Abin da ƴan Afirka mazauna Amurka ke son gani a zaɓen ƙasar

Annette Njau

Asalin hoton, Annette Njau

Bayanan hoto, Annette Njau na ganin kudurin ƴan ci-rani na Amurka ne batun da ya kankane zaɓen 2024
    • Marubuci, Chimezie Ucheagbo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 7

“Abin da ke akwai shi ne kasancewar mu ƴan ci-rani a nan, domin yin kasuwanci da kuma kaɗa kuri'a a nan," in ji Annette Njau, wata ƴar asalin Saliyo da ke aikin lauya da kuma kasuwanci a Texas.

Mambobin ƙungiyar ƴan Afirka mazauna Texas su 300,000, na aiki tukuru wajen ganin al'ummominsu sun fito kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa na Amurka da za a yi ranar 5 ga watan Nuwamba.

"Duk da cewa ban san yadda kasuwancina zai kasance ba karkashin kowacce gwamnati, zan tabbatar da cewa kasuwancina ya ɗore," in ji Njau.

"Akwai rarrabuwar kawuna da saɓani dangane da batun launin fata da kuma ƴan ci-rani. Wannan na shafar al'ummomin mu matuka," a cewar Nneka Achapu, wani ɗan asalin Najeriya mazaunin Amurka kuma wanda ya kirkiro da kwamitin hulɗa da jama'a na Afrika, AfriPac.

Texas ta kasance jihar da jam'iyyar Republican ke samun nasara tsawon shekaru tun lokacin zamanin Bush. Sai dai a 2020, ɗan takarar Republican Donald Trump ya samu nasara kan Joe Biden a jihar da maki da bai fi kashi 6.5 ba, wanda shi ne mafi ƙankanta tsakanin jam'iyyun tun 1966.

Yanzu, abubuwa na sauyawa a Texas. Ƴan Afrika mazauna jihar shi ne mafi girma a Amurka, waɗanda suka haɗa da Ƴan Najeriya da Ghana da Kenya da kuma Ethiopia da sauransu.

Duk da cewa al'ummomin Afrika a jihar suna ƙaruwa, mutane da yawa sun ce gwamnati ta yi watsi da su.

"A matsayina na matashiya, abin da muka fi damuwa a kai shi ne ta yadda zan rayu, ta yadda zan tashi da safe da kuɗaɗe a aljihuna da zan yi buƙatu, da kuma abin da zan adana domin gaba," a cewar Udeme Anthony, ƴar Najeriya mazauniyar Amurka kuma mai riƙe da kambun Miss Nigeria USA a yanzu.

'Yan Afirka mazauna Texas su ne al'umma mafi girma a Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan Afirka mazauna Texas su ne al'umma mafi girma a Amurka

Rayuwar ɗan Afirka a Texas

Houston wadda ake wa lakabi da "Karamar Najeriya" gida ne ga ɗimbin ƴan Najeriya da ke zaune a Amurka - waɗanda suka kai mutum sama da 60,000.

Yadda aka tsara titunan birnin za ka ɗauka Legas ne. Akwai ƴan Najeriya da suka mallaki wuraren kasuwanci da kuma cibiyoyin al'adu da ke nuna salon rayuwar ɗan Najeriya a Texas.

Za a iya ganin mutane sanye da tufafin Afrika da kuma tattaunawa da harsunan nahiyar ko kuma ana iya jin wakokin salon Afrobeat na tashi a kasuwanni ko kantunan sayar da abinci da ke kusa.

Ivy Okoro

Asalin hoton, Ivy Okoro

Bayanan hoto, Mutane irinsu Ivy Okoro na cikin matasa masu zaɓe a Texas da ke da burika na daban
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƴan ci-ranin Afrika sun bayar da gagarumar gudummawa a cigaban tattalin arzikin Texas ta ɓangarori da dama kamar kafa wuraren kasuwanci, zuba jari da lafiya da kuma ɓangaren iskar gas.

A yawan lokuta ƙananan masana'antu mallakin ƴan Afrika na tafiya da irin salon al'adar ƴan Afrika da kuma rayuwa a Texas ta hanyar abinci da tufafi da kuma sauran kayayyaki.

"Addinivma yana da muhimmanci ga rayuwar mu," a cewar ɗan Najeriya mazaunin Texas Ivy Okoro.

"Muna ɗaukar bauta da gaske ko da kuwaa kai Kirista ne ko Musulmi."

