Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fugu: Rigar da aka ayyana ranar da ‘kowa‘ zai saka ta a Ghana
- Marubuci, Thomas Naadi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Accra
- Marubuci, Wycliffe Muia
- Lokacin karatu: Minti 5
Dandazon al'umma a faɗin Ghana sun fito domin saka kayan gargajiyar ƙasar mai gwanin sha'awa da aka fi sani da fugu, bayan da gwamnati ta ayyana ranar Laraba a matsayin "Ranar Rigar Fugu"
Matakin na zuwa ne bayan da aka yi wa shugaban ƙasar ta Ghana shaguɓe lokacin da ya saka rigar ya kuma kai ziyara Zambia a makon da ya gabata. Wasu sun ce rigar "ba ta da wani kyau", abin da ya janyo zazzafan martani a shafukan sada zumunta daga ƴan ƙasar ta Ghana.
Ministar yawon buɗe ido na Ghana Abla Dzifa Gomashie ya bayyana a ranar Talata cewa saka tufafin a kowane mako zai taimaka wajen fito da ƙimar ƙasar a idon duniya.
Ta ƙarfafa wa mutane wajen ganin an saka tufafin a kowane irin yanayi da kuma ɓangare, ganin cewa rigar tana da gwanin ban sha'awa.
Rigar ta fugu da aka fi sani da batakari, wani kayan gargajiya ne da aka ɗinka daga arewacin Ghana ta hanyar amfani da wasu auduga masu ƙarfi inda suka haɗu wajen samar da rigar mai kyau.
Sarakunan gargajiya na saka rigar a arewacin Ghana, har ma da mazauna ƙasar, kuma alama ce ta sarauta da kuma iko.
An fi alaƙanta tufafin na fugu da maza, waɗanda a wasu lokuta ke saka rigar tare da wani wando da kuma hula wanda kalarsu ya zo ɗaya, sai dai mata ma na sakawa - wani lokaci a matsayin dogon riga ko kuma karami.
Lokacin da Ghana ta zama ƙasa ta farko daga yankin kudu da hamadarar Sahara a Afirka da ta samu ƴancin kai a shekara ta 1957, wanda ya jagoranci ƙasar wajen samun ƴanci - Kwame Nkrumah - tare da wasu mutum biyar sun saka rigar fugu lokacin bikin murnar samun ƴancin kai daga Birtaniya.
Ba ya ga muhimmancin da tufafin yake da shi ga al'ada, Gomashie ta ce saka rigar a kowane mako zai taimaka "wajen samar da alfanun tattalin arziki da kuma na zamantakewa" ga ƙasar, musamman ma masu yin saka, masu zane, masu kayan ƙawa da kuma ƴan kasuwa.
"Gwamnati na fatan karɓar tufafin fugu baki-ɗaya zai karfafa haɗin-kai, samar da kuɗi a ɓangaren ƙirƙire-ƙirƙire da kuma inganta a'aldar Ghana," in ji ministar.
Bayan sanarwar, ƴan Ghana da dama sun bi kiran ministar, inda suka riƙa saka tufafin a launuka daban-daban a faɗin ƙasar.
Bismark Owusu Sarpong ya faɗa wa BBC a birnin Accra, cewa yana alfahari da saka tufafinsa na fugu mai launin shuɗi, fari da kuma baki, wanda ya ce ya samu a matsayin kyauta domin 'Fito da Ghana a duniya" - sannan ya ce wani abin daɗi da tufafin shi ne akwai sakewa mutum ba zai takuru ba.
Raymond Avenor wanda yake zama a Accra, yana cikin mutane da suka gamsu da cewa: "fugu tufafi ne mai sauki wajen sakawa.
"Da zarar ka ɗauke kawai sai sakawa. Ba sai ka goge shi ba, ba mu cika wanke shi ba," kamar yadda ma'aikacin gwamnatin ya shaida wa BBC, sanye da rigarsa mai launin shuɗi.
"A fahimtata al'ummar yankin arewacin Ghana ne ke saka tufafin da kuma fito da shi, a matsayin alama ta sarauta. Ina jin daɗi idan na saka rigar."
Ga mutane irinsu Andrews Tetteh Zutah wanda yake da sama da riguna bakwai, ya ce bai kamata a saka Laraba kaɗai a matsayin "Ranar Fugu" ba.
"Ina son samun ƙarin kwanaki," a cewar Andrews wanda ke aiki a Accra sanye da rigarsa mai launin jajayen layuka da kuma bakar hula.
"Zan so a ce za a bar ni in saka rigar a kowace rana zuwa aiki amma saboda yanayi na aiki ba na iya saka shi kullum. A ɓangarena, yana ɗaya daga cikin tufafi na fi so."
Hankali dai ya karkata zuwa ga masu ɗinka fugu har ma da masu sayarwa.
Elijah Suleman Musah, wani kamfanin buga fugu, ya ce kasuwa na haɓaka - inda ya ƙara da cewa ya samu sakonni da dama musamman daga manyan mawaƙan ƙasar waɗanda ke son a yi musu rigar irinsu Okyeame Kwame da Kwabena Kwabena.
"Na samu kiraye-kiraye daga wurare da dama a ciki da wajen Ghana. Bai daɗe ba na haɗu da wata wadda ta ce ƴan Zambia sun kirata kuma suna son a buga musu fugu don haka tana son a sama mata," kamar yadda ya faɗa wa BBC.
Batun rigar mai gwanin ban sha'awa ya karaɗe shafukan sada zumunta na tsawon kwanaki bayan yi wa juna ba'a tsakanin ƴan Ghana da Zambiya.
Wannan ya farfaɗo da batun al'ada a shafukan sada zumunta, inda ƴan Ghana ke koƙarin ayyana Juma'a a matsayin "Ranar Fugu" domin nuna tufafin. Gwamnatin da ta gabata ta keɓe ranakun Juma'a a matsayin ranar ƙarfafawa mutane su saka tufafin gargajiya.
Muhawarar ta jawo ƴan Ghana, ciki har da ƴan majalisa shiga shafukan sada zumunta suna alfahari da saka fugu, yayin da aka nuna ƴan Zambia su ma sun fito sanye da nasu tufafin da aka fi sani da siziba.
Muhawarar ta janyo hankalin shugaban Zambia, Hakainde Hichilema, sanar da cewa ƙasarsa za ta sayo fugu daga Ghana.
Shugaba Mahama ya ce shi ma yana duba yiwuwar kai tufafin da dama zuwa Zambia.
Yayin da yake nanata muhimmancin fugu a ɓangaren al'ada da kuma siyasa, Mahama ya yaba wa Nkrumah kan yadda ya saka tufafin a shekara ta 1957 kuma ya ce shi ma a baya bayan-nan ya saka rigar zuwa wani taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sauran shugabannin Ghana, ciki har da Nana Akufo-Addo, John Kufuor da kuma Jerry John Rawlings, sun sha saka rigar da kuma ƙarfafa muhimmancinta ga al'umma.