Sojar Ukraine da ta zama bazawara kwana biyu da aurenta a filin yaƙi

    • Marubuci, Diana Kuryshko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Ukrainian

"Ya haɗa zoben aure ta hanyar amfani da gwangwani kuma ya nemi na aure shi. Tabbas na amince," a cewar Valeria Subotina.

"Masoyina ne na ƙwarai. Zobinanmu sun yi kyau sosai," in ji ta.

Ita da saurayinta Andriy Subotin mai shekara 34 kuma sajan a rundunar sojin Ukraine, suna shirin ɗaura aure a Mariupol kafin yaƙi ya ɓarke tsakanin ƙasar da Rasha.

Sun yi ta burin haɗa gagarumin biki tare da 'yan'uwa da abokan arziki.

Sai dai jim kaɗan bayan mamayen da Rasha, dakarun ƙasar sun wuce kai-tsaye zuw wannan gari mai tashar jiragen ruwa kuma mai muhimmanci a kudancin Ukraine kuma suka suka yi masa zobe cikin 'yan kwanaki.

Dakarun Rasha sun yi ta luguden wuta a kan birnin Mariupol, tituna suka dinga ci da wuta, babu abinci, babu wuta, babu ruwa, babu wata hanyar barin garin.

Garin ya shafe kusan wata uku a garƙame. An yi imanin cewa an kashe dubun dubatar fararen hula.

A gefe guda kuma, mazauna Mariupol da yawa sun nemi mafaka a ginin masana'antar ƙarafa ta Azovstal, inda ake da maɓoya sama da 30 waɗanda aka gina tun lokacin Tarayyar Soviet saboda tsoron harin nukiliya.

A nan ne kuma aka ɗaura wa Valeria aure - kuma ta zama bazawara a kwana biyu kacal.

‘Yunwa a kan iyaka’

Valeria mawaƙiya ce lokacin da Rasha ta afka wa Ukraine. Daga nan kuma sai ta zama kakakin Bataliyar Azov.

Yayin da Rasha ke tsananta hare-hare a kan Mariupol, dole aka tilasta wa dakarun Ukraine guduwa zuwa maɓoyar Azovstal tare da fararen hula.

Mashigar maɓoyar kamar rami take, kuma sai mutum ya yi ta yin ƙasa a kan matattakalar da suka lalace, in ji Valeria.

Mutane sun giggina madafa a cikin maɓoyar, inda ake sake girka abincin da aka ci aka rage.

Idan suka samu fulawa sai su kwaɓa ta don haɗa ket (cake).

"Muna kiran sa burodi amma dai ket ne kawai da ruwa. A haka muka rayu. Yunwa ce kawai a wurin," a cewar Valeria.

"Mun zama kamar wasu ɓeraye saboda duk abin da muka samu ci kawai muke. Mukan yi barci a ƙasa ko kuma a kan tsimma.

"A wani wurin babu haske ko kaɗan, amma sai da idanuwanmu suka saba har ma ya zama jiki. Amma maganar gaskiya rayuwarmu ta daban ce a lokacin."

A ranar 15 ga watan Afrilun 2022, an jefa wani babban bam a kan masana'antar, wanda ya raunata valeria.

"A cikin gawarwaki aka gano ni, kuma ni kaɗai ce a raye. Sa'a ce kawai, amma kuma bala'i ne me tsauri."

Bayan rauni da ta ji a ka saboda buguwa, Valeria ta shafe kwana takwas a asibitin da ke maɓoyar ta ƙarƙashin ƙasa tare da sauran marasa lafiya.

"Ba su iya samun kulawar da ta dace ba saboda babu isassun magunguna. Warin jini da kuma na ruɓewar abubuwa sun cika wurin," in ji ta.

Shi ma mijin Valeria mai suna Andriy a Azovstal yake. Jim kaɗan bayan raunukan da ta ji, nan take ya nemi aurenta kuma a wurin.

A ranar 5 ga watan Mayu, ma'auratan suka sanya hannu kan yarjejeniyar aure kuma suka aika wa iyayen Andriy kwafin takardun ta intanet a Kyiv, waɗanda daga baya suka je ofishin hukuma don ƙarƙare shirin.

Sun yi bikinsu a maɓoyar sanye da kakin soja a matsayin kwalliyar biki, da kuma zobinansu da aka yi da gwangwani.

Andriy ya yi alƙawarin zai saya mata zoben gaske idan aka gama yaƙin.

Amma an kashe shi ranar 7 ga watan Mayu a bakin daga.

Fursunonin yaƙi

A farkon watan Mayu, dubban 'yan Ukraine da suka ɓuya a ɗakunan ƙarƙashin ƙasar suka buƙaci a kwashe su bayan shafe kusan kwana 80.

Da farko an ƙyale fararen hula su fice. Sai kuma Rasha ta kama sojojin a matsayin fursunonin yaƙi.

Ana fatan za a sake su ne ta hanyar musayar fursunoni.

Amma bayan sama da shekara biyu, dubban dakarun Ukraine ciki har da na Bataliyar Azov da ake kallo a matsayin gwaraza - suna hannun Rasha.

Dakarun Ukraine kusan 3,000 Rasha ta saki a yarjejeniyar musaya tun bayan fara mamayen.

Ana tunanin har yanzu akwai sojoji kusan 10,000 a hannun Rasha.

Ita ma Valeria ta zauna a hannun Rasha wata 11. An azabtar da ita da kuma cin zarafinta, a cewarta. Ta wallafa wani littafi a kwanan nan kan zamanta a gidan yari.

Har yanzu gawar mijinta Azovstal na cikin masana'antar Azovstal.

"Rashawa sun kashe tare da lalata dukkan abubuwan da nake ƙauna - garina, abokaina, da mijina," in ji ta.