Yi wa masu zaɓe rajista da gudanar da tarukan wayar da kai na ci gaba da gudana a faɗin jihar a cikin majami'u na Afrika da wuraren jama'a da kuma wuraren kasuwanci, don janyo hankalin mutane kan muhimmancin zaɓe.

Duk da cewa ana samun ƙaruwar adadin 'yan Afirka da ke zaune a jihar, hulɗa tsakanin al'umma ta yi kaɗan idan aka duba tarihi. Binciken Yawan Jama'a na Hukumar Kididdiga ta Amurka kan zaɓe da rajista, ya ba da rahoton cewa kusan kashi 61 na Afrika sun kaɗa kuri'a a Texas.

Yayin da wannan adadi ya ƙunshi duka Amurkawa ƴan asalin Afrika da kuma ƴan ci-ranin Afrika, hakan na nuna yadda ake dama a na su a zaɓe a jihar.

Maazi Okoro - mahaifin Ivy - ɗan asalin Najeriya wanda ya isa Amurka a 1977.

Ya ce shi da sauran 'yan Afirka sun mayar da hankali kan samun ilimi don su koma ƙasarsu ta asali don ba da gudummawa ga gina ƙasa. Ya ce ba su da sha'awar shiga cikin harkokin jama'a a Amurka.

"Muna alfahari da ƙasashenmu wanda ba ma son wani abu da zai saka mu ci gaba da zama a nan balle mu shiga cikin tsarin dimokraɗiyyar Amurka," in ji shi.

Amma waɗannan ƴan Afrika sun zauna na tsawon gomman shekaru a Amurka kuma sun kafa wuraren kasuwanci da kuma samun iyalai,

“Saboda ba mu shiga harkokin jama'a ba, ba mu samar da abin koyi ga matasanmu su gani su shiga harkar siyasa ba amma ya kamata hakan ya canza! Muna buƙatar mu kara ƙaimi a harkokin siyasar ƙasar nan,” in ji Okoro.

"Yanzu muna da 'ya'ya ƴan asalin Najeriya waɗanda ba za su taɓa komawa gida ba, amma za su iya samar da muryar da za ta shafi Afirka gaba ɗaya idan sun shiga."

Nneka Achapu says the lack of any African-born representatives from Texas in state or federal office leaves many in the community feeling disconnected

Asalin hoton, Nneka Achapu

Bayanan hoto, Nneka Achapu ta ce rarrabuwar kai da kuma saɓani da ya dabaibaye batun ƴan ci-rani na shafar al'ummomin da ke zaune a Texas

‘Waɗanda za su yanke hukunci’

Batun kudurin ƴan ci-rani ne ya mamaye zaɓen 2024 ga yawancin ƴan ci-ranin Afirka, kuma lamari ne mai jan hankali.

Mutane da yawa suna ganin tsallakewa tsarin zai yi wuya ba saboda tsawon lokaci na jiran biza, ƙarancin damarmaki ga masu neman mafaka da kuma tsauraran matakai kan samun shaidar zama ɗan ƙasar.

Wasu na tambayar cewa ko tsarin na nuna wani ajandar siyasa.

"Shin nuna wariya ga baƙaƙen fata na shafar mutanen da ke son shiga ƙasar musamman rashin samun biza?" In ji Nneka Achapu, wadda ta kafa AfricaPac.

"Abin da mazauna Afirka ke nema daga kowace gwamnati, shi ne mafi kyawun manufofi - waɗanda ke ba da fifiko ba ga Afirka kawai ba har ma da iyalai Amurkawa," in ji ta.

Achapu na son ganin ingantattun tsare-tsare game da haɗin kan iyali, izinin aiki da kora waɗanda za su ba da damar ga iyalai na Afirka su zauna da samun aikin yi a Amurka.

Maazi Okoro na son a ƙara hulɗa tsakanin jama'a musamman daga wajen matasan ƙungiyar ƴan Najeriya mazauna waje

Asalin hoton, Maazi Okoro

Bayanan hoto, Maazi Okoro na son a ƙara hulɗa tsakanin jama'a musamman daga wajen matasan ƙungiyar ƴan Najeriya mazauna waje

Idan muka ajiye manufofin a gefe, batun ayyana ƴan ci-rani a matsayin masu aikata laifuka a lokacin yaƙin neman zaɓe ya kasance abin damuwa ga 'yan Afirka da ke zaune a Amurka.

Kalaman wariyar launin fata da 'yan siyasa ke amfani da su sun janyo hukunci masu tsauri kan bakin haure, musamman waɗanda suka fito daga Afirka da sauran yankuna masu tasowa - suna kwatnata su da a matsayin waɗanda ba su da kyau.

