Me ya faru da mafiya yawan manyan jagororin Hamas?

Lokacin karatu: Minti 6

An kashe mafi yawan manyan jagororin ƙungiyar Hamas tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da ƙungiyar ta kai cikin Isra'ila, lamarin da ya sa ƙungiyar ta fuskanci mummunan koma-baya.

Ga wasu abubuwan da suka samu wasu manyan jagororin ƙungiyar:

Yahya Sinwar

Isra'ila ta yi amannar cewa shi ne ya jagoranci kai harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 zuwa cikin Isra'ila, lamarin da ya yi sanadin kisan kusan mutum 1,200 tare da yin garkuwa da 251. Tun daga wannan ranar ne kuma ya kasance cikin jerin mutanen da Isra'ila ke farauta.

Yahya Sinwar ne shugaban Hamas a cikin Zirin Gaza. Amma ya zama shugaban ƙugiyar baki ɗaya bayan kisan Ismail Haniyeh a birnin Tehran cikin watan Yuli cikin wannan shekara.

Sinwar, wanda aka haifa Zirin Gaza a 1962, ya shiga ƙungiyar Hamas tun yana matashi.

Shi ne ya kafa sashen tsaron ƙungiyar, da aka fi sani da Majd, wanda ya dinga lura da sha'anin tsaron ƙungiyar, da binciken waɗanda ake zargi da zama jakadun Isra'ila, tare da kama jami'an leƙe asirin Isra'ila da sauran jam'an tsaronta.

Isra'ila ta kama Sinwar sau uku a baya. An yanke masa ɗaurin rai da rai har sau huɗu a 1988 saboda kitsa garkuwa da kuma kashe Isra'ilawa biyu da kuma kashe Falasɗinawa huɗu.

Sinwar ya kasance cikin Falasɗinawa 1,027 da Isra'ila ta saki a matsayin musayar sojanta da Hamas take tsare da shi a Gaza tsawon shekara biyar.

Ya koma Gaza kan matsayinsa na babban jagoran Hamas, inda a shekarar 2017 aka naɗa shi shugaban sashen siyasa na ƙungiyar a Zirin Gaza.

A 2015, Amurka ta saka Sinwar cikin baƙin littafinta na "yan'ta'addan duniya".

A ranar 16 ga watan Oktoban 2024 ne dakarun Isra'ila suka kashe Sinwar a birnin Rahaf.

Ismail Haniyeh

Ana kallon Ismail Haniyeh a matsayin jagoran Hamas mafi girma, har zuwa lokacin da aka kashe shi ranar 31 ga watan Yulin 2024.

A matsayinsa na shahararren mamban ƙungiyar ne tun a shekarun 1980, Isra'ila ta taɓa tsare shi a gidan yari shekaru uku a 1989 lokacin da take daƙile boren Falasɗinawa.

Sai kuma ya koma gudun hijira a wani yanki tsakanin Isra'ila da Lebanon tare da wasu shugabannin Hamas a 1992.

Bayan shekara guda a zaman gudun hijirar ya koma Gaza, inda aka naɗa shi shugaban sashen addini na Hamas a 1997, wanda ya taimaka masa wajen kafa ikonsa.

Shugaba Mahmoud Abbas ya naɗa Haniyeh firaministan Falasɗinawa a 2006 bayan Hamas ta lashe akasarin kujeru a zaɓen majalisa. Amma an sauke shi sakamakon tashin hankali a Gaza, inda Hamas ta kori jam'iyyar Fatah ta Abbas daga Zirin Gazan.

Haniyeh ya ƙalubalanci sauke shi a matsayin "wanda ya saɓa wa doka" kuma Hamas ta ci gaba da mulkin Gaza.

An zaɓe shi a matsayin shugaban sashen siyasa na Hamas a 2017, abin da ya sa ya zama kamar wani mafi girman shugaba.

A 2018, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Haniyeh a matsayin ɗanta'adda.

Ya shafe tsawon shekaru yana rayuwarsa a ƙasar Qatar.

Mohammed Deif

Mohammed Deif ne jagoran rundunar Izz al-Din al-Qassam Brigades, ɓangaren soji na Hamas.

Kuma shi ake zargi da kasancewa babban wanda ya tsara harin 7 ga watan Oktoba.

Deif ya kasance ƙwararre a wajen Falasɗinawa, amma kuma mutum mai rayuka da yawa a wajen Isra'ila, (saboda yadda ya sha tsallake rijiya da baya).

Hukumomin Isra'ial sun kulle shi a gidan yari a 1989, bayan ya kafa rundunar al-Qassam da nufin kama sojojin Isra'ila.

Bayan da aka sake shi ne kuma ya taimaka wajen gina hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da suka bai wa Hamas damar shiga cikin Isra'ila daga Gaza.

