An gayyaci matar da ta yayyaga fasfo ɗin mijinta a filin jirgin sama na Legas

Hukumar kula da shige da fice a Najeriya ta gayyaci wata mata domin amsa tambayoyi bayan an gan ta a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta tana yayyaga fasfo ɗin mijinta a filin jirgin sama na Legas.
Matar mai suna Favour Igiebor, an gan ta a cikin bidiyon tana yi masa ihu tare da watsar da takardun fasfo ɗin a ƙasa.
Ta dawo daga Turai ne tare da mijinta da 'ya'yanta, wadanda suka sauka a filin jirgin sama na Murtala Mohammed, inda lamarin ya faru a gaban waɗansu fasinjojin.
"Na kekketa," a cewarta.
Hukumomi a cikin sanarwar sun ce suna sake duba lamarin.
"Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta soma gudanar da bincike kan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda wata fasinja ta yayyaga fasfo ɗin mijinta a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas," in ji wata sanarwa daga hukumar.
"Mun gano matar, sunanta Mrs. Favour Igiebor," a cewar hukumar.
Hukumomin ƙasar sun ce laifi ne a kekketa fasfo ɗin ƙasar kuma duk wanda aka kama da laifi zai iya shafe shekara guda a gidan yari.

Bayan da bidiyon ya karaɗe shafukan sada zumunta, mutane sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu a kai, lLamarin da ya sa Mrs Igiebor ta fitar da wani bidiyo tana bayyana cewa tana shan wahala a zamantakewarsu ta aure da mijin nata.
"Duba idona - na sha kuka sosai. Mutane da yawa na ta tsokaci a kai a soshiyal midiya, ba su san halin da nake ciki ba," a cewarta.
"Sai ku tambaye ni me ke faruwa - ba wai ku duba abin da na yi kadai ba. Ina da hujjojina. Ina fuskantar abubuwa a cikin iyalina. Na sha wahala a kansa."
Ta ce tun a Turai ta so kekketa fasfo ɗin amma sai ta yanke shawarar hakan zai jawo masa matsala sosai.
A cikin bidiyon, an ji wani mutum na cewa tun a cikin jirgi suke faɗa tsakaninsu (mata da miji).
Waɗansu mutane a cikin bidiyon sun yi ta bai wa mijin haƙuri suna ce masa ya kawar da kai.
Idan har aka gurfatanar da ita a kotu, za ta kasance mutum na farko a Najeriya da za ta fuskanci shari'a a kan lalata fasfo ɗin ƙasar.










