Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Isra'ila da Hamas na gab da tsagaita wuta'
- Marubuci, Yolande Knell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
- Marubuci, Rushdi Aboualouf
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gaza correspondent, Istanbul
- Lokacin karatu: Minti 4
Bayan kwashe watanni ana rabuwa baran-baran, akwai alamu da ke nuna cewa Isra'ila da Hamas ka iya cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin mutanen da Hamas ɗin ta yi garkuwa da su nan ba da jimawa ba.
Wani babban jami'i na Falasɗinawa da ke cikin masu shiga tsakani ya shaida wa BBC cewa tattaunawar na a "matakin ƙarshe".
Ministan tsaro na Isra'ila, Israel Katz shi ma ya ce ana dab da cimma yarjejeniya fiye da kowane lokaci.
A makonnnin da suka gabata, Amurka da Qatar da Masar sun koma shiga tsakani kuma rahotanni na nuna akwai alamu masu ƙarfi a wannan karo cewa dukkannin ɓangarorin biyu sun nuna aniyar kawo ƙarshen yaƙin na watanni 14.
Wata tawagar Isra'ila da aka bayyana da "wadda ke kan matakin aiki" yanzu haka tana birnin Doha na ƙasar Qatar a daidai lokacin da ake fuskantar matsalar hulɗar jakadanci a yankin.
Jami'in na Falasɗinawa ya fayyace tsarin tattaunawar mai mataki guda uku wanda zai tabbatar da sakin fararen hula da sojoji mata da Hamas ke garkuwa da su a kwanaki 45 na farko na tattaunawar, sannan su kuma dakarun Isra'ila su fice daga tsakiyar biranen Falasɗinawa da titunan bakin ruwa da kuma wurare masu muhimmanci da ke kan iyakarsu da Masar.
Za a samu wani tsari ga ƴan Gaza da yaƙin ya ɗaiɗaita su koma matsugunansu da ke arewa, kamar yadda jami'in ya shaida.
Mataki na biyu kuma na yarjejeniyar zai tabbatar da cewa an saki ragowar mutanen da Hamas ke garkuwa da su sannan kuma dakarun Isra'ila za su fice kafin kai wa ga mataki na uku na yarjejeniyar wanda zai kawo ƙarshen yaƙin.
Daga cikin mutane 96 da Hamas ke ci gaba da garkuwa da su a Gaza, ana tsammanin mutum 62 suna raye.
Tsarin ya dogara ne a kan yarjejeniyar da shugaban Amurka, Joe Biden ya tsara a ranar 31 ga watan Mayu kuma rahotanni daga dukkan ɓangarori na nuna cewa akwai wasu sassan yarjejeniyar da ake buƙatar a warware su.
Waɗansu jerin tattaunawar da aka yi a tsakiyar watan Oktoba sun gaza samar da matsaya, inda Hamas ta yi watsi da daftarin yarjejeniyar tsagaita wutar ta wucin-gadi.
Mai magana da yawun fadar ma'aikatar tsaro ta Isra'ila, ya ce Katz ya shaida wa mambobin kwamitin ƙasashen waje na majalisar dokokin Isra'ila ranar Litinin cewa "Ba mu taɓa zuwa kaiwa gab da cimma yarjejeniya kan sakin waɗanda ake garkuwa da su ba kamar yanzu tun bayan jerin tattaunawar da aka yi a baya," yana nuni da musayar waɗanda ake garkuwar da su da fursunonin ƴan Falasɗinu da Isra'ila ke tsare da su a watan Nuwamban 2023.
Kuma ya rubuta a shafinsa na X cewa: Matsayina kan Gaza a bayyane yake. Bayan mun samu galaba kan dakaru da gwamnatin Hamas a gaza, Isra'ila za ta kula da tsaron Gaza bisa cikakken ƴanci, " yana mai kwatanta wannan yanayi a gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
"Ba za mu bar kowane irin aikin ƴan ta'adda da zai cutar da garuruwan Isra'ila da ma Isara'ilawa daga Gaza ba. Ba za mu amince da sake faruwar irin abin da ya faru a ranar 7 ga watan Oktoba ba."
Akwai yiwuwar masu shiga tsakani sun yi wa irin waɗannan kalamai kallon masu matsala wajen shawo kan ƙungiyar Hamas. To sai dai a Isra'ila kuma suna kallon kalaman ne da masu nuna goyon baya ga masu tsattsauran ra'ayi da ke gwamnatin Netanyahu waɗanda suka yi gargaɗinn cewa ba za su amince da abin da suka bayyana da yarjejeniya mai cike da "ganganci" da Gaza.
Wata jaridar ƙasar Qatar al-Araby al-Jadeed ta kuma rawaito cewa ƙungiyar Hamas ta miƙa jerin sunayen ƴan Isra'ilar da ba su da lafiya da tsofaffin da ta yi garkuwa da su tare da ƴan Amurka ga jami'an sirri na ƙasar Masar. Jaridar ta kuma ce akwai sunayen fursunonin Falasɗinawa da Hamas ɗin ke neman a sakar mata su duka a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wutar.
A farkon yaƙin dai, Isra'ila ta sha alwashin wargaza gwamnati da dakarun Hamas.
Fiye da Falasɗinawa 45,000 aka kashe kawo yanzu, kamar yadda ma'aikatar Lafiyar Gaza ta ce kuma Majalisar Dinkin Duniya tana gaskata alƙaluman.
Mafi yawan al'ummar Gaza miliyan 2.3 sun ɗaiɗaita sannan kuma an lalata muhallai, abin da ya tilasta yankin neman tallafi ga masu buƙata sakamakon matsananciyar yunwa da ake fama da ita a Gazar.
Nasarar da Donald Trump ya samu a watan Nuwamba a zaɓen shugaban ƙasar Amurka ya ƙara bai wa ƙoƙarin samar da tsagaita wutar ƙarfi.
A wani taron manema labarai ranar Litinin, ya sake yin gargaɗi cewa ya zama dole a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta kafin ya hau karagar mulki, inda ya ƙara da cewa idan kuma ba haka ba to " al'amarin ba zai yi daɗi ba."