Albashi mafi ƙanƙanta: Wane hali malaman makarantun firamare ke ciki a Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 3

Malaman makarantun firamare a wasu jihohi sun koka kan yadda suka ce har yanzu ba a soma biyan su sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000 ba, duk da an soma biyan ma'aikata a matakin jiha.

A jihar Kebbi malaman makarantun firamaren sun ce gwamnatin jihar ta yi musu ƙarin da bai wuce naira dubu goma ba, wasu ma ko sisi ba a ƙara musu ba, yayin da takwarorinsu na Sokoto da Yobe ke zaman jira.

Gwamnatin jihar Kebbi tuni ta soma biyan sabon albashi ga ma'aikatanta, sai dai malaman makarantun firamare a can ma sun ce kwalliya bata biya kudin sabulu ba, inda wasu an ƙara musu adadin da bai kai na albashi mafi kankanta ba.

"Ƙarin da aka yi bai taka kara ya karya ba,wasu sun samu 10,000, wasu ba su samu ba wasu kuma kuka suke cewa an rage masu albashi, nima yadda ake biyana haka ake biyana ko sisi ba'a ƙara mani ba," Cewar wani malamin makarantar Firamare a jihar Kebbi.

A jihar Yobe tun bayan da gwamnatin jihar ta amince da biyan sabon albashin yau wata biyu kenan, amma malaman firamaren jihar ba wani labari, kamar daya daga cikin su ya tabbatarwa da BBC.

"An biya malaman sakandare amman mu malaman firamare an yi mana ko oho, ba mu san me muke ciki ba, ya kamata a fito a yi mana bayani kan dalilin da ya sa ba a biya mu ba."

Hakazalika, gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya soma biyan albashin na naira 70,000 daga watan Janarun da ya gabata, amma can din ma ba da malaman firamare ba.

"Ƙarin albashi dai shiru, muna kira ga gwamna da ya taimaka yayi mana kamar yadda yayi wa kowa, ya dubi irin wahalar da malaman firamare ke sha," in ji wani malamin firamare a jihar Sokoto.

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin ɓangaren gwamnatocin jihohin sai dai haƙarmu ba ta cimma ruwa ba, amma kungiyoyin kwadagon jahohin sun ce sun zauna da gwamnonin, kamar yadda kwamared Musa Sarbutu shugaban kwadago na jihar Yobe ya shaidawa BBC.

Haka shi ma kwamared Abdullahi Aliyu na kungiyar kwadagon jihar Sokoto, ya ce sun yi zama da gwamnatin jihar inda ta ce ba za bar kowa ba

"Nima ma'aikacin ƙaramar hukuma ne saboda haka kowa tafiya za a yi da shi, gobe ma'aikatan lafiya za su anshi albashinsu, kuma maigirma gwamna, Ahmed Aliyu ya amince zai ba kowane ma'aikaci a kowe mataki albashi mafi ƙanƙanta na dubu 70,000," a cewar Abdullahi Aliyu.

A watan Yulin 2024 ne, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ƙara albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan ƙasar daga naira 30,000 zuwa 70,000, inda galibin jahohin kasar suka soma aiwatar da shi.

Malaman makarantun furamare a Najeriya dai, kusan an jefar da su, musamman a karin girma da albashi, abin jira a gani dai shi ne ko gwamnatocin za su saurari wannan korafi, lokaci ne zai tabbatar.