Me ya sa aka tsagaita wuta a Lebanon ban da Gaza?

Lokacin karatu: Minti 5

Gwamnatin Isra'ila ta sanar da tsagaita wuta a yaƙinta da Hezbollah a Lebanon. Isra'ila ta kasance tana gwabza yaƙi biyu ne tun bayan 7 ga watan Oktoban bara da na Hezbollah da na Hamas.

Yadda yaƙin ya ta'azzara ne ya sa ƴansiyasa da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum suka bayyan fargabarsu ta jefa yankin gabas ta tsakiya baki ɗayanta a cikin yaƙi.

Mun tambaya wakilan BBC daga yankin a kan me ya sa aka sanar da tsagaita wuta a Lebanon, amma ba a yi hakan a Gaza ba, kuma yaya aka yi har aka kai ga wannan matsaya?

Carine Torbey, wakiliyar BBC Arabic a Beirut

Akwai bambancin yadda Isra'ila take kallon yaƙin da take yi da Hamas da na Hezbollah a Lebanon. Ita Gaza tana ƙarƙashin mamayarta ne, ita kuma Lebanon ƙasa ce mai zaman kanta - duk da cewa ita ma ta taɓa kasancewa ƙarƙashin mamayar Isra'ilar har zuwa lokacin da Hezbollah da wasu ƙungiyoyin suka ƙwace ta.

Duk da kayan yaƙin sama da take da shi, Isra'ila ta daɗe tana fama da tsaikon kutsawa Lebanon ta ƙasa. Bayan kimanin wata biyu ana gwabza yaƙin, ta kasa ƙwace iko da wasu garuruwa a kudancin, haka kuma ta kasa hana Hezbollah jefa mata rokoki zuwa arewacin ƙasarta.

Hezbollah ta kuma samu nasarar faɗaɗa hare-harenta zuwa cikin ƙasar Isra'ila, inda ta kawo tsaiko a yanayin yadda ake tafiyar da rayuwar yau da kullum a wasu birane.

Kuma wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ita kanta rundunar sojin ƙasan Isra'ila ta rasa dakarunta a kudancin Lebanon.

Haka kuma Isra'ila ba ta samu nasarar tabbatar da abin da take so ba, musamman na mayar da ƴan kasarta da suka bar muhallansu a arewaci. Wannan zai iya zama ɗaya daga cikin manyan dalilan da za su firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya amince da tsagaita wuta da Hezbollah.

Haka kuma sojojin Isra'ila sun fara gajiya, ga kuma yanayin da siyasa da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

Dr Leila Nicolas, mawallafin littafin Global and Regional Strategic in the Middle East ya ce, "Isra'ila ba ta da wani tabbataccen tsari a game da Gaza."

Amma a ɓangaren yaƙi da Hezbollah kuwa, dama akwai yarjejeniyar.

Har yanzu ba a fayyace asalin abin da yarjejeniyar ta ƙunsa ba. Wannan ya nuna cewa kowane ɓangare zai sake duba buƙatunsa domin ganin yarjejeniyar ta tabbata. Isra'ila ta kasa hana Hezbollah kataɓus da kuma tabbatar da komawar mutanen ƙasar muhallansu da ke arewacin ƙasar.

Hezbollah, wadda ta sha fama da matsaloli saboda rashin shugabanninta, ita ma da alama ta janye daga matakin da ta ɗauka a farko cewa ba za ta daina yaƙin ba, har sai an Isra'ila ta daina luguden wuta a Gaza.

"Akwai kuma alamu Iran (wadda ke ba Hezbollah tallafi) ba ta so Hezbollah ta cigaba da jan yaƙin, har ta gaji ba," in ji Dr Nicolas.

Adnan El-Bursh, wakilin BBC Arabic a Gaza

Wasu a Gaza suna ganin Hezbollah ta shiga yarjejeniyar ce domin yin watsi da tsarin haɗakarta da Hamas wajen yaƙi da Isra'ila, wanda aka tsara a farkon yaƙin domin samun haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin da suke adawa da Isra'ila, ciki har da ƙungiyoyin Gaza da Houthi a Yemen da wasu ƙananan ƙunyiyoyi a Iraq.

Babban abin da ya sa aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, ba a Gaza ba, shi ne Hezbollah ta bar batun tattauna yarjejeniyar a hannun gwamnatin Lebanon ne, ita kuma Hamas tana jagorantar nata tattaunawar a Gaza, kuma ta ƙi amincewa ta sanya hukumomin yankin Falasɗinawa domin su wakilce ta.

Rashin haɗin kan mutanen yankin Falasdinawa da ma rashin amince da ƴancin ƙasar domin ta jagorancin tattaunawa da Isra'ila ya taimaka wajen hana cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Wasu masana suna ganin akwai kuma rashin sanannen shugabanci a Hamas bayan Isra'ila ta kashe fitattun jagororinta. Wannan na nufin Hamas yanzu zai yi wahala ta samu nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Sannan wahalar isar da saƙo zuwa ga shugabannin Hamas, ya sa lamarin ya ƙara zama da wahalar gaske.

Farfesa Fathi Sabah, wani marubuci ne kuma mai sharhin al'amuran yau da kullum, ya shaida wa BBC cewa, " Isra'ila na ganin yaƙinta a Gaza a matsayin mai matuƙar muhimmanci, domin Hamas ce ta fara yaƙin ba Hezbollah ba. Hare-haren Isra'ila a kan Hezbollah a Lebanon wata dama ce da ta samu bayan ta fahimci ta riga ta kassara Hamas a Gaza.

Farfesa Sabah ya yi amannar cewa zafafar yaƙin Hezbollah - wadda ta fi ƙarfi, kuma ta fi zama barazana sama da Hamas - na cikin abubuwan da Isra'ila ta lura da su domin shiga yarjejeniyar tsagaita wutar.

"Rokokin Hezbollah sun kai har birnin Tel Aviv da Haifa kuma sun ɗaga hankalin mutanen ƙasar, sannan dubban mutanen an tursasa su barin muhallansu na arewacin ƙasar," in ji Sabah.

Muhannad Tutunji, wakilin BBC Arabic a Kudus

Akwai abubuwa da dama da suka sa Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a wannan lokacin, musamman ganin bambancin ƙarfin soji da siyasar Lebanon da Gaza.

A Lebanon, Hezbollah - wadda ke gwabza yaƙi da Isra'ila - tana da tsari mai ƙarfi, kuma ɗaya ce cikin ƙungiyoyin ƙasar. Wasu masu sharhi sun ce ba dukkan ƴan ƙasar Lebanon ba ne suka amince da yaƙin Hezbollah da Isra'ila.

Amma lamarin Gaza na da bambanci. A Gaza, Hamas ce gwamnatin kuma ita ce take yaƙin, kuma tana samun goyon bayan wasu ƴan ƙalilan ne cikin masu adawa da Isra'ila.

Ita kanta Isra'ila tana kallon yaƙin na Lebanon daban da na Gaza.

BurinIsra'ila a Lebanon shi ne fuskantar barazanar da ƴan ƙasar suke fuskanta ne a arewacin ƙasar da tabbatar da amincinsu.

A Gaza kuma, burin Isra'ila shi ne ganin bayan Hamas baki ɗaya, nasarar da har yanzu ba ta samu ba. Haka kuma Isra'ila na so ta dawo da sauran mutum 101 da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.

Tsohon shugaban kwamitin tsaro na Isra'ila, Yaakov Amidror ya shaidawa BBC cewa mutanen Lebanon suna fargabar yaƙin zai iya faɗaɗa zuwa wasu yankunan ƙasar.