"Ba daidai ba ne ɗan takarar shugaban ƙasa a wata babbar ƙasa kamar Amurka ya yi zagi, izgili, da kuma wulakanci tare da yin amfani da kalaman ɓatanci wajen siffanta wasu mutane," in ji Dr Christian Ulasi, Farfesa a Jami'ar Kudancin Texas.

"Ba daidai bane ware ko siffanta wata al'umma a matsayin masu laifi kuma a matsayin cutar da ba ta da kyau ga ƙasa, ya kamata a yi hukunci a kan hakan, mutane su hukunta wannan ɗan takara idan sun je rumfar zaɓe," in ji shi.

Annette Njau, wata lauya 'yar ƙasar Saliyo kuma ƴar kasuwa ta ce: "Hakika akwai waɗanda za su yanke hukunci a wannan zaɓen."

“Ni bakin haure ne; Na zo nan da iyalina tun ina yaro. Na je makaranta, na je makarantar lauya na kuma biya haraji. Don haka, ga wani ya yi amfani da shige da fice a matsayin maƙamin siyasa, bai mutunta ƴancin ɗan'adam ba,” inji ta.

"Ina ganin kamar wannan zaɓen zai kasance kan al'umma, kuma al'umma ba ta buƙatar mutanen da za su ci gaba da raba kan mu da kuma lalata mu ba."

Duk da cewa al'ummomin Afrika na ɗaya daga cikin al'ummomi masu ƙaruwa a Texas, mutane da yawa na cewa gwamnati ta yi watsi da su

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duk da cewa al'ummomin Afrika na ɗaya daga cikin al'ummomi masu ƙaruwa a Texas, mutane da yawa na cewa gwamnati ta yi watsi da su

Amurka a idon duniya

Har ila yau, manufofin harkokin wajen Amurka na da matukar damuwa ga ƴan ci-ranin Afrika.

Zuwa shekarar 2021, akwai kusan ƴan ci-ranin Afirka miliyan 2.4 da ke zaune a Amurka, da yawa har yanzu suna da alaƙa da ƙasashensu ta hanyar iyalai da zamantakewa, da kuma tattalin arziki, a cewar Cibiyar Kula da Hijira.

A gare su, wanzar da kyakkyawar alaƙar Amurka da Afirka abu ne na kashin kai. Wasu na da shaidar ƙasa biyu domin samun damar komawa gida akai-akai.

"A matsayina na ɗan Afrika a Amurka da ke yin kasuwanci a nan, ina so in ga gwamnati da za ta bunƙasa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, wadda za ta yaba da Afirka da kuma karfafa haɗin gwiwa," in ji Maazi Okoro.

A cikin 2022, kuɗaɗen da ake turawa zuwa yankin kudu da hamadar saharar Afrika sun kai kusan dala biliyan 53, inda wani kaso mai tsoka ya fito daga ƴan ci-ranin Afirka a Amurka, a cewar Bankin Duniya.

Ga matashiya kamar Udeme Anthony, nasarar da tattalin arzikin Amurka zai samu shi zai nuna yadda za ta kaɗa kuri'a.

"Idan wasu mutane ne ke jagorantar mu waɗanda ba lallai ba ne su damu idan za mu iya tsira ko adana ƴan kuɗi ba ga iyalanmu, zai yi mana wahala mu aika kuɗi ga mutanenmu da ke can gida," in ji ta. .

Masu kaɗa kuri'a ƴan Afirka na kuma neman 'yan takara da za su ba da fifiko mai inganci, mai mutuntawa.

Haɗin gwiwar da za ta iya amfanar 'yan Afirka da kuma Amurka.

“Mutane ne da Amurka za ta iya amfani da su a matsayin kadara don ciyar da dangantakar Amurka da Afirka. Bai kamata a yi mana wani irin kallo ba, ” in ji Nneka Achapu.

Yayin da Texas ba ta da 'yan siyasa haifaffu daga Afirka, ana samun ƙaruwar wayar da kan jama'a harkokin siyasa na fara wa ne daga hulɗa da jama'a.

Ƙungiyoyi irin su AfriPac na Achapu, na jagorantar ƙoƙarin ilmantarwa da ƙarfafa al'ummomin su don samun shiga.

"Ba koyaushe wakilci ke kawo sauyi ba, amma samun jajirtattu na taimakawa. Muna buƙatar kasancewa a cikin tsarin siyasa," in ji Achapu.