda haka nan, idan har aka haramta amfani da TikTok ta wannan hanya, zai iya yiwuwa waɗanda suka nace kan sai sun yi amfani da ita za su iya, amma ba za ta yi musu daɗi kamar yadda suka saba ba.