Majalisar Australia ta amince da dokar hana 'yan ƙasa da shekara 16 hawa soshiyal midiya

Hukumar kula da intanet ta ƙasar ce za ta aiwatar da haramcin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hukumar kula da intanet ta ƙasar ce za ta aiwatar da haramcin
    • Marubuci, Hannah Ritchie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Sydney
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ƙasar Australia za ta hana yara 'yan ƙasa da shekara 16 amfani da shafukan sada zumunta bayan majalaisar dattawan ƙasar ta amince da sabbin dokoki masu tsauri.

Dokar wadda ba za ta fara aiki ba har sai nan da wata 12, zai jawo cin tarar kamfanonin fasaha kuɗin ƙasar dala miliyan 50 (dalar Amurka miliyan 32) idan suka saɓa ta.

Firaminista Anthony Albanese ya ce ana buƙatar dokar ne domin kare matasa daga "cutuwa" a shafukan zumuntar, abin da iyaye da yawa suka daɗe suna faɗa.

Amma masu sukar lamarin na cewa akwai tambayoyin da babu amsarsu musamman game da yadda za a tabbatar da aiki da dokar - da tasirinta kan sirrin rayuwar mutane (privacy).

Ba wannan ne karon farko da ake yunƙurin hana yara amfani da dandalin zumuntar ba a duniya, amma dai ƙasar ce ta fi tsaurarawa kan shekarun yaran.

"Wannan matsala ce ta duniya baki ɗaya kuma muna son matasan Australia su ji daɗin yarintarsu," a cewar Albanese lokacin da yake ƙaddamar da ƙudirin dokar a majalisar wakilai a makon da ya gabata.

"Muna son iyaye su samu kwanciyar hankali."

Bayan majalisar dattawa ta amince da ita a ranar Alhamis, za a kai ƙudirin dokar majalisar wakilai - inda jam'iyya mai mulki ke da rinjaye kenan za ta samu wucewa - don ta amince da gyararrakin da aka yi kafin ta zama doka.

Dokar ba ta fayyace dandalin zumuntar da za a hana yaran hawa ba. Daga ministan sadarwa zai bayyana hakan, bayan ya tattauna da kwamashinan tsaron intanet - wanda zai lura da aiki da dokokin.

An keɓance dandalin wasannin game da na aika saƙonni, kuma ana sa ran waɗanda za a iya shiga ba tare da mutum na da shafi ba (account) kamar YouTube, za a ƙyale su.

Gwamnati ta ce za a dogara ne kan fasahohin da ke iya tantance shekarun mutum, kuma nan gaba za a gwada abubuwan. Alhakin dai zai dogara ne kan hukumar kula da ɓangaren domin tsara yadda za a yi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai kuma masu bincike a fannin intanet na cewa babu wani tabbas game da fasahohin nan - waɗanda suke dogara da zanen yatsun mutum kafin su tantance shekarun.

Haka nan, masu sukar lamarin na neman tabbacin yadda za a kare mutane daga yi musu kutse a kan sirrikansu. Sun kuma yi gargaɗi cewa za a iya saɓa wa dokar ta hanyar amfani da manhajojin VPN - waɗanda suke ɓoye wurin da mutum yake amfani da intanet.

Sai dai kuma ba za a hukunta duk yaran da suka lalubi hanyar da za ta ba su damar karya dokar ba.

Wata ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa akasarin iyaye a Australia na goyon bayan dokar.

"Tsawon lokaci, iyaye sun sha tsaka mai wuya kan ko dai su haƙura ko kuma su nema wa ɗansu wata na'ura da za ta ɗauke hankalinsa, ko kuma ya zama miskili kuma ya dinga ware kansa," kamar yadda Amy Friedlander, ɗaya daga cikin masu neman kafa dokar, ya faɗa wa BBC.

"Mun faɗa cikin taskun da babu wanda zai so ya auka cikinsa."

A shekarar da ta gabata, Faransa ta ƙaddamar da wata doka da za ta hana yara 'yan ƙasa da shekara 15 amfani da shafukan zumunta ba tare da sanin iyayensu ba, kodayake bincike ya nuna cewa kusan rabin yaran kan yi amfani da manhajar VPN wajen saɓa dokar.

Wani alƙalin gwamnatin tarayya a Amurka ya yi watsi da wata doka da jihar Utah ta ƙasar ta kafa, yana mai cewa ta saɓa wa tsarin mulki.

A kwanan nan ƙasar Norway ta ci alwashin bin sawun Ausralia, kuma a makon jiya ma sakataren kimiyya na Birtaniya ya ce suna duba yiwuwar kafa irin wannan dokar - amma daga baya ya ce "ba dai a yanzu ba".