An buɗe taron G20 a Afirka ta Kudu amma Amurka ba ta halarta ba

Asalin hoton, EPA
Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya shaida wa ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arziƙin duniya cewa mayar da hankali ga cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da martaba dokokin ƙasa da ƙasa su ne ƙashin bayan warware rikicin da duniya ke fama da shi.
Kalaman nasa na zuwa sakamakon damuwar da ake da ita cewa Amurka ta ƙaurace wa taron bayan da sakataren harkokin ƙasashen waje na Amurka, Marco Rubio ya ƙi halartar taro sannan shi ma ministan kuɗin ƙasar Scott Bessent ya ce ba zai halarci taron ministocin kuɗin ƙasashe ba mako mai zuwa.
Rubio ya ce ba zai iya "taimakon tsari ƙin Amurka" ba, inda shi kuma Bessent ya ce yana da wasu al'amuran da zai yi a Washington.
Afirka ta Kudu ce dai ƙasa ta farko daga nahiyar Afirka da ta fara jagorantar taron ƙasashen na G20, inda take cike da fatan bujuro da muradan ƙasashe masu tasowa.
Ƙungiyar ta G20 wanda ta ƙunshi ƙasashe 19 tare da tarayyar Afirka da Turai- sannan kuma ƙasashen ƙungiyar na da ƙarfin tattalin arziƙi fiye da kaso 80 na tattalin arziƙin duniya sannan kaso biyu bisa uku na yawan al'ummar duniya.
Ministocin harkokin waje na ƙasashen China da Rasha da Faransa da Burtaniya na daga cikin waɗanda ke halartar taron a birnin Johannesburg, inda ita kuma Amurka ke samun wakilcin mataimakin jakadanta na Afirka ta Kudun.
Da yake jawabin buɗe taro, shugaban Afirka ta Kudun, Cyril Ramaphoza ya ce "zamantakewar ƙasashen duniya da ke tangal-tangal" na fuskantar barazana daga rikici na rashin haƙuri da juna da sauyin yanayi.
"Babu matsaya ɗaya a tsakanin masu faɗa a-ji da suka haɗa da G20 dangane da yadda ya kamata su tunkari waɗannan matsaloli da ke da muhimmanci a duniya." In ji Ramaphoza.
"Abu ne mai girma a yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya, ƙulla cuɗanya da juna da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa su zama abubuwan da muke bai wa muhimmanci," Ya ƙara haske.
Ƙasar Afirka ta Kudu ce ke riƙe da kujerar shugabancin ƙungiyar ta G20 har zuwa watan Nuwamban 2025 lokacin da ake sa ran za ta miƙa ikon ga Amurka.
Alaƙa tsakanin Amurka da Afirka ta Kudu ta yi tsami tun bayan da shugaba Trump ya kama aiki a watan janairu, wani abu da ya janyo tambayoyi dangane da wace riba Afirka ta Kudun za ta iya samu daga jagorancin ƙungiyar ta G20.
Donald Trump dai ya yanke tallafi ga ƙasar inda ya zarge ta da "rashin gaskiya da aikata wasu abubuwan da suka saɓa da hali mai kyau" ga tsirarun farar fata da kuma kai Isra'ila kotun duniya kan zargin kisan kiyashi ga al'ummar Falasɗinawa a watan Disambab 2023.