Deif ya kasance cikin mutanen da Isra'ila ta fi nema ruwa a jallo saboda zargin kitsa harin bamabamai kan bas-bas da suka kashe gomman Isra'ilawa a 1996, da kuma kamawa da kashe sojojinta uku a tsakiyar shekarun 1990.

Isra'ila ta ɗaure shi a gidan yari a 2000, amma ya tsere a lokacin farkon fara boren Falasɗinawa da aka fi sani da intifada.

A ɗaya daga cikin yunƙurin kashe shi da aka yi a 2002, Deif ya kuɓuta amma ya rasa idonsa guda. Isra'ila ta ce ya kuma rasa hannu da ƙafa guda-guda, kuma ba ya ma iya magana da kyau.

Dakarun Isra'ila sun sake yunƙurin kashe shi yayin wani hari a Gaza a 2014, amma ya kuɓuta, sai dai sun kashe matarsa da 'ya'yansa biyu.

A ƙarshe Isra'ila ta ce ta kashe deif a wani hari da ta kai kan wani gida a Khan Younis ranar 13 ga watan Yulin 2014.

Marwan Issa

Marwan Issa ya kasance mataimakin kwamandan bataliyar Izz al-Din al-Qassam Brigades, kuma na yi amanna yana cikin waɗanda suka kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoba.

Ya kasance cikin jerin mutanen da Isra'ila ta fi nema, kuma an jikkata shi lokacin da Isra'ilar ta yi yunƙurin kashe shi a 2006.

Sojojin Isra'ila sun tsare Issa a farkon boren Falasɗinawa (1987-93), na tsawon shekara biyar saboda ayyukansa da Hamas.

Hukumar Falasɗinawa ta kama shi a 1997, amma aka sake shi bayan fara boren Falasɗinawa na biyu a 2000.

Jiragen yaƙin Isra'ila sun taɓa rugurgaza gidansa har sau biyu yayin samamen da suka kai a 2014 da 2021, inda aka kashe ɗan'uwansa.

Sojojin Isra'ila na yi masa laƙabi da Inuwa saboda yadda yake kauce wa mutuwa. Ba a san siffarsa ba har sai a 2011, lokacin da ya shiga wani hoton rukuni da aka ɗauka na musayar fursunoni.

Khaled Meshaal

Khaled Meshaal, da aka haifa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a 1956, ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka kafa ƙungiyar ta Hamas.

Bisa umarni kai-tsaye daga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, hukumar leƙen asiri ta Isra'ila Mossad ta yi yunƙurin kashe Meshaal a 1997 lokacin da yake zaune a Jordan.

Dakarun Mossad sun shiga Jordan ɗauke da fasfon ƙarya na Canada kuma aka yi wa Meshaal allura mai ɗauke da guba yana tsaka da tafiya a gefen titi.

Hukumomin Jordan sun gano yunƙurin kisan kuma suka kama dakarun na Mossad.

Tsohon Sarkin Jordan Hussein ya nemi firaministan Isra'ila ya ba da maganin allurar da aka yi wa Meshaal.

Bayan matsin lamba daga Shugaban Amurka Bill Clinton, Netanyahu ya bayar da maganin bayan ya ƙi tun da farko.

Meshaal da ke zaune a Qatar, ya je Gaza a karon farko a 2012. Shugabanni da mazauna Gaza sun fita domin tarɓarsa.

Hamas ta zaɓi Haniyeh domin maye gurbin Meshaal a matsayin shugaban sashen siyasarta a 2017, sai kuma Meshaal ya zama shugaban sashen amma a ƙasashen waje.

Mahmoud Zahar

An haifi Mahmoud Zahar a Gaza a 1945, mahaifiyarsa 'yar Masar ce, mahaifinsa kuma Bafalasɗine.

Ana kallaonsa a matsayin fitattun shugabannin Hamas na siyasa.

Ya yi makaranta a Gaza kuma ya yi karatun jami'a a Alƙahira na Masar. Ya zama likita a Gaza kafin daga baya Isra'ila ta kore shi saboda aniyarsa ta zama ɗansiyasa.

An tsare Mahmoud Zahar a gidan yari a 1988. Yana cikin mutanen da Isra'ila ta fitar daga yankin a 1992, inda ya shafe shekara ɗaya a yankin da ke tsakanin Lebanon da Isra'ilar.

Bayan Hamas ta lashe zaɓen Falasɗinawa na 2006, Zahar ya zama ma'aikacin ma'aikatar harkokin waje a gwamnatin su Ismail Haniyeh kafin a sauke shi daga muƙamin.

Isra'ila ta yi yunƙurin kashe Zahar a 2003, lokacin da wani jirgi ya jefa bam a kan gidansa da ke birnin Gaza. Harin ya ji masa ƙananan raunuka amma ya kashe babban ɗansa Khaled.

Ɗansa na biyu Hossam, wanda mamba ne a bataliyar al-Qassam Brigades, ya rasu a harin Isra'ila na 2008 a Gaza.